Page 10
*WANNAN SHAFIN NA KI NE KE KADAI FATIMA ZAHRA (eyman)MARUBUCIYAT AUREN ZAHRA INA TAYAKI MURNAR KAMMALA BUK DINKI ALLAH YAKARA BASIRA MUNA JIRAN SABOβ€β€β€β€πππ*
-------------------""""""""""""""'""" Ba abinda ya fara fitowa da ga bakin Adam sai, "HAMEEDA." ko wa ya yi shiru sosai dan ganin A bun mamaki.
Malamin ya kara da cewa, "ka ce me?"
Sai alokacin Hankalin Adam ya dawo a kidime ya ce, "we have two type of memory. We have ROM AND RAM. _ROM_ means read only memory and than _RAM_ means Read All memory. Sai kuma Hameeda ta ce min....." anan ya tsaya ya na tunanin me zai fad'a. Lecturer din ya daka ma sa tsawa tare da cewa, "Adamu wai wacece wata banzar Hameeda da ka ke son bata mana aiki akan ta an fada ma nan wurin wasa ne?" Abin ya zo ma Adamu biyu ga zagin Hameedarsa ga kuma kiransa da suna Adamu.
Adam bai san lokacin da ya fice a ajin ba, kawai kowa ya bisa da kallo.
Ya na fita ba inda ya nufa sai hostel, duk da ce wa Adamu jarumin namiji ne amman akan Hameeda ba ya iya jure hakan yasa banda zubar hawaye ba abinda ya ke, ya na kara tuna, "WAI BANZAR HAMEEDA? Anya ko shi yasan wacece Hameeda A gu na kuwa.?" Hmm.
Sambatu ya ke wanda shi kansa bai ya ce ga ya ga dalilen sa ba.
Nusaiba kuwa Hankalinta ya ta shi ganin ran Adam ya ba ci, hakan ya sa itama ta nemi excuse domin fita.
Ta na fita ta hadu da wasu 'yan mata a bakin kofar ajinsu ta tambaye su, "Dan Allah ba ku ga Adam ya wuce ta nan ba?" "Yanzun nan kuwa ya wuce ransa a bace ina ga dai ya wuce hostels." Su ka bata amsa. Tabi Adam hostel.
Da shi ke ta san dakinsu nan ta wu ce kawai aiko ta na shiga ta ga Adam cikin ya na yi ma ra dadi ,kwance ya na rawar sanyi in banda , "Hamee Hamee."ba abinda ke fitowa abakinsa.
Ta yi matukar firgicewa hakan ya sa ta yi saurin komawa motar ta dan komawa cikin makaranta domin dauko Mubarak ,ta na zuwa ku wa shi ma Mubarak ya rikice ,da sauri ya bi yo ta su na zuwa Mubarak ya rike Adam da kyar ya sa shi A mota domin su kai sa asibiti.
Su na zuwa aka karbesu ka san ce wa yanayin jikin na sa ya yi tsanani tuni likitoci su ka taru akansa ,sai da su ka dudduba shi sannan aka masa allurai ya sa mi barci.
Gaba daya Nusaiba ta rikice in banda kuka ba abinda ta ke kai ka ce sun yi shekara da haduwa.
Mubarak kuwa ya ka sa magana ga kuma wayar Adam Hameeda sai kira ta ke kaman ta san me ke faruwa,tun safe yau jikinta asanyaye ya ke hakan yasa ta nemansa ,gashi ta kira kusan sau biyar ba a dauka ba ,hankalinta ya kara tashi.
Mubarak dai ya yi daure tare da zama kusa Da Adam addu"o"i kawai ya ke ma sa.
Sai misalin karfe Hudu na yamma Adam ya fara farfadowa.
Ya farfado ya na, "..........
_It's Ur's Xayyeesherth_
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ _{ Ganganci }_
*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCATIONπ€π»* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _οΌRamadan Mubarak)_. *Writing by:*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.
*Facebook Aisha Mohammed Sani*.
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.
*LOvE MEssEGE*
_.I have a million things to talk to you about. All I want in this world is you. I want to see you and talk. I want the two of us to begin everything from the beginning luv yhu honey_