AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-36-37

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

_*My Group Members Ina Matukar Alfahari da Ku Addu'o'in Ku gareni babban makamine a duk in da na ke🥰Allah yabarmin Ku masoyan Asali Son so na ke mu Ku fisabilillah Xayyeesherth ta Ku ce❤️❤️*_

Yana shiga yaga Safiya sai waige-waige ta ke yi.

Faruq ya ce, "Dawa ki ke wayane naji kinata dariya?"

Sosa kai Safiya ta fara tana fadin, "Wallahi Wallahi Mama CE Au Kawata Zainab zan ce."

Faruq ya ce, "Anya akwai kamshin Gaskiya kuwa duk kin wani dibibice kin rikice to ni bama wannan ba wanka nakeso nayi kinga jikina ba kwari." Karasa maganar ya yi tare da nufar bakin gado domin ya zauna.

Da Sauri Safiya ta taresa tana fadin, "Aa muje dakin ka in hadama ruwan ka yi ni hitata ta samu matsala ai dazu."

Faruq ya ce, "Kai Safiya Amman baki kyautamin ba da kin fada ai naturo a gyara Amman muje chan din to."

Safiya ta bi bayansa ta na ma sa gwalo tare da fadin, "Ai ma naga jikin na ka ya yi kyau muje."

Tana raka Faruq ta hada ma sa ruwan wanka sannan ta yi sanda ta dawo dakinta domin fitar da Adam.

Ta na zuwa kuwa ta tarar Zai fitan ma Kennan.

"Yauwa munsha dakyar wancen gajan bai ganmu ba."cewar Safiya.

Shi ko Adam Kiss kawai ya ma ta sannan ya ce, " Byee byee ni da fatan gobe ma akuma." Maganar ya ke ya yin da ya fita yana ma ta bankwana da hannu.

Safiya ta ce, "Karkaji komai ai yanzu aka fara wasan."

Dariya kawai ya bita da shi yayin da ta komo gida shi kuma ya tafi.

Tana komawa ta tarar Faruq ya fito shagwabe Fuska tai tare da fadin, "Sweety kasan mi ye?"

Girgiza kai kawai Faruq ya yi.

Ta ce, "Ni Wallahi har ka fara bani tausayi ace wai kana son wadda ba ta damu da kai ba kwata-kwata ai ko da ace kullum Jajjagenta mu ke indai tana sonka to ba inda zata ka ga fa kahanata fita Amman da yake tana ji da girman kai shine ta fita inaga yanzu sun rasa abin yi ne anje gun bokayen an kasa mallakeka shine a ka tsiri barin gidan kuma."

Faruq dai ya kasa magana sake-sake kawai ya ke yi wata zuciyar na tabbatar ma sa da cewa maganar Safiya gaskiyace wani bangaren kuma na fadin cewa Sakina ba za ta taba ma sa haka a son ranta ba.

Safiya dai taga alamar har yanzu bai gama gamsuwa ba .

Hakan yasa ta fara kukan munafurci tana fadin, "Ni da nake sonka na ke binka kamar mayya Amman kana wulakantani ita ko kana binta tana kinka ai Shikennan kata son na ta ni dama mutuwa na yi na huta nagaji ita da kakeso ai gashi kana ta ma ta ciki tana zubarwa ni kuwa kaki ko sau daya ma." Kara feshewa da kuka tayi tare da fadawa jikinsa.

Tuni ta jagwal-gwala ma sa tunaninsa hankalinsa ya dawo gareta kawai.

***Misalin karfe 2 dai-dai Hajiyan Faruq ta nufo gidan domin likita yasanar da ita cewa Faruq ba lafiya.

Afalon Safiya ta tsincesu Faruq na zaune safiya kuwa ta kwanta ajikinsa.

Tana jin sallamar Hajiya ta kara k'ank'ame Faruq ba ta da alamar tashi bare ta amsa sallamarma.

Hajiya na shigowa tai saroro ganin Faruq da Safiya ahaka.

Faruq ne ya amsa tare da fadin" Ina kwana Hajiya."

Ka sa amsawa tai tana fadin, "Me zan gani haka Faruq ko da anganni ba a tashi haka ba? Safiya ko gesuwa ma ban isheki ba ko?"

Wata irin masifaffiyar harara Safiya ta gallawa Hajiya yayin da ta tashi ta yi wani hamshakin Tsaki sannan ta nufi daki tana fadin, "In ni ban hau jikinsa ba inaga ke kikeso ki hau jikin na sa ko ince ki auresa ma."ta shige daki abinta.

Hawaye kawai ke zuba daga idanun Hajiya ta na fadin, " Lallai wannan shine halaccin da zaku min ke da mahaifiyarki ba laifinki ba ne nawa ne nagode."

Ta dubi Faruq sannan ta kara fadin, "Ina Sakinar ta ke?"

Faruq ya fara Sosa k'eya yana fadin, "Jiya ta tafi gidansu."

Hajiya ta kasa fadin komai fita kawai tayi agidan tana kuka.

Sakina.....

Urs Xayyeesherth

*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_