PAGE-28/29
________________________________________________________
"Ka tashi wallahi ni bazan yarda ba kullum shiga da fitan kayan da matar nan ta ke daban kuma ma su tsada da angani za'a fahimci hakan,sannan nasan ba wanda zai siya ma ta face kai, to wai ni ma ba mace ba ce ko ya wallahi bazan yarda ba."
Ta kara fashewa da .
Faruq ya ce, "Safiya ke kan ki kinsan dai Sakina tanada shagonta wanda shi kan sa shagon ba ko biyar di ta aciki bare kuma kayan sawan ta."
"Karya ka ke wallahi abin da sun riga sun gama mallakeka ai dole ka ce min haka kuma wallahi bazata sabu ba ni dai." cewar Safiya kennan tare da guntun hawayenta na munafurci.
Faruq ya ce, "Shikennan dai bari Sakinan ta dawo kin san ba na son tashin hankalin nan na ki."
Safiya tai dariya tare da fadin, "Ummm wai ma kasan da tazo tafiya fa nace ma ta, ta tsaya in tasheka ta ma sallama ta wani gwalalo ido tare da fadin ina ai ni sauri na ke inya tashi kya fada ma sa."
Faruq da mamaki ya ce, "Sakinar?"
Safiya ta ce, "kwarai ma kuwa nayi-nayi ta zauna ta jiraka amman ta ki fir daga karshema tsaki ta min ta fice abin ta."
Faruq na tantamar hakan azuciyarsa amman wani gefen kuma natabbatar ma sa da maganar Safiya.
Daga nan Faruq ya shirya ya yi wanka sannan shima ya tafi aiki.
******Kamar yadda su ka saba Misalin Karfe biyar Faruq ke zuwa dauko Sakina ashago yayin shima ya tashi a aiki domin su koma tare, Sakina ta na ankare da lokacin da taga lokacin zuwansa ya yi kara gyara kwalliyarta tai tare da feshe jikin da turare.
Yau ba kamar kullum domin kuwa duk tsiya ya kan zo da fara'a amman yau fuskarsa a murtike ba alamar walwala.
Tun daga nan jikin Sakina ya yi Sanyi tare da fadin, "Ina hini."
Ya amsa ya na fadin, "Ki kulle mutafi ,batare da ya kalli inda ta ke ba ma bare ya ma ta kyakkyawan kallO.
To kawai Sakina ta ce jiki asanyaye ta rufe shagon ban da Addu'ah ba abin da ta ke cikin zuciyarta.
Ya kan bude ma ta kofa da kansa amman yau kam ko ajikinsa ya je ya zauna kawai.
Ta na zuwa ta bude ta shige Ciki.
Haka akai tafiyar nan batare da kowa ya ce kalla ba.
Ita dai Sakina Addu'ar ta tacigaba da yi domin za ta iya cewa bata taba ganin Faruq a irin yanayi na fushi kamar yau ba.
A haka har su ka isa gida, Ya na gama Fakin ya ce, "Ki zo dakin Safiya ina nemanki."
Sai da gaban Sakina ya fadi, ta na shiga dakinta ta ajiye jakarta sannan ta nufi dakin Safiya.
Ta na shiga taga Safiya tsamo tsamo a kan cinyar Faruq suna ta washe baki.
Faruq na ganinta ya murtike fuska Safiya kuwa kara jan sa da wasa ma ta ke.
Faruq ya ce, "Safiya Stop it tsaya mu yi magana incire abin da ke rai na."
Sakina dai ta zauna shiru kanta a kasa.
Faruq ya ce, "Sakina! abin nan na ki ya isheni haka wato kin bijiro da sa kayayyaka kala daban-daban domin ki sa Safiya zargin ni ke siya mi ki? nagaji na fada mi ki nagaji ki kiyayeni wallahi daga yau indai kaya ba ni nasiyo mu ku kalla daya ba ko na akwatin ki to karki kuskura ki kara sa wani daban sannan kuma wa to da safe yanZu kin fi karfin kizo ki gaidani mu yi sallama ko? ana ki Zo ki na Aa shago ya fini mahimmanci."
Girgiza kai kawai Sakina ke yi domin ta ma rasa ta cewa.
Safiya ta ce, "Ni fa ban yarda ba in ma drama ku ka shirya ni dai kawai asiyamin irin rigar jikin tan nan ehee."
Faruq ya ce, "Haba My dear karki damu wadda ta fita ma gobe zan siya mi ki."
Safiya tai wani murmushi wanda ba wanda yasan fassararshi illa ita da Ubangiji.
Faruq ya kara da cewa, "Ki tafi kawai ki kulle kofa danni ba zuwa dakin ki zanyi ba tunda ban da amfani."
Safiya ta ma Sakina gwalo.
Sakina ta tashi za ta tafi sai ta dawo tare da fadin, ".........
Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_