PAGE-31/32
________________________________________________________
*_Daga yau zan ajiye typing sai Allah ya kai mu bayan sallah,kar amanta dani arabon Neman hilis🤣amman fa ni naman saniya Ina so_*
_wannan fejin na Ku ne,,Yan GRP dina Rukkayya Fulani,Ummu Nana, Aysher shu'aibu,Ummu khairat,,Ummukausar,,Er Hajja,Waya, Hauwa Alhaji Muhammad,,Rabaha,Maman Shukhra,Nafy mudangi,Rahima Adam,da ma sauran oll INA son Ku INA jin dadin sharhin Ku a ajiyemin naman Sallah na😘😘😘_
"Hmm Allah dai yakyauta."
Sakina tai Mumurshi tare da fadin, "Ai da gaskiyarta kuma ma ni naji karfi zan Iya komai."
Faruq ya CE, "Allah ya Sa nidai yanzu babban burina bai huce ace Kin Sauka lafiya ba."
Sakina ta CE, "Karka da mu bakomai insha Allah."
Nan Faruq ya hini agida ya na jinyar matarsa ya kira Maryam ta Dan tayasa wasu abubuwan.
**Safiya na zuwa ta farama mamanta kuka tana, "Mama anya ni INA haihuwar nan kuwa? Ki ga Sakina fa ciki na biyu Kennan to ni wai me ke faruwa da ni ne?"
Mama ta janyo yarta ta zaunar da ita gefenta sannan ta ce, "Haba Safiya ta me ya kawo wannan tunanin? To ma tsaya wai kin manta da ajiyar mu na karkashin gadonta ne? Ai indai abin nan ya na gun to Sakina ba ta isa ta dau ciki har ya zauna ba ko ya fara zama muna nan da ke jikin nan zai zube kamar na farkon."
"Oh natuna Ai ni da hankalina ya tashine Wallahi, to Mama a yi tawa maganar wai ba Yarda xa ayi in sami cikin nan ne?" Cewar Safiya.
Mama tai murmushi tana, "Wannan kam ba abin da muka isa mu yi illa Addu'ah Allahn da ya ba ta shi zai baki."
Safiya ta ce, "Umm to ni kam Gaskiya Adage da Addu'ar nan Dan na matsu."
Mama ta ce, "Iyeee Safiya ni kike fadawa hakan ko kunya."
Safiya ta rufe fuska tare da fadin, "Umm to ni kam Ai Mama na matsu ne."
"Umm to karkiji komai diyar kirki nakusa samu yar jika." Cewar Mama.
Safiya ta ce, "Mama to bara nakoma gidan mukwashi kallo zan kiraki duk yadda akai ma."
Mama ta ce, "Owk ki kula ma yi wayar."
Safiya ta koma gida ta tarar da Faruq sai nan-nan yake da Sakina.
Abin ba karamin takaici ya ba ta ba Amman ta barsar domin tasan abin da ta kulla.
A kwana atashi cikin Sakina ya na cikin wata na uku.
Kullum acikin tashin hankali Safiya ta ke da Mamanta domin sun koma wajen boka yatabbatar mu su cewa wannan abun fa ya na nan kuma ba by shakka ko da cikin Sakina ya kai wata Tara sai ya zube muddin abun bai bar mazaunin Sa ba.
Duk da bayanin da bakon na su ya mu su bai ishesu ba domin sai da su ka cigaba da bin wasu bokayen Wanda duk sukance ai abin ya fi karfin su ba abin da suka isa suma Sakina.
Hakan ya Sa Safiya kudiri niyar zubda ma ta cikin da kanta.
Ta yi girkin dare miyar Ayayo sai da ta bari kowa ya shige daki kan taje dai-dai kofar dakin Sakina ta zuba bayan ta gama zubawa ta na sauri za ta koma kar a gan ta kawai sai gashi ta sule.
Da Sauri Faruq da Sakina su ka fito su ka dagata ban da kuka ba abin da Safiya ke yi tana fadin, "Nazo zan duba jikin Safiyane sannan in huce in zubar shine ya zube santsin ya yardani."
Sai da ya kai ga Safiya ta yi targade akafarta da kyar ta ke Iya tafiya hakan yasa ta hakuri da duk wata mugunta ta zubawa sarautar Allah ido.
Wa ta ranar jumma'ah Faruq da Sakina sun fito za ta tafi shago shi kuma xa shi gun aiki.
Zuwanta kofar gida ke wuya ta fadi kasa.......
Urs Xayyeeesherth [11/08 à 06:17] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_