WASA DA SO

PAGE*-20

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA GAREKU YAN KUNGIYAR ZAMANI WRITERS ASSOCIATION,KUNGIYA DAYA TAMKAR DA DUBA INA ALFAHARI DA KU,KUYI YADDA KUKESO DA PAGE DINNAN SON RANKU AMMAN BANDA BABA LAYUZA KABIRπŸ˜›KIN TSUFA SAI DAI HANGE DA GA NESA INAYIN KU IRIN TOTALLYN NAN OLL😘😘😘*

Ita ko murmushi tayi tare da karasawa gare su tana fadin, "Wai yau waya tabomin Yayanmu ni da Hamee ne?"

Kalmar Hamee da ta fito daga bakin Nusaiba ya sa Adam yin wani murmushi mai da dauke da fasarra daban-daban.

Nusaiba tasan cewa in kana son ganin farincikin Adam kawai ka ambaci Hameeda mussaman ma ka kira ta da Hamee wato sunan da ya ke kiranta dashi.

Adam yace, "Yarinya ni ba Wanda ya batamin rai,kin San mu irin mu manya sai munayi muna basarwa sabida gudun rai ni."

Dariya kawai Mubarak Da Nusy su ke.

Adam ya ce, "Umm gwanda Ku ni yunwa fa na ke ji muje mu sai Abinci Dan bazan iya zama haka ba."

Nusaiba ta ce, "Ai ko Wallahi ni ma Yunwar nan na ke ji muje."

Tafiya suke suna hira har su ka isa wajen cin Abinci.

Daya daga cikin ma su sai da Abincin CE ta tawo garesu domin tambayar me za'a kawo mu su.

Adam ya wani murtukye fuska ya ce, "Ni Tuwon gari miyar kuka na ke so."

Mai aikin ta ce , "What! Ai ba ma sai da tuwo anan."

Mai su Mubarak zasu yi banda dariya.

Adam ya kara murtukewa kaman bai San dashi suke ba , "To wani abinci ne ya fi kowanni abincin tsada a gun nan?"

Ta ce, "sai dai soyayyar shinkafa,da salat tare da naman kaza."

Rai A murtuke ya ce, "To A kawo min ko ma da miye."

Ta jure ga su Mubarak da suketa dariya ta ce, "Sir, Ku fa?"

Nusaiba na dariya ta ce, "Irin na yayanmu mukeso."

Adam ya kalleta ya yi wata dariyar mugunta tare da cewa , "Eh je ki kawo mu su duk zan biya."

Ita ko ta tafi ta kawo musu abinci harda drinks .

Bayan sunci sun kwoshi an kawo list Adam ya tashi yana bata rai, Wai adole zai biya,kuma bayan yasan bai da ko sisi a aljihunsa.

Nusaiba ta ce, "Aa Yaya zan biya fa." Ta sa hannu ajaka domin ciro kudin.

Adam ya ma ta alamar dakatawa da hannu.

Nusaiba za ta kara magana, Mubarak ya ce, "Aa barsa za mu ga da wani kudin zai biya ai."

Adam ya na ta lalube dai ba kudi kuma yasan babun kawai burga CE adole bayason raini,ya na zakuwa akan Nusaiba ta kara magana Amman ta ki sun ma ja gefe banda dariya ba abinda suke ya na juyowa sai su murtuke.

Ya ga dai abun ba yi gsshi har mai aikin ta fara masa magana ya ce, "Ku kubani Aron kudi a gun Ku Ashe na manta da wallet di ta."

Mubarak zai yi dariya Adam ya masa wani mummunan kallo tuni ya mayar.

Nusaiba ko da sauri ta biya kudin sannan suka tafi yana, "in munje hostel fs ki tuna min in baki kudin ki."

Nusaiba ta ce, "To." Domin tasan tana cewa wani Abu zai iya ja musu fada.

____________________________________________

Abban Muhsin ya isa gida jiki ba kwari domin alamu sun nuna dai ba bawa d'ansa Hameeda za ai ba.

Shigar sa kedawa wuya Umman muhsin ta ce, "Anya kuwa ya na gan ka haka?"

Abba ya ce, "Hmm kawai dai kiramin Muhsin sai kije duk yadda akai."

Kan umma taje kiransa har ya jiyo dawowar Abba Dan haka ya tawo da saurin sa ganin yanayin da ya ga mahaifinsa ne yasa ya gane cewa da matsala zauna yayi kasa jiki asanyaye.

Abba ya musu bayanin duk abinda sukai da Dadyn Hameeda.

Gaba daya Muhsin ya rikice ya rasa me ke masa dadi aransa,Dan haka ya kudiri niyar tsayawa da karatu sai ya nemi kudin auren Hameeda ko da ma zai cigaba da karatun.

Shi dai Abba ya na nuna masa cewa kawai ya yi hakuri ya nemi wata.

Muhsin araunane ya ce, "Abba kamin Afwa wallahi INA son Hameeda banajin zan IYA rabuwa da ita, na yanke shawarar tsayawa da karatu in nemi kudi ko da,da karfin jiki na ne Dan naga na mallaki Hameeda amatsayin in Mata."

Abba ya yi dogon numfashi sannan ya ce, "ba zan hanaka hakan ba Amman INA so ka sani indai Neman Auren Hameeda ne na cire hannuna aciki,ko da ka nemi kudi kamar yadda mahaifinta ya bukata to nidai bazan kara komawa garesa da niyar Neman Aure ba,Ni maihaifin ka ne Amman bazan iya ba illa kawai zan kasance mai ma fatan alkairy a kullum."

Muhsin ya ce, "Nagode Abba,Allah yasaka da alkairy kuma insha Allah bazan taba baka kunya ba Addu'ar ka kadai na ke bukata akullum kamar yadda ka saba,na gode."

Ya na gama fada ya tashi fita.

Umma kamar za tai kuka domin tausayin d'an na ta,ta ke.

________________________________________________

A bangaren gidan su Hameeda kuwa Dady Na shiga gida ya kira Momy da Hameeda ya sanar da su komai.

Ita dai Hameeda ko ajikinta hakan bai bata ma ta rai ba, kuma bai sa ta farinciki ba.

Ta shiga d'aki Kennan sai ga kiran Muhsin da kamar bazata daga ba sai kuma wata zuciyar ta ce daga mana Hameeda.

Dagawar da zatayi taji muryar Muhsin ya na kuka Hameeda na da matukar tausayi hakan yasa ita ma kawai ta fara..........

Urs XAYYEESHERTH

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOvE MEssEGE* Ì £ØVè Yâù.. Your Love Is My Inspiration And Happiness. With Your Purest Love And Sincerity, I Was Out Of Emptiness. The Strength And Power You Gave Me Makes My Life Endless. From Today, Tomorrow And Forever. .My Dear.. I Love You Always.