PAGE*-25
*Sorry for d late wishes br amman duk da haka vazan yi kasa agwiwa ba domin kuwa wannan shifin na ka ne kai kadai*
Wishing you all the fun and excitement that only birthdays can bring. Happy birthday yaya hayat admin of Adminsπππππ,Allah ya karo shekaru masu albarka. ____________________________________________________________________________
Murmushi Abba ya yi tare da fadin, "Ai kannen ka ne ka yi sorry kawai."
"Umm wai bako ya zo a na nu na ma sa banbanci yasin tafiya ta ma zan."cewar Adam kenan dai-dai da shigowar Aunty. Ta ce, "Wa ya isa ya koran min d'a na a gidan nan ai sai dai ku, ku fita." Dariya dukan su, su kayi Adam ya na, "Yauwa daz my lovely Aunty."
Bayan yan wasu kwanaki.
Adam ne da Hameeda Tare da Auta sun fito za aja shoppin.
Dukkan su Anko su kayi na bluen shadda, Adam ya sa farar hula da farin takalmi,haka ma Auta da Hameeda farin gyale tare da farin takalmi, Mama ce ta fito ta na murmushi tare da fadin, "Ah yaran kirki kun sha kyau Adawo lafiya a dai kula."
Hameeda ta ce, "Ameen Mama sai mun dawo."
Suna isa kuwa Auta ce kan gaba wajen shiga,da gudun ta.
Adam ya kalli Hameeda tare da fadin, "Ke ba kya yi gudun ba ne?"
Murmushi Hameeda ta yi sannan ta ce, "Ai in ka ga na yi gudu to kai ma ka yi ne."
" kut wato ka sa'an ki nan, lallai yar nan kin ga ma rainani wallahi."cewar Adam.
Hameeda ta ce, "Haba yaya Adamu na."
Tuni ya bata rai zai yi magana sai ga kiran ya shigo wayar sa, dagowan da zai yi sai ko ya ga lambar Nusy, murmushi ya yi tare da cewa Hameeda, "Ki shiga ki fara zaba ina zuwa."
Ba karamin bacin rai Hameeda ta ji ba kawai tafiya ta yi batare da ta kara furta komai ba.
Kara wayar ya yi a kunnen sa tare da fadin, "Amincin Allah ya tabbata ga saurauniya ta."
"Tare da sarkin da ya fi kowani sarki adalci." cewar Nusaiba.
Waya su ka yi sosai ta masoya domin zallar soyayya kawai su ke ginawa, a bisa tsarin da ya dace.
Tun daga ranar da Hameeda ta nunawa Adam cewa ta na son Muhsin shima ya kudiri niyar koyawa kan sa son Nusaiba, ko da kuwa zuciyar sa taki amincewa da hakan zai daure domin ya kawar da soyayyar Hameeda da ke son shiga zuciyarsa, *shi a gun sa soyayyar Hameedan ma ba ta shiga zuciyar sa ba wai so ta ke ta shiga, fans shin kun yarda wannan hasashen na Adam ku wa?*
Sai da ya gama iya kwokarin sa dan nunawa Nusaiba soyayya sannan ya bi bayan Hameeda da Auta wa'in da tuni sun gama siyayyarsu shi kawai su ke jira.
Tun daga nesa ya ke murmushi da ka gansa kasan cewa An faranta ma sa rai.
Hameeda na ganin sa kuwa ta bata rai kamar wadda ba ta taba dariya ba arayuwar ta.
"Oh wai har kun gama ne."cewar Adam
Hameeda ta ce, "Daman ina zaka san mun gama tunda ka na waya da wa ta yar iska,ka manta da mu kaman ka shanya gawar shanu."
Tun da Hameeda ta fara maganar nan Adam kawai ido ya zuba ma ta tsabar mamaki sai da ya ga ta tsaya sannan ya ce, "Kin gama ko da kari?"
Ta fara un'uni ta na, "A kan wata yar iska kawai........
Adam ya ce, "Hameeda! ina ni bakin ki ke furtawa magana haka?, nagode ba laifin ki ba ne, huce mu shiga mota."
Auta ta shige A bin ta ita ko Hameeda ta na tsaye ba bu alamar motsi.
Adam ya kara da cewa, "Ba ki ji me nace bane wai?"
Hameeda ta ce, "Na ji Amman kuma bazan shiga ba napep zan hau."
Tsabar bacin rai Adam bai san lokacin da ya kwashe Hameeda da mari ba.
*Ni ko ina gefe nace ana wata ga wataπ€*
Urs xayyeesherth ***
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ ππΉππΉππΉππΉ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE* π€£π€£ _Yau ba kalaman love na kai kasuwa asiyar min_