AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-21/22

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*CIKIYA🗣️🗣️DAN ALLAH MUNA NEMAN SHAFUKAN LITTAFIN MAI SUNA YAYA IMRAN WANDA MU KA FARA NIDA FATIMA ZAHRA EYMAN MUN RASA WAYOYIN KUMA MUN RASA FEJIS DIN INDA MAI SHI PLS TA TURO MANA MUNA SO MUKARASA INAGA DAGA 1 ZUWA 12KO 13 MU KA TSAYA👏👏*

*WANNAN SHAFIN NAKINE KE DAYA JIDDATYY TA GRP DIN IMAAN CASTLE KI YI YADDA KI KESO DASHI SHARHIN NA SANI NISHADI*

Nufi inda Sakina take janyota ya yi jikinsa tare da fadin, "Sweetheart kin san yadda ki ka yi kyau kuwa."

Murmushi Sakina ta yi tare da fadin, "Ban sani ba kuma bana fatan sani indai nama wanda na yi dan shi."

Faruq ya ce, "Madalla da mace ta gari yanzu dai azubamin abincin nan na ci domin hanjin jikina sunfara motsi."

Dariya Sakina tai tare da fadin, "Ai kuwa naga alama tunda ga Safiya ma ta kasa magana."

Wani mummunan kallo Safiya tai ma ta,,ita kuwa Sakina Murmushi ta sake ma ta mai nunin cewa ba ta ga komai ba.

Ababban faranti Sakina ta zuba mu su doyar dukan su sannan ta sa miyar a karamin boll,, tean kuwa ta zubawa kowa nasa.

Faruq ya fara shafa ciki tare da fadin, "Ni har kamshin ma ya fara kosar da ni, gwanda muyi muci kar ciki ya koshi baki bai koshi."

Dariya sukai su biyun ban da Safiya wadda tuni ta hasala da kaganta zaka fahimci akwai wa ni abu aranta.

Faruq ya lura da hakan amman ya basar.

Faracin abincin ya yi tare da fadin to , "Duk wadda ta riga bude baki ita zan bawa."

Da gangan Sakina ta yi jinkirin budewa domin ya ba Safiya ai kuwa take Safiya ta washe ya ba ta.

"Umm umm to nima ka tsaya in ba ka mana." cewar Safiya.

Murmushi Faruq ya yi tare da bude bakin sa, Ta ba sa.

Faruq ya ce, "Yauwa matar kirki ke da bakya son cin abinci ma dole yau inyi feeding din ki da kai na."

Sakina ta ce, "umm Honey zanci kabarni kawai."

Faruq ya ce, "Aa."tare da kara janyota jikin sa, ya rada ma ta magana akunne, wanda ni kai na banji ba sai dariyar su da ke tashi.

Tuni Safiya ta tashi tare da fadin, "Nikam na koshi inka gama ina so zamuyi magana." sai da tama Sakina wani irin kallo sannan ta fice.

Faruq ko, ko ajikinsa dan ko amsa ma bai bata ba ya ce, "Darling kinga bude bakin ko sai na bude miki da kai na ne?"

Sakina ta bige ma sa hannu tare da fadin, "umm ni na bude."

Ya ba ta ta ci chokaki 3sannan ta ce, "umm nikam nakoshi tsaya mu yi magana."

Faruq ya ce, "ba wani magana sai kinci kin koshi."

Sakina ta shagwabe tare da fadin, "umm umm Allah amai zanyi kabari zan sha tean kawai."

Ya ce, "Owk Madam to yanzu wace maganace."

Sakina tai murmushi sannan ta ce, "Ka yi hakuri da duk abinda zance karage zakyewarka akaj na indai Safiya na guri kaga bata jin dadi kuma hakan bai kamata ba."

Faruq ya ce, "Amman dai kin san ina iyaka bakin kokari na ko kuma naga ai dukanku din matanane jiya ma fa......

Sakina ta rufe ma sa baki tare da fadin, "Umm ni karka fadamin komai nidai kawai ka yi kokarin kiyaye abinda na ce."

Murmushi Faruq ya yi tare da fadin,"Matar kirki matar aljanna ina sonki Sakina ta ina alfahari da ke dabi'unki suna birgeni, Ki yafemin pls."

Sakina ta sauke ma sa hannunsa kasa tare da fadin, "Ni bakamin komai ba, ina sonka mijina."

Faruq ya ce, "To yanzu mekikeso in miki?"

Sakina ta shagwabe ta ce, "Umm ni ka goyani to."

Faruq ya ce, "Laa ashema so kike in balle."

Sakina ta kara shagwabewa kamar zatai kuka.

Faruq ya ce, "Haba gimbiyata miye na kuka ku ma wasa na ke miki fa ai yau har abin da ya fi goyama zan miki."

Sakina ta ce, "To muje."

Daukan ta ya yi chak sunata dariya ....

Safiya kuwa tunda taje daki ta kasa tsaye ta kasa zaune Zuciyarta kamar zata fashe dan takaici daga karshe dai ta kira maman ta awaya.

, "Mama ni wallahi na gaji haba dan Allah wai inyana gaban waccer munafukar sai ya manta dani kamar an ajiye dusa ni wallahi bazsn iya ba nagaji duk abin da namai da yaganta sai ya manta."cewar Safiya

Mama ta ce, "Da Sauranki Safiya kin manta abinda kika fadamin jiyane wai? ai dole sai kinyi hakuri kin nuna ma su soyayya dukan su hakan ne kawai mafita, wai ma bai taka alayar nan ba ne?"

Safiya ta ce, "Ina fa tunda ta makyalesa adaki ai inaga ko kofar gidan ma ba ya je ba."

Mama ta ce, "Oh nikam ko ya zanyi da wannan mayyar ne oho kuma fa kinsan ya ce inya kwana biyu ko antaka ba zsi yi aiki ba, amman karki damu anjima zanzo miki da wani sirrin."

Safiya ta ce, "Owk ni ina son zuws kasuwa ma dole zsn yi siyayyan kanun kaya dan naga alamar so ta ke ta kereni da yawa."

Mama ta ce, "ki bar wannan ma aguna zan siyo mi ki fitattiu ban so kije ko ina gwanda ki zauna agidan.

Safiya ta ce, "Yauwa Mamana byebye sai kinzo."

****Afannin su Sakina kuwa..

*Yawan comments yawan typing🤷‍♀️*

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:18] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_