PAGE* 19
____________________________________________________________________________
*A min afwa na ji shiru da ku ka yi kwana biyu,hakan ya faru ne sanadiyar ciwon yayata wanda har ya kai mu ga kwanciya a asibiti,amman yanzu kam Alhmdlh ta fara samun sauki,insha Allah zan cigaba da typing ko da ba kullum ba ne,Inayinku masoyana irin over dinnan*.πππ
Adam na sosa kansa da alama dai ya na jin kunyar fada ma sa wacece Hameeda.
"To shi kenan tunda ba zaka fadamin ba, tashi ka je." Mallam ya fada tare da nuna hanya da dan yatsarsa. "Aa mallam ba wai....." "kaga Adam ba wani ja-in-ja zamu yi da kai ba, kawai ka je."
Adam ya sunkuyar da kansa kasa alamar dai ya na matukar kunyar Mallam. Har ya kai bakin kofar fita Mallam ya ce ma sa zo dawo..."
Adam ya dawo tare da sauke wani numfashi mai nauyi. Mallam ya ce "Adam ka da ka damu irin halin da ka ke ciki ya as na ke matukar tausayinka na kira ka ne dan naji ko akwai hanyar da zan tallafama da ita. Amma idan har hakan ya zama takura a rayuwarka to kada ka damu ka je abinka kuma kada ka dauka na yi fushi da kai ne.
Wani sabon numfashin Adam ya sake saukewa sannan ya ce "Mallam karatun nan na ke so na daina me zan yi a sallameni ba tare da bata sunana ba.
" kai subhanallahi! Wai me ke faruwa da kai haka Adam." daga nan Adam ya kwashe labarin Hameeda duka ya fadawa Mallam. Wayyo Allah rayuwa kamar Mallam ya fashe da kuka saboda tausayinsa da ya ke. "ka ga Adam kada ka yi fatar fita daga wannan makarantar ba tare da kammalawa ba, a koda yaushe ana son namiji mai juriya shin yanzu idan ka koma gida ba tare shedan kammalawa ba me zaka ce da ita abar kaunar ta ka wacce itama burinta ne ka yi karatu sosai?
Adam ya fara dogon nazari a kan abinda Mallam ya fada.
"ka ga Adam ka yi dauriya ka cikawa abar kaunarka burinta ka da ka manta ta ce ta na son kafi kowa karatu dan haka lallai ka yi kokari ka zama jarumi dan ganin ka cika ma ta burinta.
Kamar ana bugawa sarkin manoma ganga Adam ya ke ji da irin kalaman da Mallam ke fada sai kuma ya ce "Mallam nagode sosai a gaskiya tunda na fara karatu ba a taba karantardani irin na yau ba dan haka na yi alkawarin zan cikawa Hameeda burinta insha Allahu zan yi kokarin ganin ban fadi ko wace jarabawa ba duk wuya duk rintsi insha Allahu zan yi kokarin ganin na zamo First Class."
Mallam ya yi murmushi sannan ya ce "yauwa yarona Idan ka yi hakan tabbas ka nuna ma ta kai jarumi ne.
Kuma zan taimakama wurin ganin ka cika wannan burin naka.
Wannan ma ba karamin farantawa Adam rai ya yi ba. Su ka yi sallama sannan ya fita da ga office din.
Adam na fita ba inda ya nufa sai wajen Mubarak.
"Haba Abokina tun tuni Ina ta jiranka ka ki fitowa kamar wani mai daukan lectures,har nusy ta gaji ta tafi hostel." Fadin Mubarak Kennan Abokin Adam.
Adam bai kulasa ba sai da ya zauna sannan ya dafa kafadar Mubarak ya ce, "Hmm Ai wannan ya fi lectures,domin Mallam ya min karatun da ba'a taba min irin sa."
Tuni Mubarak ya washe baki ya na, "To ba ni kawai Mana Nima na sha."
Adam ya ce, "kai dilla sirri ne abun."
Mubarak ya yi murmushi domin yasan zance bai wuce na Hamee ba.
"Kai tashi muje ni fa yunwa na ke ji gashi ina so na je library kuma in dawo na kara Hamee domin akwai labari."
Adam ya fada tare da tashi.
Mubarak kuwa bin sa ya yi ya na dariya tare da fadin, "Da alama dai Mallam ya saita min kai."
Su na cikin tafiya kenan sai ga Nusaiba ta na tawowa garesu,tuni Adam ya bata rai..........
Urs xayyeesherth
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ ππΉππΉππΉππΉ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOvE MEssEGE*
_l feel something in my heart, its like a little flame, every time l see you, this flame lighat up, this flame is special for you, because I LOVE YOU!_