PAGE-38
________________________________________________________
*_Xayyeesherth fans group Ku ji dadin Ku da wannan fejin na gode da addu'o'in Ku gareni🙏domin ku kadai nai wannan kuntun typing din❤️_*
Sakina na zaune ta yi jigum ban da tunanin Faruq ba abin da ta ke aiyanawa aranta, Mama ce ta karaso garete ganin shirun ya ki ci ya ki cinyewa, "Haba Sakina me ya sa ki ke so ki kara jefa rayuwarki cikin wata ukubar? Na lura tin da ki ka zo gidan nan kin kasa sake ranki, to in baki sake anan ba ina zaki sake?"
Murmushi Sakina tai tare da fadin, "A yi hakuri Mama insha Allah zan kiyaye."
Mama ta ce, "Yauwa diyar kirki Dan nasan tunanin ki bai huce a kan Faruq, abin da ciwo ace kiri-kiri gidanka ya fi karfinka Amman karki damu Addu'ar nan dai da mu ke itace mafita sannan zan ba da sadaka ma domin a kara tayamu da Addu'Ah Dan ina da wata tantama akan Safiya Amman bakomai Allah ya fita kuma ya na gani."
Murmushi ne kawai ya fara bayyana afuskar Sakina ta ce, "Nagode sosai Mama ke ce uwa ta gari wadda ko wa miji ke bukatar samun uwar 'ya'ya kamar ki, ina Alfahari da ke Mamana duk da irin son da ki ke mana hakan bai hanaki tsawatarwa garemu ba tare da nuna ma na hanya madai-daiciya, Allah ya bar min ke Mamana." Karasa maganar tai tare da kwanciya ajikin mahaifiyarta ta.
*Wannan ita ce Uwa ta gari, mace tagari sannan kuma tauraruwar al'umma Allah ya ba mu ikon aikata alkairy tare nuna hanya ma fi kyau ga 'ya'yan mu har ma da na wasu....*
*****Shigewa daki Faruq ya yi, Safiya ya tarar ta na kwalliya gaban mirror, Faruq ya ce, "Safiya ina za ki kuma bayan kin San ba isasshiyar Lafiya gareni ba, ba ma wannan ba yanzu abin da ki ka ma Hajiya ya kamata kennan?"
Juyowa tai ta ma sa wani matsiyacin kallo tare da fadin, "Anguwa za Ni kuma baka isa ka hanani ba, sannan maganar Hajiya kuma ai Gaskiya na fada in son ka ta ke sai inbar ma ta kai ka Aura."
Abin ya matukar batawa Faruq rai Amman ya ka sa magana ko miye dalilin hakan oho,, ji ya yi kawai ya fara jin haushin kan sa.
Safiya kuwa ko ajikin ta kwalliyarta ta karasa sannan ta dauko wa Ni karamin mayafinta tana, "To malam ko saj na yi maganane za ka matsamin ahanyar?"
Faruq kawai tsintar kan sa ya yi da matsa ma ta Amman ba Dan zuciyarsa na so ba.
Kara ma sa kallon banza tai tare da fadin, "Sak'ago kawai." Ta yi ficewarta ba tare da ta kara waiwayarsa ba.
A gurin kawai ya durkusa ya na kukan miye dalilin da ya sa Safiya za ta bakanta ma sa son ranta Amman ba zai iya budan baki ya yi magana ba.
Gaba daya ji ya yi ya tsani kan sa domin kuwa ya rasa me ke damunsa ma.
Safiya na fita kuwa tai wajen Adam su ka cigaba da sharholiyarsu, sai Misalin karfe Tara n dare ta dawo, Faruq na ganin ta maimakon ya fara ma ta fada Amman sai ya tsinci kan sa da ma ta barka da dawowa.
To kallonsa ba tai ba ta nufi dakin ta ta kulle kofar.
Washe gari, da sassafe Maman Sakina ta Tara malamai domin Sauka Wanda babama ya na chan ya Tara nasa ba tare da sanin ta ba.
Sakina ta sake sose da jin irin nasihar da mahaifiyarta ta ma ta Amman abun da ya fi ba ta Mamaki shine wai Tun da ta dawo gida ko lek'ota ma Faruq ya kasa.
Abangaren Faruq da Safiya kuwa...
Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_