PAGE*-24
____________________________________________________________________________
*WANNAN SHAFIN NA KU NE YAN GRP DIN BENEFICIAL WRITERS ASSOCIATION mussaman ku Aisha humaira da AG ina yin ku irin sosai dinnan comments din ku na bani nishadiππππ*
Sai tai shiru, Adam ya ce, "Ina jin ki Hamee." A nan Hameeda ta kwashe duk abin da ya faru tsakanin ta da Muhsin da ma na Abban Muhsin da Dadynta ta fada ma sa.
Gaba daya jikin Adam ya yi sanyi domin ga dukkan Alamu Hameeda ta Amince da Muhsin, duk da cewa ya na jin kishin kanwar ta sa, to Amma fa wannan karon ya zama dole ya taimaka ma ta wajen cimma burin ta, domin farin cikin ta.
Murmushi Adam ya yi tare da riko hannun kanwar ta sa ya ce, "Haba Hamee na, A kan wannan karamin abun ki ka shiga damuwa?,indai wannnan ne na mi ki alkawarin duk ranar da Muhsin ya dawo, ni zan jagoranci maganar Auren."
Hameeda ta kasa d'ago kai ta kalli Yayan nata.
Adam ya d'ago ma ta da fuska ya k'ara da cewa, "Haba Amaryar Dan Shila Abokina Smile mana kinsan fa bana son ganin ki cikin damuwa."
Tuni Hameeda ta fara dariya ta na dukan yayan na ta wai a dole ya ce wa mijin ta d'an shila.
Aunty ta nunawa Mama tana, "Ni ko Mama Anya ba soyayya tsakanin Son da Hameeda kuwa?" Murmushi Mama ta yi tana, "Ai indai Adam da Hameeda ne ni na ka sa gane mu su kawai mu zubawa sarautar Allah ido."
Aunty ta ce, "Haka ne Amman dai zan yi farinciki in son ya sami Hameeda A matsayin Mata, barin yadda ta san halin sa shi ma ya san na ta."
Mama ta ce, "Haka ne kam."
Ranar kuwa Hameeda ta k'i tafiya gida Anan ta kwana ban da labaran makaranta ba a bin ya ke ba wa kanwar ta sa har ma da labarin Nusaiba da dramar da su kai A wajen cin abinci, ban da dariya ba abin da Hameeda ta ke mussaman in ta tuna gun cin abincin nan.
Karfe 11:00 Hameeda ta ce, "Umm good night yaya Adamu gwanda kai, ku ma kar ka man ta gobe da sassafe za ka ta shi mu fara karatu."
Adam ya ce, "Ok night sweetie saura ku ma ki zo ki isheni tun A suba." Dariya kawai Hameeda ta yi ta tafi dakin ta.
Ta na zuwa tai alwala ta yi sallah sai da ta yi karatun QUR'ANI sannan ta yi Addu'ah ta kwanta.
Haka ma Adam domin sun saba haka iyayen su su ka nu na mu su tun su na k'anana.
Washe-gari
Bayan sun yi sallar Asuba duk sun koma barci, Hameeda har ta kwanta ta tashi tuni taje ta tashi Auta da ya ke yau weekend ne su ka nufi d'akin Adam da ruwan sanyi su aboye.
Su na shiga Auta ta fara mintsinin Adam ta na, " yaya ka tashi safiya ta yi."
Ita ku ma Hameeda na ta watsa ma sa ruwan .
Adam ya na, "Haba Auta ku barni na yi barci na mana dan Allah na gaji fa."
Ya gyara kwanciyar sa kawai ya cigaba da barcin sa.
Hameeda ta fadawa Auta abu a kunne .
Ai ko tuni Auta ta gantsarawa yayan na su cizo a kumatu.
Da ihu Adam ya tashi ya na, "Auta wallahi yau sai na zane ki A gidan nan."
Kan ya ta so Hameeda ta dau Auta sun bar d'akin da gudu.
Adam ma gudu ya ke ya na bin su a baya.
Su na zuwa falo su ka zaune ku sa da Abba.
Abba ya na , "An fara ko?"
Auta ta ce, "Umm ba Yaya ba ne ya ki tashi mun tashe sa, shi ne wai sai ya da ke mu."
Abba ya ce, "Ah to ba abin da zai mu ku, ku zauna anan abin ku."
Ai ko sai ga Adam ya shigo ya na, "Allah yau Auta da Hameeda sai na zane ku a gidan nan."
Abba ya ce, "A'a fa ni na ce su ta so min kai."
"Allah fa Abba wallahi yaran nan sun raina ni ka bari in zane su."
Abba ya ce, "To ku bashi hakuri dan bakuda gaskiya."
Kunnuwansu su ka kama su na "sorry Yaya bazamu sake ba."
Abba ya yi murmushi ya na, "Yauwa yaran kirki."
Adam ya ce, "Umm za ku sa ni ne."
Hameeda ta kalle sa ta ma sa gwalo
"Abba ka ga yarinyar nan har gwalo ta ke min fa?"
Urs xayyeesherth
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ ππΉππΉππΉππΉ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*
when you wait for someone for few mintues-its need for few hours-its trust for few weeks-its friendship but when you know the person will not come and still wait-its love.