PAGE*-23
____________________________________________________________________________
A shagwabe Hameeda ta ce, "To bayan Auta ce ta rigani." Zuwa ta ke ta na fadin hakan.
Adam ya yi murmushi ya na, "Ai na zata zaki nunamin kin girma ne an dai na min Oyoyo."
Dariya kawai Hameeda ta yi tare da karban jakar hannun sa su ka shige gida.
Su na shiga Aunty ta tawo ta rungeme D'an ta tare da fadin, "Barka da dawowa my son."
Murmushi Adam ya yi tare da durkusawa kasa yana, "Nagode Aunty na na same Ku lafiya."
Dago dashi Aunty tayi tare da fadin, "Smile lafiyan mu lau,ma za jekayi wanka ka yi sallah sannan ka zo ga abincin ka nan komai ya na shirye."
Adam ya ce , "Ok Aunty ina Mama tsohuwa ne wa to ita ko murnar dawowa ta ma bata yi."
Mama ta fito tana, "Yoo ni ina ruwana da dawowarka ka dawo ka ishemu dai."
Aunty ta ce, "Eh munji son bar tsohuwar nan je kayi abinda ke gaban ka."
Adam kawai murmushi ya yi yatafi yana murnar kasancewa D'a ga Mama da Aunty DOMIN akullum kara birgesa su ke yadda suka hada Kansu su ke zaman lafiya tsakanin su.
Hameeda ce ta bi bayansa da jakarsa,su na shiga Adam ya kulle kwofar tare da fadin, "Hamee nah da alama kina cikin damuwa Dan ban sa ba ganinki cikin ya nayi haka ba."
Murmushi Hameeda ta yi tare da fadin, "Smile yayana ka yi wanka kai sallah in kaci abinci za muyi magana."
Adam ya ce , "Oh shikenan sai na fito."
Hameeda ta fita tana, "Adai yi wanka mai kyau kar ai jika-jika."
Adam kawai dariya yayi yana, "za ki sa ni zan fito ai."
A nutse Adam ya yi wanka ya gabatar da farilarsa sannan ya shirya cikin Kananun kaya,bluen Riga da farin wando,tare da Glass din sa Wanda ya saba sawa,da ka gansa kai kace wani babban taro za shi.
Aunty da Mama ne Afalo su na zaune.
Ya na fitowa Mama ta ce, " Ai mun za ta sai an shigo an janyo ka za ka fito ne."
Aunty ta ce, "Umm su Tsohuwa dai an cika sa ido,son rabu da ita ka je ga abincin ka chan Hameeda ta shirya."
Adam ya ce, "Aunty na rabu da Mama nasan damuwarta bai huce goro ta ke bukata ba."
Mama ta ce, "Dukkan su zaku sani ne Bari Abban Auta yadawo."
Dariya dukansu suke sannan Adam ya nufi wajen Hameeda.
Ya na zuwa ta ce, "Wooo yaya Messi na gaskiya turaran kan nan kamshinsa dadi dole in sace."
Adam ya tabu ne fuska, "Tab yasin ba ki isa ba budurwa ta ce fa ta siyamin ."
Hameeda ta ce, "Oh ka ce yan karya ne su ka siyama ba ma wannan ba ga food din ka nan bismillah."
"Woooo Amman dai Auntyce ta yi girkin nan daga jin kamshin,Dan nasan ita kadai za ta iya." Cewar Adam
Hameeda ta ce, "Ohooo dai ni kaci abinci."
Adam ko ya yi shiru sai afa abinci ya ke abin sa, Hameeda ko ta zuba masa ido ta na ta kallon sa.
Sai da Adam ya ji cikin sa yadauka dam sannan ya ce, "HAMEEDA ki nutsu muyi magana ba na son ki boyemin komai ki fadamin komai,me ke damunki? Miye damuwarki? Kar kiji tsoro ko shakkar fada min duk abin da ke faruwa."
Hawaye ne ya fara zubowa a idanun Hameeda ta rasa me ma zata CE da yayan na ta.
Adam ne ya fara goge ma ta hawayen da ke kwarara afuskarta ya ce , "Hamee na please ki nutsu mu yi magana."
Hameeda ta ce, "Yaya ......
Urs xayyeesherth
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ ππΉππΉππΉππΉ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*
You're Always On My Mind, Day And Night When I Think Of You, All Feels So Right Need To Have You, Need To Hold You And Tell You That I Love You. My Dear, I Don't Want To See Us Apart This Separation Just Tears Away My Heart I Miss You, Oh, I Really Miss You Will Need You More And More Each Day I Know I Cannot Live Without You I Miss You, More Than Words Can Say.