PAGE-41-42
________________________________________________________
*_GROUP MEMBERS😘YAU ZAN YI WALIYAR LAUNIN FATA WA IN DA KADAI BASA GAZAWA WAJEN MIN SHARHI ZANWA KYAUTAR FEJIN NAN DOMIN NASAN XASU FI KOWA JIN DADI GAREKU MASOYAN ASALI⬇️_*
_*RUKKAYYA FULANI,BABY LOVE,FIRDAUSI,RAHIMA ADAM,UKTY UMMI,WALIDA,MAMAN SHUKRA,MAMAN KHAIRAT,MOMYN IHSAN,HAWWA MUKTAR,HAUWA ABUBAKAR,UMMI JAMILAT,FATIMA ZAHRA, HAFSAT,MAMAN RUKKY, MARRIYA DAUDA,AISHA SHU'AIB, JIDDATY,SISTER,NAFY MUDANGI, PRINCESS OF LIGHT, MAMAN RUMASA"U, MAMAN USMAN,RAHABA🥰🥰I HEART U OLL MASOYAN ASALI SON SO SABIDA ALLAH*❤️❤️_
******* ******* *******
Ma ta komai ba ko?"
Murmushi Hajiya tai tare da fadin, "Alhamdulillah yanzu dai kaje kai sallolin da ake bin ka tin na jiya kan sai ka zo mu yi magana."
Bai karacewa komai ba Ya tashi ya dauro alwala sannan ya yi sallolinsa ya na idarwa kuwa bai ko karasa wajen Hajiya ba ya yi saurin ficewa domin komawa gidan sa.
Tuki ya ke yi cikin sauri Amman duk da hakan ya Gaza gani ya ke kamar motar ba ta tafiya.
Ya na zuwa kofar gidan ya jefar da motar ba tare da yayi kwakkwaran Pakin ba .
Da sauri ya shige gidan ba inda ya nufa sai dakin Safiya ya yi sa'a kuwa tabar kofar abude, ya na bugawa ta bude kuwa ya yin da ya ga abin da ya sa shi suman tsaye, Safiya ce kwance da Adam suna lalalata ba su ma lura da shigowarsa ba kasancewar sunyi nisa a iskanci.
Da Faruq ya mu su wata gigitacciyar tsawa sai da Adam ya ji sa a kasa, Safiya kuwa kallo kawai ta kura ma sa tare da fadin, "Miye ha ka zaka shigomin daki ba sallama?"
Faruq ya ce, "Au tambayata ma ki ke? OK bara nafara gama da wancen karamin Dan iskan kan nadawo gareki."
Cire bel din sa ya yi ya fara zabgawa Adam ba ji ba gani tin Adam na ihu har ya ga ji ya yi shiru, sai da Faruq ya fara nishin wahala kan ya kyale Adam.
Tin ni kuwa Adam ya ja jiki wando ahannu ya fice.
Kukan munafurci Safiya ta fara tana fadin, "Faruq Dan Allah ka yi hakuri wallahi shine ya sa ni dole."
Karasowa Faruq ya yi yana numfasa ya ce, "Ina ni ki ke Tambaya na shigo mi ki daki ba sallama ko?"
Tuni ya fara dukanta sai da ya ma ta jaga-jaga jini ta baki ta hanci.
Sambatu kawai ya ke, "Wa to ni kin maidani boyi-boyi ko? Kin je kinyi tsubbunki kin rabani da farinciki kina snnan Ku ma ki zo ki na cin amanata? Kin maidani Dan iska Kennan ko?"
Sai da ya jibgeta son ransa sannan ya fige zuwa kofar gida ya ce, "Wallahi ki barmin gida ba na bukatar kara ganin kazantaccen jikin nan na ki, ki je chan ki karasa iskancinki.
Ba komai a jikin Safiya sai wa ni da mayafi Wanda shima din akanta ya ke ta zaro ta daura ga Faruq ya kulle gidansa bare ta shiga ta sa kaya haka ta fara tafiya da kafafunta domin zuwa gida.
Ahanyar komawarta gida ban da ihu ba abin da yara su ke ma ta suna mahaukaciya gabadaya ta rikice ban da kuka ba abin da ta ke yi har ta isa gida.
Ta na shiga Mama na ganinta ta sume ta ke awajen.
****A bangaren Faruq kuwa Ya kulle gidan ba inda ya nufa sai gidan su Sakina,,,
Ya na zuwa ya tarar da Yaya Haiydar tsaye ajikin gate wani mummunan kallo yaya Haiydar ya ma Faruq, Wanda shi ko kawai durkusar da kai ya yi azuciyarsa ya na fadin ," *ba a ma yi ba ya a ka kare bare anyi kuma ai sai ta Allah*."
A zahiri kuwa gaida Yaya Haiydar ya yi.
Murmushi yaya Haiydar ya fi sannan ya amsa.
A bin da ya bawa Faruq Mamaki Kennan Wanda ya kai ga ya kusa summan tsaye.
*A jiya bayan tafiyan Mama da Faruq ne yaya Haiydar ya zo a ka ma sa bayanin komai ba karamin tausayawa Faruq ya yi, sannan kuma ya ji dadin gane kuskuren da hajiya ta yi ta kuma gano hanya madai-daiciya, duk da kasancewar hakan ya faru Amman baya fatan komawar Sakina gidan Faruq kamar yadda Baba ma haka*.
Bayan sun gama gaisawa ne Haiydar ya ja Faruq su ka shiga gidan domin ga dukkan alamu Haiydar ya fahimci cewa Faruq ya sami sauki ya dawo dai-dai.
Sakina na jin Muryar Faruq ta ji wani irin farinciki aranta da sauri ta koma daki, kasancewa ta gansa cikin kwanciyar hankali ba kamar jiya ba ta yi hamdala ta godema Allah, Amman alokaci daya ta chanja yanayi ta fara kuka.
Faruq bayan sun gama gaisawa da su mama sannan su ka masa murnar samin mafita Baba kuwa fada ya ma sa sose akan yadaina wasa da ibada ya rikye Addu'o'i dare da rana.
Bayan Baba ya kammala ne Faruq ya nemi alfarmar da Sakina ta koma dakin ta,, anan ne fa Baba da Yaya Haiydar su ka ki Yarda fur Wanda ita dai kam Mama tanason hakan har cikin ranta domin farincikin 'yarta.
Jiki a sanyaye ya fito zai tafi kawai sai ya hange sakina ta window.....
Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association___
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_