AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-39/40

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*Baby love tnx for d song😘😘i really like ita*

*Ina ki ke Mrs Habeeb marubuciyar lauratu wannan fejin kacokan sadaukarwane agareki ki ba wa Wanda ki keso ya karanta Amman ban da Kawu atk😉*

Ba magana harkarta ta ke yi domin kuwa ko abinci na ta daina girkawa kullum sai dai ya fita waje ya ne ma.

Safiya sharholiyarta ta ke son ranta ba mai tanka ma ta.

Hajiyan Faruq ta yi matukar nadama da danasani akan lamarin aminiyarta da diyarta , hakan ya sa fara bin malamai domin nemawa kan ta da 'Dan ta mafita.

Rokon Allah ya ta shi gadan-gadan ko wa ni bangare kawai yi a ke.

Safiya da uwarta kuwa sun cigaba da ma ka tsiyarsu da makircin su ba tsagaitawa kamar zigasu a ke.

Washe gari

Da sassafe Hajiyan Faruq ta nufo gidan, ta na zuwa kuwa ta tarar da Faruq tsaye atsakar gida ban da sake-sake ba abin da ya ke aransa.

Hajiya ta ce, "Yauwa Faruq zo muje."

Rik'o hannunsa tai ta na murmushi ba mu su ko Faruq ya bita.

Ba inda su ka nufa sai gidansu Sakina.

Jiki Asanyaye Hajiya ta shiga, shi ko Faruq tin da su ka je k'ofar gidan gabansa ban da faduwa ba abin da ya ke.

Fitowa Sakina daga daki Kennan sai ga shigowarsu, saroro kawai Sakina ta yi ganin abin da ba tai tsammani ba, Faruq kuwa ya ma kasa magana ban da hawaye ba abin da ke zubowa daga idanunsa.

Murmushi Mama tai tare da fadin, "Sannu dai Sakina ina Mama ta ki ta ke?"

Sakina ta durkusa ta ce, "Ina kwana Hajiya, Ku shiga Suna ciki." Ta ma su alamar shiga falon da hannu.

Ba karamin Mamaki Mama tai ba ganin Hajiyan Faruq da faruq murmushi tai tare ba su wajen zama Sannan ta sa Maryam ta kirawo Babansu.

Bayan sun gama gaisawa ne Hajiya Faruq ta fara jawabi.

"Dafarko dai ina mai ba Ku hakuri da dukkan lamarukan da su ka faru daga gareni da ma d'ana faruq, na gane kuskureni kuma na yi nadama ko ince wa inda na ke ta tsiyar Dan su, sun nunamin halarci na fahimci inda na dosa ba hanya ba" ce me fillewa, nuna faruq tai tacigaba da fadin, "Shi da na ke gadarar da shi anfara rabani da shi kamar yadda a ka rabasa da matarsa, Ku yafemu Ku gafarce ma na domin yanzu ma daga nan gida zan kai sa anata faman ma sa Sauka."

Babane ya yi gyaran murya ta re da fadin, "To Alhamdulillah dai zan ce tin da yanzu kin gane kuskurenki kuma kin fahimta, Faruq kuwa shi ma sai dai mu CE Allah ya kara kiyayewa, Amman fa zan iya cewa da lafinsa adukkan abin da ke faruwa domin kuwa ya na wasa da ibada, Sannan kuma ya na biyewa makircin mace Wanda inkace za ka bi to bazaka taba ganin dai-dai ba arayuwarka domin makirar mace babbar illa ce ga al'umma, kin gan mu nan tin da Sakina ta dawo gida ba mu zauna ba kara dagewa mu ka wajen Addu'o'i da rokon Allah, Sauka kuwa ba fashi kullum sai anyita.

Faruq dai na zaune kasak'e ban da hawaye ba abin da ke fita daga idanunsa ya na jin duka abin ake fada Amman ya ka sa koda magana daya ce.

Hajiya ta ce, "Godiya na ke da fahimtar da Ku kai min Amman na ce Dan Allah ko Sakina zata koma gidan Faruq ba yan komai ya dai-daita? A taimaka Dan Allah, Dan yanzu ma nasan innace ya saki Safiya ba abin zai taburane na bari yadawo haiyacinsa."

Baba ya ce, "To Maganar Gaskiya dai ban jin cewa Sakina za ta kara komawa gidan Faruq , Sannan kuma maganar ya saki matarsa ba ta ki bace, Fatan mu anan shine Allah ya yaye ma sa ita kuma Allah ya ganar da ita zuwa hanya madai-daiciya Maganar Sakina kam abarta Dan yanzu ma anfara maganar komawarta makaranta ne."

Ba dai haka Hajiya ta so ba Amman haka tai godiya Sannan su ka tashi ita da Faruq, Sakina na daki ta na jin duk abin da ke faruwa kamar yadda Faruq ke zubda kwalla haka ita ma ta fara zubarwa.

Mama ce ta raka Hajiya da Faruq har bakin gate sannan su kai sallama ta dawo gida.

Hajiya kuwa gida su ka nufa ita da faruq inda malama su ka cigaba da karatu da Addu'o'i, tuni kwakwalwar Faruq ta fara jagwal-gwale ta rikice gabadaya Wanda hakan ya sa shi yin wani barci da bai taba yin irin sa ba.

Safiya kuwa na gadj rashin ganin Faruq da ba tai ba ko ajikin ta sabgoginta ma ta ke sai kiran Adam da tai cikin gidan.

Tare su ka kwana suna sharholiyarsu...

Washe gari

Tin jiya karfe 2da Faruq ya fara barci a dakin hajiya bai farka ba sai Sa karfe biyar na yammacin yau, ya na farkawa ya fara fadin, "Mama ina Sakina ta ya jikinta, Ina ta ke Safiya ba tai.......

Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_