WASA DA SO

PAGE* 8

by @xayyeesherthulhumaerath

_*WANNAN PAGE DIN KACOKAN SADAUKARWANE GA YAN GROUP DIN POWA PATISKUM WRITERS ASSOCIATION INA YINKI IRIN OVERN NAN*_ ❤❤❤

ina son ku gane shi harshen turanci ba shi ne abin burgewa ba, domin idan har turawa ba su damu da yarenmu ba to mu miye amfanin damuwa da na su yaren. Ina son ku gane muna koyon turanci ne badaon komai ba sai don idan mun fita kasashen waje inda mu ke haduwa da wayan da ba sa jin namu yaren, kuma anan kasar tamu idan mun hadu da wani yare wanda baya jin namu yaren. Babban abin da yakamata mu gane shi ne ta ya ya za mu samu ci gaba a wannan kasar tamu. Babbar hanyar da zamu ci gaba shi ne hanyoyin da Nusaiba ta lissafo domin lallai karatunmu shi ne alfaharinmu kuma darajarmu yarenmu, hakika babu dakiki irin wanda ya raina kansa, idan kuma ka raina asalinka to tabbas ka raina kanka ne. Saboda haka yaren Hausa shi ne babban yare a gare mu 'ya'yan Hausawa."

Duk jama'ar da ke wurin su ka kara rangada ma sa tafi tare da fadin tabbas Adam abinda ka ke fada gaskiya ne kuma mun gansu sosai da sosai Allah ya kara basira. Haka dai aka yi taron wannan yazo ya fadi nashi wannan ya fadi nashi har aka watse.

Akan hanya Adam ta komawa hostel da ya ke wurin nesa ne sai ya hadu da Nusaiba a cikin motarta kirar Vibe itama za ta je hostel duk da ya ke ita gida ta ke komawa ba'a hostel ta ke kwana ba.

Nusaiba ta tsaya tare da ce wa, "Adam inba damuwa ku shigo na rage muku hanya ma na."

Adam ya ce, "No kibari kawai." azuciyarsa ko ce wa ya ke kawai na hau motarki araina ni dan ni banzo da ta wa ba.

Nusaiba ta ce, "please ina so muyi magana ne ,aboki tunda kai bansan sunan ka ba sa baki mana ku shigo na rage mu ku hanya."

Mubarak ya yi murmushi tare da fadin, "Bakomai Abokina mu shiga mana." Adam bai so shiga ba dan ba yadda ya iya da Mubarak ya sa ya shiga domin gani ya ke in an gansa A motar ta raina sa za ayi.

Nusaiba ta budewa Adam kwofa ya zauna a gun mai zaman banza shiko Mubarak ya shiga baya.

_It's Ur's xayyesherth_😘

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 _{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_. *Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_Lots of people want to ride with you in the limo, but what you want is someone who will take the bus with you when the limo breaks down. I’ll take the bus with you._