PAGE -14
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Hameeda ce ta gaji da surutun Yayan nata ta ce, "Toh Yaya Messi Abarni na yi aiki please kar mami ta zo."
"Bazan kashe ba din toh yanzu ma aka fara wayar." cewar Adam.
Hameeda tai murmushi tare da fadin, "Toh Yaya Adamuna."
Da sauri Adam ya ce, "Dalla chan yar rainin hankali sai anjima."
Kan tai magana ma ya katse wayarsa, ita ko dariya ta ke dan ta yi maganin Yayan nata inba haka ba sai su kusan wuni Ana wayar nan.
Ya na katse wayar Hameeda ta shige cikin gida tare da fara gyare-gyaren gida.
Bayan ta kammala ta sanar da mami cewa Yaya Muhsin na zuwa yau da ya ke daman sun Saba zuwa da Adam shi ya sa hakan bai ba wa Mami mamaki ba, sannan ta fara girki.
Aiko an yi masa abinci kala kala sannan ta shige ta yi wanka ta fito kenan sai ga kiransa ya shigo ta na dagawa ya sanar da ita cewa gashi nan ya kusa iso.
Make up ta fara ba jimawa ta gama domin ba ta cika yiwa fuskarta kwalliya ba, domin kullum ta yi kwalliya mai yawa sai sun yi fada da Adam wai ta yi kwalliyar aljanu, hakan ya sa ta saba tun ba ta saba bama yanzu ya zame ma ta jiki kuma ita kanta tasan tafi kyau in tai simple make up.
Muhsin na isowa ya kira Hameeda,aiko alokacin ta fito.
Ya na ganinta banda murmushi ba abinda ya ke ita ko Hameeda sunkuyar da kai tai dan ganin irin kallon da ya ke ma ta,ta ma sa iso zuwa falo sannan ta shiga ciki ta dibo kayan abinci tare da mai aikinsu hanse wadda ta rikwo drinks.
za ma Hameeda tai su ka fara gesawa da Muhsin sannan su ka fara hira jifa-jifa kasancewar Hameeda A kwai kunya,hakan bai damu Muhsin ba domin yasan ha ka ta ke inba yayanta na waje ba,ba ta iya sakewa.
Muhsin ya ce, " Inaga in ban kira Messi ba ya mi ki magana ba za ki sa ke muyi magana ba."
Sai da gaban Hameeda ya fadi amman ba ta nuna ba murmushi kawai ta yi.
Muhsin ku wa ya ciro wayarsa sannan ya kira numbar Messi,ringin biyu ya daga kasancewar ta na hannunsa.
Sallama Muhsin ya yi Adam ya amsa tare da fadin , "mutanen kasar waje karka ce min ka dawo sokoto."
Muhsin ya yi murmushi tare da gyara zama ya ce, "Karshen magana ma ina tare da kanwata Hameeda."
Adam na kwance sai da ya tashi ya na fadin, "What?"
Urs Pretty Xayeesherth ***
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 _{ Ganganci }_
*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_. *Writing by:*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.
*Facebook Aisha Mohammed Sani*.
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.
*LOvE MEssEGE*
_You have no idea how much I like you, how much you make me smile, how much I love talking to you or how much I wish you were here.._