WASA DA SO

PAGE*-21

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

*WANNAN SHAFIN NAKINE MY DOTA HAUWA SULAIMAN KIYI YADDA KIKESO DASHI MUCH LOVE DEAR MIE😘😘*

Kuka , Muhsin da ya ga hakan ba zai kai mu su ba yayi saurin tsagetawa da kukan sa tare da fadin, "Sorry Sweetheart ki daina kukan nan bazan juri ganin ki kina zub da hawayenki ba domin tsada garesa."

Da kyar Hameeda ta lallaba ta tsaida kukanta cikin shagwaba ta ce, "To To ba kai ne ka fara kukan ba."

Muhsin ya ce, "Sorry Daliline yasa hakan, fatan Dady ya sanar mi ki yadda sukai Da Abbanmu."

Hameeda tai shiru sannan ta ce, "Eh." Jiki a sanyaye.

Muhsin ya ce, "Karki Damu wannan ba matsala ba ce domin na kudiri niyar neman kudi domin Aurenki."

"To maganar karatun ka fa."cewar Hameeda.

Muhsin ya ce, " Aa wannan ba matsala ba ne zan ajiye sai naga na mallaki ki amatsayin uwar 'ya'ya na."

Hameeda ta numfasa tare da fadin , " To Allah ya ba da sa'a."

Muhsin ya ce , "yauwa sweety mie byee byee,oh na manta ma baki fadamin ba."

Hameeda tai murmushi tare da fadin, "I love yhu byeee."

Muhsin ya katse wayar yana murmushi ji ya ke kamar ma bai da wata sauran damuwa aransa.

_________________________________________________

Su Mubarak sun isa dai-dai hostel din su Nusaiba,Ta kalli Mubarak tare da fadin, "Toh yaya Mubarak ka kar ban min kudin in kun je hostel,sannan ka rikye na baram."Nusaiba ta fadi hakan ta na murmushi.

Adam ya kalle ta sannan ya ce, " Ba ya so din kudin ki za ki karba."

" Tab yadda nayi broke dinnan ka ke son min bakin ciki,Nusy kyalesa Sai na karbi Abuna."cewar Mubarak

Nusaiba kawai dariya ta ke domin yau ta San Adam kiris ya ke jira tuni ta shige Hostel.

Adam ko kula Mubarak bai ba kawai tafiya su ke ba magana har su ka isa dakin su, Su na shi ga da Adam ya fara wata muguwar dariya harda kai wa kasa yana, "Hhhh Wallahi fa kasan banda ko ficika,kawai banson yarinyar ta raina ni ne,INA ta Addu'ar kar Allah ya sa ta CE in bata kudin ta,Dan da naji kunya wallahi."

Mubarak ma kawai dariya ya ke yana, "Ai kawai kallonka na ke wallahi nasan ba ka da ko biyar,Amman ka na ta wani batsewa kaman mai jin kashi,HHHH hhhhhh wallahi nima na so ta ce ka bata kudin ta muga yadda zakayi,ba kai dan karya ba,kuma wai ba ka son raini."

Adam ya ce, "Eh din to mugu ba ta fada ba kuma wallahi ko na Ciro kudi ba zan ba ka ko siSi ba,ai kasan ba wai kwata-kwata ba kudin ba ne mu na hanya Dady ya turomin."

Mubarak ya ce, "Kut Ai Wallahi sai ka ba ni ko in fadawa Hamee ta samu abin tsokana."

Adam ya ce, "Ka CE dai kawai ka na so sai kowa a family ya ji kasan Hameeda kiris ta ke jira."

"Ohooo dai ni dai Abani kudi na kawai." Mubarak ya fada yana dariyar mugunta.

Adam ya ce, "kai dalla chan Dan dai 10k zan ba ka basai ka kaini BBC Ba."

Mubarak ya ce, "Da dai ya fi."

Adam ya Ciro wayar sa Kennan sai ga kiran Hameeda.

"Hello Yaya Adamu na."

"Kut kawai ma ki ce Adamun ma na ai ba Amfanin sa Yayan tunda kin Riga kin rainani."

Hameeda ta yi dariya sannan ta ce, "Sorry yayan Hamee,wai yaushe za Ku fara exams din ne,ni fa na zaku ka dawo ka ga munkusa fara WAEC din mu kuma banda mai min lesson,bana gane na kowa in ba na ka ba." Ta na maganar cikin shagwaba.

Gaba daya Hameeda ta gama kashewa Adam jiki da sanyayyar muryarta,Arauna ne ya ce, "Insha Allah nan da 2weeks zan dawo gida Hamee nah,Amman me ki ka tanadarmin."

Hameeda ta ce, "Smile sai ka zo kawai, za ka sha mamaki."

Hirarsu suke cikin nishadi,Wanda duk Wanda ya gansu zai ce Masoyane , A masoyan ma wa'inda sukai zurfi cikin so.

Amman su kam ba su fahimci hakan ba su dauki kulawar da sukewa juna kawai shakuwa CE ta yan uwan juna.

In kaga Adam ya wage baki yanata dariya da tsayawa to suna tare da hameeda ko su na waya,In ba haka ba kana ganinsa kasan miskiline.

Haka kuwa ita ma Hameeda surutun ta agunsa ya tsaya ko ince akanta domin in dai ka ga ta zakye tana zubar ba da labari to A kan yayanta Adam ne.

Duk da cewa iyayensu sun fahimci cewa akwai soyayya tsakanin su amma hakan bai sa sun fada musu ko su nuna cewa sun fahimci hakan ba,kawai sun zuba musu idone suna ganin ikon Allah.

Adam na gama waya da hameeda Mubarak ya ce, "Nikam dai yau ba zanyi shiru ba,Adam wai mai yasa ka ke *WASA DA SO* ne?,ka son Hameeda Amman ka kasa fahimtar hakan.

Adam ya ce, ............

Urs xayyesherth ***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOVE MESSAGE*

whenever U feel Blue, i will be there for U, Whenever u are sad' i will stay by ur side, whenever U need sumone to love, i will always be there for u......