PAGE* 6
Adam ya shiga mota ya kasa waiwayo ya kalli Hamida ita ko sai dariya ta ke ta na, "Toh su Yaya Adam agaida yan matan makaranta banda wasa."
Alokacin motarsu ta tashi sannan su Abba su ka kai Hamida ma gida.
MISSALIN KARFE HUDU
Dai dai Adam ya isa Makarantarsu Dake Birnin Kebbi Tare da Abokinsa Mubarak wanda daman shi tun jiya ya dawo.
A kofar, Adam na shiga ya hadu da wata tsalleliyar budurwa wadda tunda ga saukarsa amota ta ke kallonsa ga duk alamu itama yanzu ta sauka.
Da sauri ta karaso garesa tare da fadin, "Am Nusaiba And You?"
Ya yi murmushi tare da fadin, "Ni fa banajin turancin nan ki yimin hausa."
Abun ya matukar ba ta dariya domin tasan ga dukkan alamu wasa ya ke mata ta ce, "Toh ai nima ban iya ba Amman dai sunana Nusai ba kai fa?"
Oh, "Ni kuma sunana Adam amman inkinso zaki iya kirana da Messi."
Nusaiba ta ce, "Ok sorry fa daga zuwanka na isheka da surutu, bari in barka kaje hostel nima na tafi anjima ma hadu." Da ganinta kasan irin yan matan nan masu yan gar tsiya.
Adam ya ce, "Ok."
Mubarak ya hango Adam daga nesa ai tuni ya tawo da sauri ya na, "Oyoyo abokina tun tuni kai na ke jira wallahi,kazo mu tafi dakin mu."
Adam ya ce, "Yess muje na yi wanka dan kasan ni ba irinka bane bazan iya doguwar tafiya banyi wanka ba."
Mubarak, "To uban yan tsurfa a school din ma ba'arage ba ,toh nidai muje."
Su ka shiga ciki sunata dariya . Bayan Adam ya yi wanka tare sallah suka ci abinci sannan fa ya fara zuba.
, "Abokina ina fada maka ina shigowa school dinnan na hadu da wata yar baby, gaskiya dole na dage dan kasan banson raini, dan haka kar mu fita kana wani kulasu fa su raina mu."
Mubarak ya ce, "Toh uban yan karya da gidan talakawa ka fito da wallahi bansan ya zaka yi ba kai kam komai kafison sa karya aciki, "hhhh ayi dai mu gani kasan ni dan kallo ne, yauwa na manta fa akwai taro da aka hadawa sababbin dalibai nasanin juna dan haka ka shirya muje."
Tuni Adam ya miki woooo abunnan fa yamin dadi za mu hadu da yarinyar nan kenan.
Adam ya ci kananan kaya da yake daman shi ba gwanin manyan kaya bane .
Sun shirya tsa, aiko su na fita da Mubarak sai ga nusaiba nan.
Adam da saurin sa ya ce, "Ah friend sannunki,kema gun zaki?"
"Eh wallahi." cewar Nusaiba.
suka jera tare su na tafiya abinsu gwanin sha'aawa Mubarak ko ya na kallon ikon Allah, domin haka su ke tafiya su na fira kamar can dama sun san juna.
Bayan sun isa wajen aka fara hidima kowa sai fitowa ya ke ya na baje kolin basirarsa daga karshe aka bukaci Nusaiba da ta fito domin ta fadi albarkacin bakinta. Sai ta fito kuwa ta na tafiya ta na rangwada kamar wacce za ta kare, tun anan aka rufe ta da tafi. Sauran matan da ke wurin sai kyashi su ke, amma kam ba yadda yan adawa za su yi domin duk gayun da ke wurin ta tafi da su. Akan step ta hau ta karbi Michael phone, kan ta ce wani abu aka kara rangada ma ta tafi. Sai ta dan gyara murya ta ce.....
*Oh Pls amsorry mu hadu a shafi na gaba.*
_It's Ur's Xayyeshert_β¦β¦βπΌ
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ _{ Ganganci }_
*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCATIONπ€π»* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _οΌRamadan Mubarak)_. *Writing by:*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.
*Facebook Aisha Mohammed Sani*.
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.
*LOvE MEssEGE*
_I feel very confident that we will make it through. Though we fight a lot I know that we will be together. -Vernon Straights i love you_