PAGE-23/24
________________________________________________________
*SADAUKARWA GAREKI MY FIRDAUSI KI YI YADDA KI KESO DA SHI I REALLY LYK UR LVLY CMMTS🥰🥰*
Ta na nan tana farantawa mijinta rai.
A na cikin haka sai ga SUBAI'ATU ta kirasa awaya *Matar sa da ke niger* Kallo daya ya ma wayar ya kauda kai,, Sakina kuwa ta janyo wayar tare da mik'a ma sa ta na, "Suby ce fa ka dauka kasan bazataji dadi ba in ba ka dauka ba.'
Murmushi Ya yi ya amsa tare da sa ta Free.
Sallama Subai"atu tai ma sa tare geshesa.
Ya Amsa tare da fadin, "Fatan ki na lafiya?"
Ta ce, "Lafiya lau ya jikin Anty Sakinan?"
Faruq ya kalli Sakina tare da fadin, "Ga ta nan ta ware."
Sakina ta ce, "Subyna na ware fatan kema kina lafiya."
SUBAI"ATU ta ce, "Lafiya lau Anty yaushe za ki biyo Yaya ku zo?"
Sakina tai Murmushi sannan ta ce, "Na kusa insha Allah subyna."
Da haka sukai sallama.
Sakina ta ce wa Faruq, "Gaskiya Suby na birgeni Wallahi kwata-kwata ba ta da damuwa."
Faruq ya ce, "Sose ma Wallahi ai yarinyar ta huta a bin ta."
*****
Maman Safiya na zuwa fuuu ta huce dakin yar ta, ta na zuwa kuwa Safiya ta taso da gudu ta rungumeta sannan su ka baje kolin su.
Maganin Mama ta fara cirowa tare da fadin, "Fatan dai yau a dakin ki ya ke?"
Safiya ta ce, "Eh."
Mama ta ce, "Yauwa wannan a cikin abinci za ki sa ma sa,, ga kuma ka yayyakin nan kala biyar ne ki zabi wanda za ki sa yau, ko ma in zaba mi ki wannan." ta dago wa ta yar shafa-shafa riga iya gwiwa da wani dogon wando.
Safiya ta ce, "Yesss Uwar kirki haka za ayi to amman maganin nan kennan a abincin sa shi kadai zan sa ko?"
Mama ta ce, "Eh shi kadai ma na, wai ma ya naji gidan tsit ne ina su ke da munafukar matarsa."
Safiya ta ce, "Hmm ai yau Su na d'aki tun safe ko kofa ba su fito ba." ta karasa maganar ta na tabe baki."
Mama ta ce, "Ke kuma ki ka bar su? to ma za ta shi muje sai ka ce ba ma ce ba, bazaki fita ki shiga da makirci ba."
Tare su ka fita, dai-dai kofar d'akin Sakina su ka tsaya Mama ta ce, "Yauwa bari kiga."
Kwankwasa kofar ta fara da karfi.
Faruq ya ce, "Wa ye."
Mama ta ce, "Ni ce."
Ya zo yana budewa ya ga Safiya da Maman ta.
Mama ta ce, "Umm daman na ga nazo ne ba mu gaisa ba na ce bara in ma magana,
Faruq ya durkusa ya gesheta tare da fadin , "To ku shigo mana."
Safiya na ja da baya Mama ko na jan ta.
Sakina na ganin su gabanta ya fadi, ka sa hada ido tai da Mama kan ta a kasa ta gesheta.
Dan gulma da Murmushin ta, ta amsa tare da fadin, " 'Ya ta ya jikin na ki dai."
Sakina ta ce, "Da Sauki Sose Mama ."
"Alhamdullillah." cewar Mama.
Faruq kuwa ya shige ciki kawai ba dan zuciyarsa ta so ba, Mama da Safiyane kadai su ke ta hira Sakina kuwa ta kasa sakewa sai wasa take da yan yatsunta kawai, Su na ta gulmarta da ido.
Sakina ta tashi zata dauko mu su sallaya su yi sallah Mama ta tashi ta shiga kicin ta dibo mangyada ta zubo a kofar dakin.
Safiya za tai magana Mama ta ma ta alamar tai shiru.
Sakina kuwa da saurin ta za ta ba su ai sai jinta tai tim a kasa ta sule.
Mama ta kasa rikye muguntarta sai da tai dariya sannan ta zo suka dagata.
Da Sauri Faruq ya fito ya karbi abarsa tare da fadin, "Sannu Sakina mi ye ya yarda ke haka? fatan dai ba kiji ciwo ba ko?."
Murmushi tai tare da fadin, "Ina ga mangyada ban san ta ya yazo kofar dakin ba wallahi,, Smile banji ciwon komai ba."
Ta tashi ta na Mama ga sallayar bara nayi mopin din wajen.
Faruq ya koma domin shima ya dauro alwala, su Mama da Safiya kuwa su kai Adakin.
Mama ta na kintsawa Safiya, "Amman gaskiya Yaron nan bai da kunya agabana zai dauki matar tasa."
Faruq ya fito za shi massallaci ya ce da Mama, "Zani masallaci na ce ko zaki zo in karasa da ke gida."
Mama ta ce, "Aa nagode jeka abin ka kawai."
Faruq ya ce, "Da dai kinzo na Kai ki dan yanzu anguwar nan in yamma ta yi ba aciki fita ba domin yan daba sunyi yawa."
Ba abinda Mama ta ke tsoro kamar yan daba dan haka tuni ta ce, "Ah mu je kawai banci ta zama ba, Safiya ma yi waya ko?"
Su ka fita tare da Faruq.
Mama na tafiya Safiya ta tafi bangarenta domin yin girkin dare kamar yadda mamanta ta bukata.
Ta gama tsaf sannan tayi wanka tasa kanun kaya.
Da kaganta zakasan ba sabanba domin rawa ma take acikin kayan ya tafi ma ta wani zulum ba kyan ga ni, bai bi jikinta ba ko kadan bare ma ko ya bi bazai ma ta kyau ba domin single ta ke.
Tana jin shigowar Faruq ta kara kintswa domin ita gani take yau tayi wankan kece raini.
Sai da Faruq ya shiga dakin Sakina ya kirata sannan su ka nufi bangaren Safiya.
Ta na jin su ta tawo da rangwada tare da shagwabe fuska.
Suman tsaye Sakina tai shiko Faruq bai san lokacin da dariya ta subuce ma sa ba.
Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:19] Shalelen Mamata🥳🥳: ***
*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_
FOLLOW ME ON WATTPAD AishaMuhammad958