WASA DA SO

PAGE -17

by @xayyeesherthulhumaerath

*WANNAN SHAFIN NA KA NE MUBARAK A KAMBA INA JIN DADIN EDITING DINKA ALLAH YA SAKA DA ALKAIRY SAURAYIN ABULLE🤣*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_ba yawan page bane abun birgewa abinda ya kunsa xaku du ba👌_

Kiran ya shiga Amman ba a dauka ba, bai gaji ba ya kara kira Amman ba amsa, hakan ya sa shi tunanin ce wa watakil aiki ta ke.

Bayan sunje asibiti a ka ma ta allurai sannan ta sa mu barci, ta kai kusan Awa hudu kan ta farka, farkawarta ke da wuya sai ga kiran Adam ya shigo, Momy ce ta mika ma ta wayar tare da fadin, "Yayanki ne Dan ya kira dazu na fada ma sa ba ki da lafiya."

Da sauri Hameeda ta karbi wayar tare da yin sallama da rarraunar murya.

Sai da Adam ya ji wani yar domin tunda ya kira ya ji ba ta lafiya, ya aiyana ce wa shine silan hakan duk da ce wa bai san dalilin da ya sa zuciyarsa ta ke fada ma sa ce wa shine silar ba.

A hankali ya kira sunnan ta kaman ya na gabanta , "Hamee nah."

Hameeda ta ji jikinta ya yi sanyi hakan ya sa ta ka sa amsawa.

Adam ne ya kara da ce wa, "Ki min magana dan Allah, kinji Hamee nah, na durkusa tare riko hannun kanwatah, ki fada min me ke damunki."

Hameeda ta yi rau da fuska kaman za ta yi kuka ta ce, "Ba kai ne......

Ta ka sa karasawa sai kuka, ita ko Momy ta na gefe ta kurawa Hameeda ido ta na ganin ikon Allah.

Adam ya ce, " Ki fada min Dan Allah, me na mi ki?, na daina daga yau, ki dai na kuka please ba ki San me na ke ji a zuciyata ba ne."

Hameeda ta tsagetar d kukan ta sannan ta ce, "Ba kai ne ka ke ta kul.....sai ta yi shiru .

Ta kara da ce wa, " Tsokanata fa ka ke wai samarina dukka tsofaffine."

Adam ya so ya gane ce wa ba haka ta so fada ba, Amman ya basar kawai tare da yin murmushi mai Dan sauti, " Oh Hamee na am sorry please na daina da ga yau,na yi alkawari insha Allah. "

Hameeda ta ce, "Umm To Byee bye anjima ma yi waya yanzu zan ci abinci na sha magani."

Adam ya ce, "Ok Bye miss you, take care Hamee nah."

Urs Xayyeesherth

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 _{ Ganganci }_

*TRUE LIFE LOVE STORY*. _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCATION🤝🏻* __________________________ *we are here to educate,motivate, and entertain our readers.* __________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_. *Writing by:*

*Aysherth Mohammed Sani* _(Preety Xayyeesherth)_.

*Facebook Aisha Mohammed Sani*.

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*. _Duk kan godiya ta tabbata ga ubangiji madaukaki sarki. Gaskiya ina matukar farin ciki da fara sabon novel dina fatana Allah yasa ya ilmantar da al'uma tare da nishdantarwa, ina rokon Allah ya yafemin kurakuren da zan yi wayanda bansani ba. Alkhairan da ke ciki kuma ya isa ga al'umma su amfana tare da alfahari damu_.

*KAMAR YADDA KUKA GANI TUN FARKO WANNAN LABARIN BA KIRKIRARRE BA NE YAFARU DA GASKE NE SAI YAN WASU ABUBUWAN DA AKA GYARA DOMIN TAFIYARDA SHI A TSARI*.

*LOvE MEssEGE* _Life is not a waste as long as there is at least one person in the world who cares for you. So when things go wrong and you feel like giving up – remember you’ve got ME!_