AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-46

by @xayyeesherthulhumaerath

πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š ________________________________________________________

Ba inda ya nufa sai dakin Mama, da fara'a kuwa Mama da Baba su ka amshe sa.

Waige-waige kawai ya ke yi Dan ganin ta ina Safiya za ta fito?

Yaya Haiydar ne ya lura da hakan ya ce, "Kar ka ji komai nan da jibi za ka tafi da abarka Dan angama komai, ko dai zaka Dan bar ma na ta kara sati ne Dan ba mu gaji da ganin ta ba."

Murmushi kawai Faruq ya yi, ya fara Sosa kyeya sannan ya ce, "ai ba komai in dai za ta koma din an gama min komai."

Dariya kawai su ka yi daganan kowa ya fita ya bar Faruq Sakina ta shigo su ka fara shan love, Faruq ji ya ke kamar kar ya rabu da sakina aranar domin wani tsantsan sonta ne ke kara shiga zuciyarsa.

*Yan Group din Xayyeesherth Fans Group kuwa sai murna su ke yiwa Sakina ban da kayan tsimi na 'ya mace ba abin da su ke kawowa mussaman Admin Ambeby,Tare da Maman Shukra sun dage sai sun maida Sakina Amarya*

***Daga ranar zuwa washe gari a ka kammala komai ya yin da akaje kwashe kayan danki Sakina kuwa anci karo da loyoyi na karkashin gado Dana kasan kujeru har ma da kicin, ba Wanda ya yi mamakin ganin hakan domin kuwa Safiya ta yi a kan faruq ma bare Sakina, sai da a ka chanja komai na dakin tsaf aka saka sabbabi, Faruq kuwa sai da ya karama Sakina setin akwati na tukwicin albishir din komawa.

Walima a ka hada akayi saukan Al'Qur'ani sannan a ka ci a ka sha .

Washe gari ma komawar Sakina sai da akaje gidan akai Sauka sannan kowa ya watse.

Sakina da Faruq jin su suke kamar amare Wanda zance ba su yi irin wannan farincikin ba ko a darensu na farko.

Faruq ne ya shigo dauke da gatuwar bakar leda ban da kamshi ba abin da ke tashi a dakin.

Zaune Sakina ta ke akan kujera chatting ta ke da yan Xayyeesherth fans group da ke WhatsApp ban da murmushi ba abin da ke bayyana afuskarta domin kowa murna ya ke tayata gashi sai tsokanarta su ke ma su korarta ta Sauka na yi ma su cewa ta zauna na yi.

Tin da Faruq ya shigo ya kasa karasowa gareta murmushi kawai ya ke ya yin da ita ma ta dago ta kallesa ta mai da ma sa da wani murmushi mai sanyaya zuciya.

"Ba za ki ajiye wayar nan ki min oyoyo ba." Cewar Faruq.

Shagwabe fuska Sakina ta yi tare da girgiza kai ta na, "Umm umm ni bazan iya tashi ba."

Da murmushi Faruq ya karaso gareta, "Ai ni ko zan karaso na mi ki abin da ya fi wannan."

Amsar wayar ya yi ya na, "To A ajiye wannan tin kan fara kishi da ita."

Daukatanta ya yi chanchank ya na, "Oyaa mu je ko?."

Dukan sa da hannu sakina ta ke tana kara shagwabe ma sa Wanda ke kara ingiza shi.

**Kwanan farinciki, cike da nishadine ya kasance acikin gidan Faruq da Sakina.

Bayan Sati daya da dawowar Sakina Faruq ya je yadauko Subai'atu.

Ba karamin jin dadi Sakina tai ba domin da ka ga subai'atu za ka San cewa ba ta da matsala, zama suke cikin nishadi da walwala.

Hajiyan Faruq ban da soyayyar da nuna kulawa ba abin da ke tsakanin ta da surukanta.

