AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-25/26

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

_~SADAUKARWA GAREKU YAN GROUP DINA XAYYEESHERTH FANS GROUP INA YIN KU IRIN SOSE DINNAN🥰🥰🥰~_

Safiya ta tsaya jim ta kasa ma motsi gannin dariyar da Faruq ya ke hadda faduwa kasa.

Sakina ta karaso gareta tare da fadin, "Safiya ai da kin ba da anrage mi ki kayan."

Safiya ta galla ma ta harara tare da fadin, "Ni haka nakeso naga kema ai haka kikesa naki."

Ta karasa gaban Faruq tare da fadin, "Sweety banyi kyauu ba ne naga kana dariya?"

Faruq ya kara kyalkalewa da dariya ai tuni Safiya ta shige cikin daki ta na kuka.

Sakina ta ce, "Haba Honey wannan bai kamata, kamata yayi ace ka gyara ma ta ba wai kafara dariya ba ka ga fa ta tafi tana kuka."

Faruq na dariya ya ce, "To ni ina ma dariya za ta barni ne ina ganin abu kamar silindar gas."

Sakina ta ce, "Ya isa yanzu dai jeka fito da ita muci abinci danni yunwa na ke ji wallahi."

Faruq ya ce, "Owk ki zauna ina zuwa."

Ya na shiga ya ga Safiya ta kafa kai banda kuka ba abinda ta ke.

Faruq ya ce, "Ah my slinda baby mi ye na kuka kuma kyan da ki kayi ne fa yasani dariya bana so sakina ta gane ne."

Da Sauri Safiya ta dago tare da fadin, "Da gaske?"

Faruq dai ya yi kokari wajen kintse dariyar sa tare da fadin, "Eh Sosai ma ki zo muci abincin ko?"

Safiya ta tashi hadda kara gyarawa kayan zama ajikinta ta fara wata sabuwar rangwadar tare da rikyewa Faruq hannu Su ka fito.

Sakina ta na ganin su ta kawar da kai domin inta cigaba da kallo itama zata iya kwashewa da dariyar da ta fi wadda Faruq ya yi ma.

Faruq kuwa murmushin dole ya ke wanda dariyar ke shirin kara subuce ma sa.

Suna zama safiya ta ce, "Eheen yau plate din ka daban namu daban."

Faruq ya yi murmushi tare da fadin, "An wareni kennan wariyar launin fata to shikennan azubamin nawa na ci ni daya tunda an maidani marayan dole."

Sakina tai murmushi tare da murguda ma sa baki sannan ta ce, "E in ba zai dai kaci da mu ba."

Faruq ya ce, "Hhhhhh yarinya zan kamaki ne."

Safiya ta ce, "Oyaa ga naka muma ga namu. "

Faruq zai fara ci kennan a ka kirasa awaya ya tashi ya na fadin, "Ina zuwa bara na amsa waya saura kuma ku cinyemin nama na."

Dukan su su ka masa dariya kawai.

Ran Safiya dai bai so ba domin burinta kawai ace Faruq ya ci maganin nan..

Sakina da Safiya kuwa suka fara cin na mu, abincin dai ba dadi kamar anwanke kan mahauukaci taliyace da tea tare farfesun kan rago, taliyar gabadaya ta jagwale, farfesun ku wa banda karni ba abinda ya ke.

Dakyar Sakina ta ke cin abincin nan wandA ta ci ma shirin dawowa ya ke amman ta na ta karawa kardai Safiya ta ji ba da di.

Ita kuwa sai rawar kai ta ke adole tayi girki mai dadi.

"Sakina ai in fada ma ki nasha wahala a kan girkin nan shiyasa ya yi dadi har fa vedio na sa ina yi ina gani, hmmm Ashe daman ana wanke nama? ai ni ban ma sani ba sai yau shine fa na wanke sa ya fita kall."

Sakina dai ta kasa magana kawai sai bin ta da Eh Eh ta ke.

Faruq ya shigo da Murmushin ya na fadin, "Yauwa afara bani farfesuna in farfesa shi a ciki."

Sakina ta ce, "Aa abincin dai ko oga?"

Safiya ta ce, "Eh ma na adai fara cin abinci danni harma na koshi Sakina ko in kara mi ki ne?"

Sakina ta ce, "Aa ni kam".

Faruq ya zauna zai ci yana......

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:19] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_