WASA DA SO

Page,-13

by @xayyeesherthulhumaerath

----------------------------------------------------------------

washe gari

Hameeda ta tashi kenan sai ga kiran Muhsin ya shigo,ta yi murmushi sannan ta amsa. "Amincin Allah ya tabbata ga ma ce ta gari."

Murmushi Hameeda ta yi sannan ta ce, "Tare da kai, Amman na ji mamakin kiranka awannan lokacin."

"Niko hakan bai bani mamaki ba kasancewar kanwata kuma abar kaunata na kira." Muhsin ya fada tare da lumshe ido.

Hameeda ta yi shiru domin ta fara gane inda ya dosa, ba wanda ta kawo ranta sai Yayanta Adam, da ya tsani wani ya ce ya na sonta,kuma shi ba sonta ya ke ba, ta dau hakan a matsayin har yanzu bai ga wanda ya da ce ba ne,watakil tunda wannan abokinsa ne ba matsala zai iya yarda da shi.

Muhsin ya ji shirun ya yi yawa hakan ya sa shi fadin, "Ya ya dai Hameeda na ji kin yi shiru?, inba matsala yau ina so na zo gida anjima."

Sai alokacin ta barga da tunanin Adam sannan ta ce, "Toh bakomai Allah ya kawomin Abokin Yayana lafiya."

, "Umm wa to dai har yanzu a abokin yayanki na ke ban zama yayan ba." Muhsin ne ya fada tare da murmushi.

Hameeda ba ta ce komai ba,sai ita ma murmushin ta yi.

"OK Byee sai na zo me kikeso na ta zo miki dashi?" cewar Muhsin.

Hameeda ta ce, "Duk abinda ka ga ya maka to nima yamin."

Anan sukai sallama.

Ta na gama wayar kuwa sai ga kiran Adam ya shigo, "Hello Habibbty Hamyy."Adam ya fada da dariyarsa.

Hameeda ta ce, "Hy sweety yah Adamu."

Adam na kwance amman sai da yatashi , "Wato ke har yanzu baki bar rainani ba ko,lallai ma kinaso sabuwar beb di'ta ta hukunta."

Hameeda taji wani iri aranta da ya ce sabuwar beb amman ta daure tare nuna rashin damuwa ta ce, "Kana ina nima nayi sabon dan beauty wanda ya fi ka kyau."

Ba karamim wani zafi Adam ya ji aransa ba amman shima ya basar kamar yadda ita ma Hameedan tai ya ce, "Yoo indai a irin tsofin da kike tarawa ne ai zasu gudu sai mai?"

Tsokanar junansu su ke amman gaba daya zuciyoyinsu ba so su ke ba.

_It's Ur's Xayyeesherth ***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 _{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🀝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_. *Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE*

_You have no idea how much I like you, how much you make me smile, how much I love talking to you or how much I wish you were here.._