AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-42/43

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*_Ina ganin sharhin Ku yan group dina Xayyeesherth fans Group Ku min afwan rashin reply network ne ke wahalar dani wallahi🤦‍♀️amman duk INA gani kuma INA sane da ma su yi da yan labe ma🙁🙁 sannan INA jin dadi❤️_*

*******

Ban da zubda kwalla ba abin da ta ke, suna hada ido ta kakalo murmushi sannan ta daga ma sa hannu.

Wani irin yanayi Faruq ya kara tsintar kan sa aciki kawai daurewa ya yi shima ya kakalo murmushin sannan ya fita.

Maganar zuci ya ke, "Allah sarki, Sakina baiwar Allah ita yakamata ta fara fushi da ni Amman ba tai ba, Allah ya sa ka mi ki da alkairansa matar Aljanna."

Ya na gama fadin hakan azuciyarwa kawai hawaye ya fara fita daga idanunsa da sauri ya shige Mota ya kwashi wajen minti talatin kan ya fara diraibin.

****A bangaren Safiya kuwa sauri tai tasa kaya sannan ta kira mutane a ka taimaka ma ta su ka kai Mama asibiti, gado a ka ba su domin tashin ba na yanzu ba ne.

*************

Annemwa Sakina Admission za ta cigaba da karatunta a polytechnic da ke cikin garin Bauchi.

Faruq ya na nan lamarin duniya ya ishe sa kullum sai ya bi Sakina Makaranta tun safe sai yamma, Sakina ta kan tsaya sudan yi hira domin itama ta na cike kewarsa.

Yau ma kamar kullum Faruq da Sakina zaune ta fito sallah daga lectures, Faruq ya ce, "Sakina ni kam dai Ina ganin mutuwa zanyi wallahi domin rayuwata ba ta da amfani, su Baba da Yaya sun kasa fahimtar me na ke ji a cikin zuciyata wallahi, Wallahi ciwon zuciya nadab da kamani Sakina."

Sakina tai murmushi tare da fadin, "Ko mai ya yi zafi maganinsa Allah, irin wannan maganar ba ta kamaceka ba sam, ko dai ba Faruq dina ba ne?"

Murmushi ya yi ya ce, "Faruq din Sakina ne a gaban Sakina ba wani bayan ni, Amman kinsan cewa abun ne ya min yawa narasa Ina zan sa raina ko Niger ma na kasa zuwa domin so na ke muje da ke sai indauko subai'atu ko zauna tare ko?"

Sakina ta ce, "A ba ya ma anrabamu fiye da hakan kar ka manta ka sakeni aranar aurenmu sannan an hargitsa aurenmu tin kan adaura to Dan kuma yanzu munyi auren mun rabu batare da ka sakeni ba to miye abun damuwa anan? Kar ka manta fa har yanzu ni matarka ce, ko da a ce bazan koma gidanka ba ina ba ka shawarar da ka je ka dauko subai'atu domin nasan ita kam ba ta matsala kuma baza asamu ba insha Allah."

Durkusawa Faruq ya yi tare da rikwo hannun Sakina ya na fadin, "Sakina Dan Allah ki min rai ki fadawa su baba zaki dawo gidana, ni na amince na Yarda zaki cigaba da karatun acikin gida, ina sonki Sakina ina so na rayu da ke."

Kara damkye hannun Faruq sakina tai ta na, "Na karbi kaddarar rayuwar Aurenane kawai Dan nasan ba abin da zan iya duk da kasancewar Allah ya Riga ya tsara dole hakan zai faru da ni Amman kasan miye musabbabin hakan? Kin biyayyawa wa iyaye ta bangarena da na ka dafarko mahaifina ya yi burin na yi karatu tin ina da karancin shekaru Amman fir na ki bin umarninsa na nunacewa ni fa Aure na ke so, a lokacin da na fadi hakan nasan cewa bai ji dadi ba Amman ko kadan bai nunamin ba kasan miye dalilin? Sabida yafifita farincikina fiye da Nasa alokacin ya manta da duk kudin da ya kashe akaina ya koma kan burina da na sa gaba alokacin, ka ga wannan fannina kenan, a na ka fannin kuwa dafarko mahaifiyarka ta ki Yarda akan ka aureni ta nuna cewa ba ta so na ba ta son tahada jini da ni, to a lokacin da ace duk munyi Hakuri munyiwa iyayen mu biyayya da hakan bai faru ba, ka ga dani da kai da Mama dukkan mu munyi kuskure awannan lamarin Amman sai dai mugodewa Allah tin ya na son mu kuma har ya nuna mana laifin mu tin kan muje ko ina, yanzu Abu mafi mahimmanci agaremu shine mu ma su biyayya sannan mu barwa Allah zabi."

Faruq da tin da Sakina ta fara magana ya yi shiru kawai ya zubawa sarautar Allah ido.

Ko da tai shiru sai da ya yi jim kan ya ce, "Maddala da samun mace ta gari, tauraruwar al'umma ke din Haske CE ga duk wa ni Wanda ke tare da ke, ina Alfahari fa ke kuma nagane kuskure domin ni musababbabin komai da na rufe mi ki ido da soyayya ta ki ya femin Sakina."

Saukar ma sa da hannunsa tai tana fadin" Allah ya yafe mana."

Da sauri Sakina ta kalli Agogonta ta ce, "Laaa kai Sweetyn ka sa har an koma ban sa ni ba."

Murmushi Faruq ya yi ya ya ce, "Ayya Sorry Matar kirki mu je in rakaki ma yi waya ko?"

Daga ma sa kai kawai Sakina ta yi sannan ya rakata har bakin lecture room ya koma.

*** Safiya na nan kudi ya kare na maganin mama sun gama sai da kayayyaki Amman kullum abin da ake bukata daban....

Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_