WASA DA SO

PAGE - 12

by @xayyeesherthulhumaerath

*AFWAN KWANA BIYU KUNJINI SHIRU,WLH BAN SAMU SUKININ YIN TYPING BANE AMMAN NASAN MASOYAN ASALI ZASU MIN UZURI,INSONKU DUKANKU😘😘*

Ta ya za ka san ina nan tunda hankalinka ya karkata gun masoyiyarka. "A haba Nusaiba to ki yi hakuri ai ita 'yar uwa ta ce, kin ga ko dole zan damu idan a ka zage ta. Idan a ka zage ta ji na ke kamar wanda ya zage ta dukan danginmu ne ba ya so wannan shiyasa idan a ka zage ta raina ya ke baci". Adam ya fada ya na dan sosa kansa. Mubarak kam ya na mamakin yadda Adam ya rikice na yan kwanakin nan duk ya sauya.

sai a lokacin Nusaiba ta dan ji sanyi a ranta sannan ta ce"to ai ya kamata ka tashi mu koma aji ko ? saboda ka ga akwai sauran lecture daya na Mallam Lawal".

Su ka shiga mota duk da ya ke ba wani nisa ne tsakanin hostel da ajijuwansu ba. Ko da su ka isa aji har Mallam Lawal ya fara lecture. idan har kasan Mallam Lawal kasan idan ya shiga aji ba a shiga. Nusaiba ta ce to ai kaddarar ta riga fata, wanda mu ke gudun ya riga mu ya shiga yanzu ya za mu yi kenan?"

Adam ya ce "ku yi hakuri dan Allah ni ne na ja muku wannan matsalar."

"Aa ka ga wannan ba damuwa ba ne dan haka kada wannan ya dame ka kaddara ce ta riga fata amma nasan yadda zan yi da shi dan haka kada ku damu idan ba damuwa mu je restuarent mu dan ci abinci mana." Mubarak ya ce to ai ba matsala mu je kawai tunda ba yadda mu ka iya". daga nan kuma su ka wuce wani restuarent wanda ke kusa da makarantarsu.

restuarent ne mai matukar tsadar abinci sai dai sun iya abinci sosai, kuma yawancin abincinsu na Hausawa ne su na zaune kan tebur wata yarinya mai rabawa mutane abinci ta zo ta na tambayarsu "ko me za akawo mu ku ?" Nusaiba ta ce "ni dai ki kawomin tuwon semonvita da miyan agushi, Adam me za a kawo mu ku ne bansan ra'ayinku ba". da ya ke Adam mutun ne da baya saurin bada gari sai ba ce komai ba MUbarak ne ya ce "kawai ki kawo mana abinda za ki kawo ma ta". yarinya ta juya ta wuce abinta. Adam ya ce "Mubarak ka ga yarinya mai natsuwa da hankali ko ba irin na mu wayanda ke da matukar jiji da kai ba, ba ruwanta sana'arta kawai ta ke ba ruwanta da kowa"

wannan maganar ba karamin batawa Nusaiba rai ta yi ba amma ba ta ce ko uffan ba har yarinyar ta zo ta kawo abincin su ka ci abinci su ka koshi su na ta labaran makaranta amma da ganin Nusaiba kasan ta sauya ba kamar baya ba. Da ya ke Adam ya na da saurin fahimtar yanayi dan haka ya fahimci yanayin da Nusaiba ta ke ciki amma duk da haka dai bai wani damu ba dan haka sai ya share. Su ka gama cin abincinsu su ka kama hanyar zuwa makaranta. A hanyarsu ta komawa makaranta su ka yi karo da wani karanin yaro wanda bai wuce shekara takwas ba zai ketara kan titi a yayin da za su wuce nan take wurin ya kidime da kalmar shahada......

Da sauri Adam ya karbi Nusaiba,sannan ya sa mu su ka kaucewa yaron nan.

Duk mutunen gun sun gama tsammanin an bige yaron sai gashi ko sun hangosa wani bawan Allah ya rikesa,banda Hamdala ba abinda su ke tare da godewa Adam Domin dan ba ya yi jarumta da dabara ba,ba abinda zai hana afkuwar mummunan hatsari Anan.

*************************** Hameeda ta fito daga makaranta kenan ta rasa abin hawa,da shike dreban su ba shi da lafiya yau kudin napep aka ba ta,ta fi minti Ashirin ba ta sa mu ba,har ta gaji ta fara tafiya sai ga wani dan sauri A mota ya tsaya tare da fadin, "Hameeda Hameeda."

Da sauri Hameeda ta juyo domin ta ji muryar da ta sa ni.

Ai ko Abokin Adam ne Muhsin! da mamakin ganinsa ta ce, "Yah Muhsin yaushe A gari?"

Muhsin ya yi murmushi tare da fadin shigo dai tukun na dan nasan gida za ki.

Ba tayi musu ba kuwa ta shige motar.

Muhsin ya ce, "Ya ki ke ya karatu?"

, "Lafiya lau wallahi." cewar Hameeda.

, "Abokina ya na skul abin sa."

Hameeda ta ce, "Eh wallahi ai ya kwana biyu da Tafiya."

Anan dai suka taba hira har yakai ta gida sannan su ka yi musayan nombar waya.

Muhsin Abokin Adam ne tun na yarinta su uku su ka ta so Adam,Mubarak,Muhsin, tare suka ta so barci ne ka dai ke raba su komai kuwa tare sukeyi,Sun gama secondryn su Muhsin ne ya fara samun makaranta a london dan haka ya fara gaba,su mubarak Da Adam kuwa sai yanzu su ka samu,tunda Muhsin ya sa ba da Hameeda sosai suna shiri.

_It's Ur's Xayyeesherth_

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 _{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_. *Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_Let me write my love for you in the sand, so the water can wash it away and I can write it again and again and again. I love you like crazy._