AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-30

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

_*SLINDA BABY🤣INJI YAN GRP DINA,,TO NIMA NA DANA SAURA KUMA AFADAWA SAFIYA😅*_

Faruq, "Ina ga dai ko me zan ma bai ci ace zaka gujeni ba, bayan kasan cewa yau a d'akina ka ke."

Tsawa ya ma ta tare da fadin, "Na ce mi ki bazan zo ba din ko kin isa kimin dole ne? Iye? Sai ka CE wata mayya to na ki zuwan."

Haka Sakina tafita jiki asanyaya zuciya na kuna, Safiya Ku wa Dadi ya mamaye ma ta zuciya da sauri ta riko hannun Faruq tare da fadin, "Haba darling Mie kabar damuwa ka rabu ita taje chan da rashin kunyarta ni zan faranta ma ai."

Faruq ya yi murmushi tare da fadin, "Gaskiya ban kyauta bara naje na bata hakuri kar hukuncin ya ma ta yawa."

Tuni Safiya ta fara kukan munafurci tare da fadin, "Haba Dan Allah ni ni fa? Ka tsaya nidai kuma ma fa yanzu inkaje za ta iyama komai tinda ran ta ya baci, ni karka je a kara bata min ranka."

Faruq ya ce, "Ku ma fa hakan Safiya kin yi tinani mai kyau barta kawai muje muyi sallah mu sha tea kawai."

****Sakina kuwa ta na komawa daki tai alwala tai sallah ta yi karatun littafi mai girma kamar yadda ta saba, nan da nan ta ji ya kore ma ta damuwar da ke ranta, kasancewar ta na jin jikinta wani iri ga yar yunwar da takeji hakan ya Sa itama ta sha tea.

Sai da ta kara gyara dakin ta tsaf sannan ta kwanta domin barci.

Addu'a tai tashafe dukkan jikinta da ita sannan ta fara barcin ta cikin nishadi,Misalin karfe 1nadare kamar amafarki ta ji wani abu na taso Ma ta da sauri ta farka taji wani irin Amai.

Dagudu tanufi toilet tin da taje ta ke kwarara Amai gabadaya jikin ta ya mutu ba kwari domin tin tana amaryar da abin da ta ci har ya kai ga tafara A man zallan ruwa.

Jan jiki ta yi dakyar ta karasa kofar d'akin ta bude sannan ta je saitin na Safiya tana bugawa, Faruq ya yi Nisan barci sose ita kuwa Safiya na jin Maganar Sakina akasale ko ajikin ta.

Tun tana da karfin bugawa har ta gaji ta daina alokacin Allah ya kawo ma ta wani irin barci ya yi gaba da ita.

Da asuba Faruq ya fito za shi masjininsa. kawai me zai gani banda Sakina kwance barci take Amman da kaganta zakasan cewa ba ta cikin koshin lafiya.

Dago ta yayi yana. 'Sakina me ke faruwa tashi ki fadamin kar dai abin da na mi ki jiya ne."

Bude idon da Sakina zatayi sai ta ganta ahanun Faruq , "Magana kasa-kasa ta ke fadin banda lafiya tun jiya da daddare na ke tashin Ku Amman ba Ku tashi ba."

Faruq ya ma kasa kara magana kawai daukan ta yayi ya kai ta dakin ta sannan ya kira likita.

Ita kuwa Safiya ta na daki tana jin duk abin da ke faruwa tai tsit.

Likita naxuwa ya duba Sakina tare da ma Faruq albishir cewa wani cikin gareta.

Ba karamin farinciki Faruq ya yi ba domin bai da burin da ya huce ya ga jininsa.

Safiya na labe tana jin hakan ta cije baki tare da komawa daki da sauri, Maman ta takira awaya tana fadin, "Mama wallahi bazan Yarda ba sai anzub da wannan ma kamar dayan indai INA gidannan ba Sakina ba haihuwa in ba wai ninafara ba."

Mama ta ce, "Kai Safiya ni Wallahi ma har kin bani tsoro dai a kan wannan karamin case din za ki na tada jijiyoyin wuyan ki? To ma za Ina so kizo gida yanzu ki sameni."

Ko wanka Safiya ba tai ba taje dakin Sakina tana, "Faruq Mamana ta na kirana bara naje."

Faruq ya ce, "Haba Safiya bakiga wai Sakina ba lafiya ba ne ke da yakamata ki zauna da ita."

Hararsa ta yi tare da fadin, "Yo to tafi uwata CE? Ni fa kagani na tafi."

Fita tai batare da ta bari ya bata amsa ba.

Faruq ya CE....

Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:16] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_