PAGE-35
________________________________________________________
💃🏻💃🏻💃🏻 *Xayyeesherth Fans GRP Ina matukar kaunarku yan GRP dina ma su sani farinciki da nishadi❤️❤️Mussamman masoyan slinda baby🤣kun ga dai tabarar da ta aikata awanga feji*
Harara safiya ta bisa da ita taja dogon tsaki sannan ta dau waya ta kira likitansu.
Dasauri kuwa likinta ya zo domin duba ubangidansa Faruq.
Yana zuwa ya dubasa sannan ya ma sa allura kan ya tafi.
Safiya ko, ko ajikinta sabgar gabanta tafara tare da kiran tsohon saurayinta gidan.
Tabar Faruq dakinsa kwance ita ko tana nan adakinta tare da tsohon saurayinta.
"Kai Baby ba karamin kewarki nai ba fa, yau jina nake cikin wani farinciki Mara misaltuwa domin na farinciki ya dade Da fita arayuwata Ashe akwai ranar har zaki tuna da ni har ki kirani? Humm." Cewar Adam Kennan saurayin Safiya da su ke cin duniyarsu.
Safiya ta ce, "Hmm ni fa daurewa kawai na ke da wancen gajan ni wallahi son sa ma yafara fita akaina kwata-kwata bai iya soyayya ba bai ma San hanyar da zaibi ba."
Dariya Adam ya yi tare da fadin, "Ki CE min da bagidaje ki ke tare yasin na tausayamiki No wonder ma na naga kin kara ramewa kamar bulugari."
Safiya ta daka ma sa duka tare da fadin, "Banason iskanci Adam ni ce bulugarin ko?"
Murmushi ya yi tare da fadin "Aa sorry babyna".
Sakina ta ce, " Kasan miye?"
Adam ya kara matsowa gareta tare da fadin, "Aa sai kin Fada."
"Ni wallahi gabadaya yafara fitamin arai shiyasa na matsu matar nan ta sa tabar gidan Dan kana zuwa muna shanawa ka ga in ta na nan ba damar harka, Dan ba wai ma ni inason cin dukiyar ba ai da tuni na gaba indawo gareka, shi abin da nafi bukatan yaki zuwa (ciki) da nasan daga nan ne zan cigaba da mulkarsa son raina."
Adam ya ce, "Aikin banza indai cikine ba sai kiyi na karya ba daga karshe muje gidan marayu arakito."
Dariya Safiya ta yi tare da fadin, "Wannan ai ba mai yuhuwa ba ne kasan Waye Faruq kuwa? Da ya ma nayi hankalinsa ya fara karkatowa gareni, hmm ayi shiru kawai ni barci ma nakeji ."
Hamma Adam ya fara yi tare da fadin, "Yau wani zai yi kwannan zaune."
Dariya kawai Safiya tai.
********** Sakina na kwance banda tunina farko ba abin da ta ke ta kasa barci kwata-kwata, haka ta kwana cikin sake-sake.
Washe gari da safe Faruq ya farka jiki dai kwari yana ta kwalla safiya kira ya ji shiru.
Daga karshe dai ya rarrfa domin zuwa dakin.
Kan ya isa yana ta jin dariyarta .
Yana zuwa ya fara kwankwasa kofar Safiya na jinsa ta rikice Adam ko tuni ya kulle karkashin gado.
Faruq ya ce, "Safiya ki budemjn mana."
Safiya ta ce, "Kaje dakin ka Ina zuwa ma na."
Da karfi kawai Faruq ya hankada kofar....
Yana shiga.....
*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_