PAGE -15
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*A BUN NA KU DA BAN MAMAKI🤔KU NA SO AMMAN KUNA KYASHIN MIN SHARHI,DAN HA KA NI MA NA FARA KYASHIN TYPING,IN KUN GYARA NI MA NA GYARA👌*
Muhsin ya mikawa Hameeda wayar ta karba tare da fadin, "Yaya Messina."
Abun ya matukar tabawa Adam zuciya hakan ya sa shi katse wayar ba tare da ya ce komai ba.
Hameeda ta kalli wayar tare da fadin, "Yaya Muhsin wayar fa ta katse."
Muhsin ya ce , "Ok ina ga network ne."
Nan Muhsin ya fara baje kolin sakon da zuciyarsa ta dauko zuwa ga zuciyar Hameeda, ya nu na ma ta ce wa shi dai aurenta ya keso ba da wasa ba.
Hameeda ta matukar ji dadin kalaman Muhsin duk da ce wa kunya ta hanata nu na hakan, Amman alamu sun nu na ce wa ta a mince .
A haka suka yi sallama tare da shawarar ce wa iyayen shi za su zo nan ba da jimawa domin bai so auren ya dau lokaci so sai.
************************ ********************
A bangaren Adam Ku wa wa ni kishin Hameeda ne ya turnikye ma sa zuciya, ya ra sa me ke damunsa zazzabi ne ciwon kai ne ohon ma sa.
Kawai ta shi ya yi ya nufi cikin makaranta Inda ya tarar da Nusaiba ta na ta nemansa zasuyi karatu.
A lokacin da ya hadu da Nusy ya ma manta da abinda ke damunsa tuni su ka fara karatu cikin nishadi, kullum Nusaiba ba ta da wa ni burin da ya wuce a ce ta farantawa Adam domin Ita ko ba komai ya na birgeta ku ma ta na son kasancewa da shi.
A yau yadda Adam ya sakewa Nusaiba Abin ya ba ta mamaki kasancewar kullum Jan ba ya ya ke da Ita Amman yau kam ya sa ke Ma ta, Ku ma ta ji dadin hakan.
Ko da Mubarak ya zo ya gansu abin ya yi matukar bashi mamaki amman kawai ya share dan yasan halin abokin nasa, in ya so abu ya so Kennan .
Yau Adam shi ne harda Zuwa shan ice cream ya na ba wa Nusy abaki banda dariyar su ba abinda ke tashi a gun da ka gansu kasan su na cikin farin ciki.
A na cikin ha ka sai ga wayar Adam ta fara ringing dagwan da zaiyi ya ga number Hameeda.
Xayyeesher ce😘
***
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 _{ Ganganci }_
*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_. *Writing by:*
*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.
*Facebook Aisha Mohammed Sani*.
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.
*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.
*LOvE MEssEGE*
_I love the way you laugh, I love the way you smile. I love the way you make me feel every single time. You are the one who takes away the blues. That is the reason why I am so in love with YOU!_