PAGE - 18
*Wannan shafin sadaukarwa ne ga baba layuza kabir INA tayaki murnar kammala buk din ki FACALA Allah yakara basira,Allah yasa ya Isar da sakon da yadauko* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Washe gari
Adam da Hameeda tare da Mubarak sun shiga cikin skul,ba jimawa aka fara mu su karatu,yau gabadaya Kowa ya ga Adam yasan ba ya walwala,Mubarak ya yi ya fada ma sa me ke damunsa Amman ya ki,har sai da Nusaiba ya ta sa baki Amman ya ki ba su amsa,lectures ake mu su Amman shi hankalinsa kwata-kwata ba ya wajen,har sai Malamin ya fahimta da farko ya kyale sa amman ya ga abun ba na yi ba ne,ya ce, "Kai Adam."
A razane Adam ya juyo tare da fadin, "Hamee na."
Murmushi malamin ya yi kawai kasancewa ya San Adam a kan Hamee dinnan.
Da ko ya dawo hayyacinsa ya kasa sukuni banda Sosa kyaya ba abinda ya ke.
Shi ko Mallam Muhammad ya kara murmushi tare da fadin, "Adam yau inason ganin ka,inna fita ka biyoni."
Kai a ka sa Adam ya ce, "Toh Mallam."
°°°°°°••••°°°°°••••°°°°•••••°°°°°••••°°°°••••°°°°•••°°°••••°°°••°°°•••°°°°••••
Yau Abban Muhsin zai je gidan su Adam,bai ba ta lokaci ba da huri da shirya domin ya na so ya je ya sami dadyn Hameeda agida kan ya fita.
Suna isa gidan kuwa dai dai da fitowar Dadyn Hameeda zai tafi office.
, "Ah Alhaji kai ne yau agidan na mu?" Cewar Dadyn Hameeda.
Abban Muhsin ya yi murmushi tare da fadin, "Wallahi kuwa Alhaji,ga shi Ku ma na zo a letti kar dai na katse ma saurin ka."
Dady ya ce, "Aa wallahi Alhaji mu shi ga ciki ai ba komai."
Shi ga cikin gida su ka yi.
Bayan sun gesa ne Abban Muhsin ya fara sanar ma Dadyn Hameeda abinda ke ta fe da shi.
Murmushi Dady yayi sannan ya fara jawabi kamar haka, "To Alhaji A gaskiya dai na ji da di da wannan magana ta Ka, Amman kash hanzari ba gudu ba,da matsala ka ga dai na farko Muhsin bai gama karatu ba,kuma bai da aikin da ya ke ayanzu,ka ga kuma Hameeda ya' ce daya tillo a guna,ba zan so na bawa Wanda bai da aikin yi ba ko innce ya ke karkashin mahaifinsa,uwa uba ku ma INA so Hameeda tai karatu,ka ga wannan shekarar za ta yi SSCEn ta."
Ya numfasa sannan ya kara da ce wa, "Amman fa duk hakan ba wai ya na nufin bazan ba sa ita ba ne A'a , Indai ya ga zai Iya to INA so ya je ya nemi Sana'a ta kansa sannan ya karasa karatunsa,ka ga kan lokacin ta yi nisa a karatu,Inda rabonsa To Hameeda ta sa ce."
Tun Abban Muhsin na jin dadin maganar Dady har abun ya fara bata ma sa rai.
Ga ba daya jikinsa ya yi sanyi domin alamu dai sun nuna ba son ba wa Dan sa yar sa ya ke ba.
Murmushi dole Abba ya yi tare da fadin, "Bakomai Alhaji,Allah ya sa hakan ne ma fi alkairy,nagode da ba ni lokacin ka da ka yi."
"Bakomai ai ana tare."
Cewar Dady Kenan.
Anan su ka yi sallama.
%%%%%%%%%%%%% %%%%%%%%
Adam su na fita daga aji ya nufi office din malaminsu kamar yadda ya bukata.
Adam na zuwa Mallam ya bashi wajen zama tare ba sa ruwa mai sanyi " ka sha ko zuciyarka zata yi sanyi domin muji dadin maganar da zamuyi."
Cewar Mallam Muhammad kenan.
Adam ya yi murmushi sannan ya kurbi ruwan.
Mallam Muhammad ya ce, "Adam wacece Hameeda?,mi ye ya hada ka da ita?"
Adam ya ce, ".......
*Bani da lfy kwana biyu amin afwa🙏🙏*
Urs xayyeesherth ***
🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOvE MEssEGE*
Ü R My Dream In Mÿ Slêêp; Ü R The Vision Of My Eye; Ü R The Smile Of My Lips; Ü R The Beat Of My Heart; Ü R An Angel In My Prayers; Ü R The Light Of My Life. My Lõve! My Life!