PAGE-44/45
________________________________________________________
Faruq na nan kullum cikin tunanin danuya ya rayuwarsa za ta kare babu sakina aciki? Maganganun Sakina ne kadai ma su kwantar ma sa da hankali a yayin da ya tuna sai ya ji bakinciki ya nisanceshi sai farinciki.
Sai da aka diba wajan watanni biyar Sakina na zuwa makaranta abin ta Faruq ma ya cigaba da rayuwarsa kamar da Amman fa kullum ya na tare da Sakina kan ya tafi gun aiki da kuma inyadawo sai ya biya ta skul ko shago yadubata.
Duk da kasancewar Mama da Baba har ma da Yaya Haiydar sun fahimci cewa Sakina na tare da Faruq Amman ba su nuna ma ta ba sannan ma ba su nuna damuwar su akai ba.
Ranar Asabar kwatsam Baba ya dawo daga wajen aiki ya ce akira ma sa Sakina.
Kowa na zaune ana jiran jawabin Baba ai ko ya fara da, "To Masha Allah na ji dadin ganinku du ka awannan lokaci daman dai magana ce a kan yar uwarku ." ya nuna Sakina ya yin da idda maganar.
Ya cigaba da fadin, "Kin ga dai zama agida ba na ki ba ne a matsayinki na 'ya mace gidan mijinki shine darajarki Dan haka na yanke shawarar nema mi ki mijin Aure."
Tuni Sakina ta ji gabanta ya fara faduwa azahiri kuwa wa ni irin murmushi dole ta kakalo.
"Nasan za ki yi Tunanin cewa Ai Faruq bai sa ke ki ba na ke fadin ki yi Aure ko? To Albishirinki diyar kwarai yar albarka ina mai farincikin sanar da ke cewa za ki koma gidan ki gidan mijinki, domin abin da ya sa mu ka jinkirta kuma mu ka ki neman Saki munaso mu ga iyaka yadda lamarin zai kasance ne domin ina gudun ka da a kara wani kuskuren kamar yadda aka yi a baya, munyi magana da Yayanki Haiydar ya ba ni goyon baya Dari bisa Dari domin na fahimci cewa hadinki keda Faruq sai Allah ba Wanda ya isa ya raba, da wannan na ke fada mi ki cewa ki sanar da Faruq ya zo yadaukeki ki koma dakinki Dan duk nan munsan kuna tare kawai zuba mu Ku ido mu kai."
Tuni Sakina ta ji wa ni irin sanyi aranta, "Murmushi ta ke Amman hawayen farinciki bayyana afuskarta, tuni ta tashi da gudu ta nufi daki.
Dariya CE kawai ke tashi a falon ganin yadda Sakina tai, Yaya Haiydar ne ya katse su da fadin, " Ni fa ina da magana Gaskiya ban Yarda ba."
Kowa ya tsura ma sa ido.
Murmushi ya yi sannan ya ce, "Bazan Yarda da komawar kanwata ba indai ba za a chanja ma ta komai na daki ba sannan akara sabon taro domin tayata murna ta manta da baya ta sa gaba aranta da shine farincikin da mu ke ma ta fata."
Dukkan su murmushi su ka yi Mama ta ce, "Wannan ai na ka komai na hannun babban yaya."
Hira suka cigaba da yi cikin farinciki da walwala.
Sakina kuwa na shiga daki ta kira Faruq awaya.
"Albishir zan ma Amman sai ka fada min wace irin kyauta zaka min?" Cewar Sakina.
"Ummm Auntyna ni Sakina. ban da lafiya ina wata kyauta ni indai ba ke zakimin kyautar kan ki ba ai ni bana bukatar komai, Sakina wallahi ni kam nagaji nakasa jurewa ina jin kamar zan bar duniya ayau dinnan."
Sakina ta ce, "To na ji nikam yi shiru ka ji, ina dai Sakina ka ke so? Baba ya ce ka zo ka daukeni mu koma gida."
Wani irin ihu faruq ya yi tare da fadin, "Gani nan zuwa yanzu, Dan Allah dai da gaske ki ke ko Sakina? Ko da mafarki na ke,indai mafarkine Dan Allah karki tasheni in farka."
Dariya kawai sakina ta fara tana, "Allah am serious natabaa wasa irin wannan?"
Tuni Faruq ya fara hamdala ya na fadin, "ganinan zuwa yanzu zan zo mu tafi, ki jirani please."
Sakina ta ce, "Kai dauki to ba yau ba ai sai anshirya biki tukunna kuma ma naji kaman Yaya Haiydar na fadin za azo akwashe kayan akawo wasu."
Faruq ya ce, "Alhamdulillah duk da haka dai gani nan zanzo na ganki wallahi har na warke karki damu ki Bini bashin kyauta inna dawo seti kin San yanzu giyar son ki na kai na."
Katse wayar ya yi kawai ya nufo hanyar gidan su Sakina.
ya na isa ya kira Sakina Awaya kan cewar ta fito, ta ce Aa ya shigo kawai.
Kana ganin Faruq za ka ga farinciki ya bayyana a fuskarsa.
Ya na shiga....
Urs Xayyeesherth*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_