WASA DA SO

PAGE*-22

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

"Ba ka yi karya ba Ina son hameeda kuma ina son mace mai irin haleyar ta da ma ya na yin ta gaba daya,Amman abinda ba Ku gane ba shine son da nake ma ta ba irin Wanda Ku ke tunani ba ne,Hameeda jinjikinace dole na so ta kuma nai kishinta Amman ba wai so na soyayyar Aure ba,bana tsammanin zan iya rayuwar da Hamee nah." Ya karasa fadan hakan ya na murmushi tare da kallon hoton Hameeda da ke screem din wayar sa.

Mubarak ya ce, "Hmm Adam kennan ina ganin ni na San ka fiye yadda kasan kan ka,Amman A kullum Ina ma fatan alkairy, domin farincikin Aminina shine na wa."

"Godiya na ke Abokina naji dadin jin hakan daga bakin ka."

Washe gari

Hameeda na zaune ta na chating A wayarta sai ga text din Muhsin ya shigo ma ta kamar haka: _"Assalamu alkaimu ya ke masoyiya ta,hasken raina,fatan kin tashi lafiya?Allah yasa haka Ameen,ina so in sanar da ke cewa yau zanbar cikin garin nan zan koma kauyen kano *gaya* asarin garin mahaifina,Ku ma bazan dawo ba sai har na mallaki Abinda zan aureki dama Wanda zan ciyar da ke da ikon Allah,Amman ina so kimin alkawari daya,bazaki taba bawa wani damar shiga zuciyarki ba,ki killacemin kanki kamar yadda kika saba,daga yau bazan kara kiran ki ba kuma bazan kara miki text ba har sai na dawo gareki,karki manta ina son ki ,kuma zan cigaba da sonki har bayan raina,na baki Amanar zuciyata,ZANYI KEWARKI ,daga masoyinki,kuma mijinki in Allah ya yarda MUHSIN."_

wassalamu alaikum

Hameeda ta na karanta text din ta na kuka ta rasa me ke ma ta dadi Aduniyar nannan.

Haka ta gama kukan ta har tai barci agun.

_________________________________________________________

A kwana atashi har Muhsin ya yi sati biyu da tafiya,Adam kuwa ya gama jarabawar sa zasu dawo gida .

Adam da Mubarak sun shirya tsaf,hakama Nusaiba wadda ita dai da ka ganta kasan ba ta son tafiyarnan.

Adam da Mubarak sun rakata har wajen motarta suna Allah ya kiyaye,Nusaiba ko ta kasa magana banda hawaye ba a binda ke zuba a idonta.

Har suka shige motar da a kazo dauka Kansu tana kallon su sai da motarsu ta tashi kan itama fara tafiya.

Hameeda tun safe ta tafi gidan Su Adam domin tarar yayanta Adam.

Ita da Aunty ne suka shiga kichin sai girke-girke su ke kala-kala,Mama in tazo hucewa sai dai ta CE aiki bai isheku ba ne,sai ka ce Abban Autane zai dawo kun wani zakye sai girki Ku ke kun cika ma na gida da kamshi."

Aunty ce tai murmushi ta na fadin, "Haba ke kuwa Mama D'a na ne fa daya tillo ke hanya ai dole na dage Dan wallahi ni na zaku ma ya yi ya dawo da,da yarda zanyi yadawo karatu agarinnan ai da na yi wallahi,gidan ba shi ba dadi."

Mama ta ce, "Oh wannan inaga to in kuma yayi AURE agidannan za ki ce ya tare."

Aunty tana dariya tana fadin , "Ai kin San ma wannan dole ne."

Duk da cewa Aunty ba ita ta haifi Adam ba Amman ta dauki soyayyar duniyar nan ta daura a kan sa,tun ya na karami ta ke wahalarsa har yau kuwa ba ta taba nuna gazawarta ba,ko yarta da ta Haifa ba ta nuna ma ta so kamar yadda ta nunawa Adam ba.

Hakan yasa kullum suke kara samun zaman lafiya da farinciki a cikn gidan su.

Auta kuwa ranar tak'i zuwa skul wai ita A dole sai yayanta ya dawo shi zai kaita,da kyar Mama ta lallabata sannan ta yarda aka kai ta tana dawowa kuma ta fara murna bai dawo ba ita zata fara ganinsa tuni ita da Hameeda suka je kwofar gida su ka tsaya.

Misalin karfe 3 na rana su Adam su ka iso.

Da gudu Auta ta karasa wajensa tare da rungume yayan na ta, ita kuwa Hameeda ta na ganinsa taji wani sabon lamari jikinta duk ya mutu,kawai kunyarsa ta ke ji,da Dane da tuni ta karasa ta na ma sa oyoyo Amman yau ta kasa.

Shi ko yadau Auta Amman hankalinsa na kan Hameeda kawai ita ya zubawa ido,ya ga ta kasa karasowa garesa.

Ba ta rai ya yi tare da fadin, "Ke ba za ki karaso ba ne?"

Urs XAYYEESHERTH

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOVE MESSAGE*

My love for you knows no bounds, it’s timeless and endless. You can enrich my life in more ways then I could ever express in words. I felt strongly connected to you the moment I looked into your eyes. I was drawn to your soul in a way I have never experienced before. You are the only one can see the door to my soul.