**Safiya kuwa Mama ta yi mutuwar wulakanci domin korarsu a kai a asibiti sun ka sa biya gashi ba Wanda su ke ragawa a family din su bare wani yayi tinanin taimaka ma su, Mama na mutuwa rayuwar Safiya ta kara rikicewa ta koma bara daga karshe ma dai ta haukaci.

Sakina kuwa ta koma makaranta, Subai'atu ma Faruq ya nema ma ta duk randa ba su da makaranta sai su je shagon Sakina tare, in Faruq ya dawo ya biya ya dauko su.

**Zaune su ke suna cin abinci ban da shewa ba abin da ke tashi a gidan da gudu Sakina ta, tashi ta shige toilet ban da Amai ba abin Da ta ke yi, tuni Faruq ya kai ta asibiti ai ko aka tabbatar da cewa tana da ciki wa ta biyu, ba karamin farinciki Faruq ya yi da jin hakan da ga hajiya har Subai'atu kowa murna.

Watan cikin Sakina tara dai dai ta haifo yan uku, maza biyu ma ce daya *Fadil,fahdil,nd little fadila*

Anyi shagali an karshe kudi kamar ba asan yadda a ke samowa ba Dan tsantsan farinciki.

........

Bayan shekara biyu Subai'atu CE zaune da tsohon ciki sai ga Sakina ta fito ta na fadin, "Mai tumbi sannunki da zama."

Subai'atu ta CE, "Aunty Allah ni kidaina cemin mai tumbi ai ke ma kina da shi."

Dariya Sakina ta fara, "A'a wlh kar kimin sharri ai Fadila CE Auta."

Faruq ne ya shigo ya na fadin, "Wa ya fada mi ki? A I kina shirya sai kin Ajiyemin dozin."

Murmushi Sakina tai tana fadin, "In dai wannan ne kaddarar Aurena na karba ko da dozin biyune za su zo su huce kamar yadda azzawajul-mukaddar ya zo karshe."

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah

*_Yau dai Allah ya yi , Ina godiya da Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai dumbin masoya cikin koshin lafiya, ya ubangiji ya Allah ina rokonka da ka yafemin duk kurakuren da aikata acikin wannan littafi, ka sa Sakona ya isa ga al'umma sannan kuma ya amfanar da su_*

*_Godiya ta mussaman gareki Antyna Real Shaxee ke din yar uwace a gareni ta mussaman, tare da illahirin yan kungiyar zamani writers Association ina Alfahari da Ku oll._*

Ban manta da Ku ba yan group dina Mussaman ku

_*RUKKAYYA FULANI,BABY LOVE,FIRDAUSI,RAHIMA ADAM,UKTY UMMI,WALIDA,MAMAN SHUKRA,MAMAN KHAIRAT,MOMYN IHSAN,HAWWA MUKTAR,HAUWA ABUBAKAR,UMMI JAMILAT,FATIMA ZAHRA, HAFSAT,MAMAN RUKKY, MARRIYA DAUDA,AISHA SHU'AIB, JIDDATY,SISTER,NAFY MUDANGI, PRINCESS OF LIGHT, MAMAN RUMASA"U, MAMAN USMAN,RAHABAπŸ₯°πŸ₯°I HEART U OLL MASOYAN ASALI SON SO SABIDA ALLAH*❀️❀️_

Dama wa'inda ban sami damar lissafawa ba inayinku duka.

_*Fatan zaku kara nunamin tsantsar soyayyar gareni ta hanyar siyan sabon novel di na JAMEEL (Nafseen) wan da na ke shirin fitarwa nan da sati daya karku bari a ba Ku labari, ta nan ne zan tabbatar da cewa ni tauraruwar kun CE da gaske ko ko dad in baki ne?_

*Domin sharhi, shawara ko gyara game da littafin Azzawajul-Mukaddar Ku tuntubeni ta wannan number ****

_*Urs Xayyeesherth*_😍