PAGE-32
________________________________________________________
_*Appy sallah my piple INA jiran nama dai har yanzu shiru inji slinda baby*😋😋_
Jinine kawai ya bara zubowa da ga jikin Sakina.
Faruq ya gigice ya rasa inda zai Sa ransa tuni ya dauketa su ka koma cikin gida Sannan ya kira likitansu.
Kamar yadda akai abaya dai cikin Sakina ya zube, ban da kuka ba abin da ta ke yi haka ma Faruq Wanda ya ka Sa jurewa,, Safiya kuwa na daki ban da murna ba abin da take ta kira mahaifiyarta sai shewa su ke.
Ha ka Sakina ta cigaba da fuskantar kaddarar Aurenta domin kuwa ta na yin ciki ba ya zama ya ke ficewa.
Safiya kuwa ansami abin yi ta fadawa Faruq cewa ai Sakina CE ke zub da cikin da kan ta domin ta ce ita bazata taba hada zuri'ah da dangin da ba Sa kaunarta ba.
Ba karamin bacin rai Faruq ya yi ba da jin wannan kalaman.
Atakai ya je ya cima Sakina mutumci zagi ta inda ya ke shiga ba tanan ya ke fita ba.
Sakina kuwa ta kasa magana ban da hawaye ba abin da ke fitowa Daga idanunta Dan takaici.
"Ki yi ta hawayen munafurci daman ai kin saba kije chan nikam dai Daga yanzu in kin kara ganina dakin ki ma to wani babban dalili ya janyo hakan kije ki ta tsiyarki ni kam na fi karfin ki zanje gun wadda za ta so hada zuri'ah da ni." Cewar Faruq
Ficewar Sa ya yi batare da ya kara kallonta ba ma bare ya saurareta.
Tin daga Ranar Faruq ya bar shiga harkar Sakina gabadaya ko kofar dakin ta ba ya zuwa bare ya shiga ko abinci ne sai dai ta girka na ta ita daya ta ce inko cefane yakare sai dai Shida Safiya suje suyi a ajiye ma ta abakin kofa inta fito ta gani sai ta dauka.
Ya kasancewa Sakina in ba Shagon ta za ta ba to fa indai ta na gida ban da kuka ba abin da ta ke yi shiyasa ta fi jin dadin tafiyanta ma yadda zata shiga mutane su Dan kawar ma ta da damuwarta.
Duk wannan abin da ke faruwa Sakina ba ta taba fadawa kowa ba ko gida ta je aka ce me ke damunta ta kan yi murmushi ta ce bakomai, ta bar abin azuciyarta Wanda ya Sa banda zabga rama ba abin da ta ke
Kullum cikin kunci ya kasance ma d gayya Safiya ke abu in ta ga Sakina.
Har ta kai ga Safiya ta hana Faruq zuwa Niger wajen subai'atu.
Hajiyan Faruq kuwa Abu yafara damunta domin kuwa Safiya ba sarara ma ta ta ke ba agaban ta take mulkinta son ranta a kan Faruq ko ta bukaci da ya ma ta Abu in Safiya ba ta Sa baki ba to fa bazai taba yi ba.
*****Sakina ta fito tana sauri za ta tafi shago shi ga Faruq nan da Safiya, Faruq ya ce, "Ki ma koma ki zauna agida Dan baza a barmin gida ba kowa ba yanzu barayi sunyi yawa Dan haka indai zamu fita bazakina zuwa shago ba."
Har Sakina ta koma daki sai ta fito.
Ta ce, "Faruq ."
Ya juyo ya kalleta .
Ta kara da fadin, "A ganina duk irin wulakancin da Ku ke min ya isa ba sai kahanani sana'a ta ba Dan haka nikam na gaji kawai ka sawakemin na koma gida."
Wani irin da di Safiya ta ji aranta.
Faruq kuwa sai da zuciyarsa ta fara bugun Tara ya ma kasa magana.
Safiya ta ce, "Sweetie ka ma ta abin da take so ma na nikam mu tafi."
Faruq ya ce, "Ai in kinga kin fita agidannan to na mutu ne Amman ba wai na sakeki ba.'
Ya ja Safiya suka fita wanda Safiya ko kadan ba ta ji dadin hakan ba.
Agurin Sakina ta durkusa ban da kuka ba abin da takeyi.
Daga karshe dai ta yanke shawarar tafiya gidan su....
Urs Xayyeesherth❤️ [11/08 à 06:17] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_