PAGE-19/20
________________________________________________________
*MY NEW GRP Xayyeesherth Fana Grp1 yau inga ruwan sharhi🥰*
Safiya kuwa su na shiga ta rungume Faruq tare da fadin, "Umm Masoyina Har na ji cikin ya fara sauki, ina ga daman rashin ka ne."
Faruq ya juyo da ita tare da zaunar da ita agefen gadon shima ya zauna sannan ya ce, "Dakyau My Princess daman ai haka na ke so."
Tuni Safiya ta fara nunawa Faruq tsantsar soyayya wanda ya kai ga ya manta da Sakina.
Sakina ta na daki har barci ya dauketa kawai sai ta juyo dariyar Safiya wanda da ka ji zakasan cewa suna cikin nishadi.
Wani azazzaban kishine ya lullube Sakina wanda ya kai ga tafara hawaye, murmushi tai tare da share hawayen sannan ta tashi ta yo alwala sai da ta yi Sallah raka'a biyu sannan ta dauki littafi mai tsarki wato AL-QUR'ANI ta karan ta iya ka yin ta wanda sai da taji ranta ya yi fari tas ta manta da damuwa da ke ran ta, tuni barci ya dauketa awajen mai cike da nishadi.
WASHE GARI"""""""""""
Sakina na tashi da asuba ta ji jikinta ras kamar ba tai wani ciwo ba, hakan ya sa ta fara gyare-gyaren gida, sai da gama gyara dakinta tsaf sannan ta gyara tsakar gidan ma, ba ta huta ba ta shiga kicin domin hada mu su kayan karyawa.
*DOYA ta fara ferewa sannan ta wanke ta tsaf ta fara suya, bayan ta gama suyan ta dibo kwai guda biyar tai greating attaruhu da albasa ta sa abin suyan ahuta da mangyada da kayan miyan sai da suka fara soyuwa sannan ta zuba kwan ciki, ta na zuba kwan ta fara jujjuya shi sannan tasa kayan dan dano tuni gida ya kaure da kamshi miya ta yi kyau sose a ido ma bare a abaki,,,,,ta gamawa ta sa aflas sannan ta koma ga yi musu tean waken suya, waken ta ta fara tsincewa kusan ba arasa kasa ko wani datti aciki, sannan ta wanke shi tsaf bayan ta wanke ta dauko blandar ta tai brandin, ta tace shi tsaf ta cire dusar tukun ta daura ahuta, ta sa gishiri dan kadan tare da yar cittar ta,,,,in kina da bukata za ki iya sa ma sa lipton,,,,Ashawarce tean waken suya ya na da matukar amfani garemu yan uwa kamar yadda Sakina tai mu ma muna kokari wajen yi domin gina jikin mu da na yaran mu.*
Ta na kammala kayan karyawan ta shirya su tsaf a kan dainin gwani sha'awa, sannan ta nufi toilet tai wanka ta na fitowa kennan sai ga Faruq ya shigo ya na fadin, "Matar Aljannah me a ka girka mana ne gidan ya cika da kamshine?"
Murmushi Sakina tai tare da wuce sa ta na fadin, "Za ka gani ai."
Faruq ya janyota cikin sa ya na fadin, "To baza afadamin ba kennan sai na gani."
Girgiza kai kawai Sakina tai tare da fadin, "Morning Honey."
Sai da ya ma ta wani k'ayataccen kiss sannan ya ce, "Morning Darling mie fatan kin tashi lafiya."
"Ni ban tashi Lafiya ba domin na kwana cike da kewar mijina."cewar Sakina.
Faruq ya tallafo fuskarta garesa tare da fadin, "Ni ma nasan da hakan amman yau kam ai sai kin gaji da ni dan ba inda zani domin nima nayi kewarki sosai."
Sakina ta ce, "Uhumm uumm Ni fa yau ina so inje in bude shagona ka ga fa nafi wata banje ba tunda dai abin da ya hanani zuwan ya tafi ai sai inkoma."
Faruq ya ce, "To a ka ce Miki wani Babyn ba zai zo bane? to ki ma sani ya hanya ehee, yau dai a min alfarma sai gobe ma fita gaba daya."
Sakina ta ce, "Uhimm to nikam kira Safiya muci abincin bara nasa kaya."
Faruq ya tafi ya na murmushi.
Safiya kuwa kaman jiran kiris take tuni ta fito tana wani rangwada.
rikye ma Faruq hannu tai suna tafiya har dakin Sakina.
shigar Kananun kaya Sakina tai wanda inka ganta zakace dan ita akayi ko, ko ajikinta aka dinka domin kuwa sun matukar ma ta kyau.
Safiya na ganinta jikinta ya yi sanyi Faruq kuwa bai san lokacin da ya bige hannun Safiya a na shi ba ya nufi..........
Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:18] Shalelen Mamata🥳🥳: ***
*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_