PAGE-34
*_jiya na yi mistake page 33 ne na sa 32 duk da feddyna dai ta ce nama naci yamin yawa🤣* ________________________________________________________
_*Fejin nan sadaukarwa gareku en GRP dina Xayyeesherth fans GRP mussaman kawayen SLINDA BABY🤣Ina jin dadin Sharhin Ku acigaba da gashi,,CNT love u less😘*_
Tattara kayanta ta ke tana kuka, kayan sawanta kadai ta diba ta kulle kofar dakin ta sannan ta janyo kofar gidan ma.
Ta ci sa'ar samun napep kuwa ta Dane sai gida.
Ta na isa gida da kuka ta shige a bin da ya bawa Mama tsoro Kennan,,,, Maryam ma ko, ko tsayawa bai tai ba ganin yayarta na kuka tuni itama ta fara.
Mama ta ce, "Me zan gani haka Sakina me ke faruwa ne wai? Sakinki Faruq din ya yi?"
Sakina ta girgiza kai alamar Aa.
Mama ta ce, "To Shikennan Ku shiga ciki."
Aiko kamar yaya haiydar ya sani sai gashi ya zo.
Mama ta ce, "jeka daki ka ga ikon Allah."
Ba musu kuwa Haiydar ya yi dakin Mama inda ya tarar da Sakina ban da zubda kwalla ba abin da ta ke sai Maryam da ke ba ta hakurin itama tana kuka.
Tsawa Ya yi Musu tare da fadin, "Dalla kuma mutane shiru kunbi kun cika ma na gida da ihu."
Zama Ya yi tare da fadin, "Sakina! Kin fara fuskantar kalubali ko? Ba wai komai ya Sa na ki Auren nan na ki illa ina guje mi ki wulakanci da tozartar da za ki fuskanta, yanzu me ya hadaki da shi."
Kan Sakina a kasa ta ce, "Yaya ni wallahi bana sonsa kawai ya sakeni ni na hakura da auren."
Murmushi haiydar ya yi sannan ya ce, "Yau Ku ma Sakina ke kike bukatan Saki da kan ki! Ba ri Baba dai yadawo sai ki yi ma na bayanin komai."
Daddare bayan Baba ya dawo kowa na falo Yaya Haiydar ya bukaci da Sakina ta yi mu su bayani kamar yadda tai ma Sa tare da dalilinta na fadin hakan.
Magana ta ke ta na shshshekar Kuka irin wulakanci, tozarci da halin ko in kulan da Faruq ke nuna ma ta.
A wajen ba Wanda bai tausaya ma ta ba, barin ma Mama da ta ke Uwa, abin ya fi taba ma ta zuciyata Wanda har sai da tai kwalla ga irin azabar da yar ta ke fuskanta agidan Aurenta.
Yaya Haiydar ne ya fara fadin, "Yanzu duk wannan abun da ke faruwa ki ka Sa fadawa kowa kamar ba ki da gata? In Faruq na da laifi 70% to 30% na ki ne wallahi domin da kin fada, da tuni andauki matakin da yakamata Amman kin bijire ke an fada mi ki ana zaman Auren dole ne ma wai?"
Girgiza kai kawai Sakina ta yi.
Baba ya ce, "Ba ma wannan ba shin yanzun ya sakekine ko kuwa cewa ya yi ki dawo gidan?"
Sakina ta ce, "Aa ni na tawo."
Baba ya ce, "Owk Shikennan ai Haiydar Ku barsa in ba wai shi yanememu ba kar wani ya kara tada maganar ."
Haiydar ya ce, "Insha Allah Baba Amman ni fa inma ya zo kawai takardarta zai ba ta domin ita ma ta na da gata ba zai yu ya maidata baiwarsa ba."
Mama dai tana ji ta ma kasa magana kawai tausayama yarta ta ke ga irin yanayin da ta koma.
Faruq kuwa suna dawowa gidan su ka tarar ba kowa ga dakin Sakina arufe bai San lokacin da ya fara zufa ba ya na fadin, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'u kar dai Sakina ta tafi gida, Safiya wallahi bazan iya rayuwa ba tare da Ina ganin Sakina ba, ki je ki dawo min da matata Dan Allah, Safiya ke muguwa CE ke ki ka rabani da Sakinata safi... Bai karasa maganar ba ya fadi a kasa warwar.
Urs Xayyeesherth [11/08 à 06:17] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_