WASA DA SO

PAGE*-25

by @xayyeesherthulhumaerath

_Wannan fejin na kune ma su lekye min status๐Ÿคฃmussaman uncle bamai, shalele,babaxee,fauziya s madaki,kulsum, feedyn bash in ba ku daina kallemin status ba sai na muku tar gade akumatu๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜ina yin ku yan uwa na๐Ÿ’ƒ_ ____________________________________________________________________________

*BEST COMMENTS OF D MONT*

DAGA AYSHA HUMAIRA

Na gode sosai Allah yabat qauna

๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ก Amma fa yau Yaya adamu tom ya zafe ni over tayaya zai mare mu bayan ya gama soyayyar sa bamu ce masa komai ba๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ

Wlh ma ni tausayi take bani yaya zayyi mata haka Dan Allah

๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ๐Ÿคจ Wacece ma take da suna ku tunamun wan nan mara kamun ka da ita yanzu ko cemata akai mata an mata kyautar Messi ai yar๐Ÿ˜Ž

Dan tasan ba sonta yake ba kawai

Kuma kwaci qwal uwaku idan baku sasanta ba kuka ja aka shiga tsakiyar ku ehe๐Ÿ˜Ž

Muna godiya sista Allah ya qara basira da zaqin hannu๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

*TO FA KUN DAI JI SAKON NMCY GAREKU ADAMU DA HAMEEDA HAR MA KAWATA NUSAIBA*๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ

Rikye kumatun ta kawai tai sai ga hawaye na kwarara daga idanun ta, ta kasa dago kai ma bare su hada ido da Adam.

Rai a bace ya kara da cewa, "Wuce ki shiga mota mu ta fi ko?"

Hameeda ba ta ce komai ba illa tafiya da ta fara kamar wadda kwai ya fashewa aciki har ta isa wajen motar, sannan ta shiga.

Adam kawai cizan harshe ya yi sannan ya shiga motar, Auta ko ta kasa magana domin duk abin da akai a idanunta a ka yi.

Tuki Adam ya fara kawai gudu ya ke domin zuciyar sa ta fasa ta ke ba abin da ya ke fadi a zuciyar sa sai, "Me ya sa zan mari Hamee na, mai ya sa hakan?, Na ji haushin kai na."

Tambayoyi barkatai kawai yake jerowa kan shi wanda ya rasa dalili kuma ya rasa amsoshin su.

Hameeda kuwa tuni ta fada duniyar tunani, "Wai yau ni Yaya Adam zai mara! ko mummunan kallo bai tabamin ba bare mari, Amman duk da hakan ni na ja domin kuwa nasan ban taba ma sa magana cikin tsiwa ba."

Dukkan su ko wa da abinda ya ke ayyanawa acikin ran sa.

Duk da cewa Hameeda tunani ta ke tare da tuhumar kan ta amman hakan bai hana hawaye fita daga idanuwanta hakan ya sa Auta ma fara kuka.

Adam na kallon su ta mirro hakan yasa shi tsayuwa da tukin sannan ya fara fadin, "INNALILLAH WA INNA ILAIHIR RAJI'UN." Azuciyar sa har sai da ya ji zuciyarsa tai sanyi sannan ya fara tukin .

Bai huce da su gida, wani wajen shakatawa da yasaba kawo su kawai ya nu fa.

Su na isa ya fito tare da budewa Hameeda kwofa, ba mu su kuwa ta fito, haka ma Auta ta fito.

Adam ya ce mu su, "Ku zo muje."

Haka kuwa akayi suka bisa abaya wani gun zama yakai su tare da mu su alama da su zauna.

Sun fi minti goma da zama amman ba wanda ya ce wa kowa komai.

Adam ne ya durkusa tare rikwo hannun Hameeda kamar yadda ya saba aduk sanda ya gan ta cikin damuwa.

murya Araunace ya ce, "Hamee na, kin san yau kin batamin rai kuwa."

Daga ma sa kai kawai tai alamar eh.

Ya kara da cewa, "To me ya sa ki kamin rashin kunya?, ko da na mi ki wani abun da ya bata mi ki rai ta wannan hanyar yakamata ki sanar da ni?"

Kara daga ma sa kai kawai ta yi.

"Kin sa zuciya ta tai zafi har ya kai ga na mare ki, nasan cewa kin ji zafin marin ajikin ki amman ni na fi ki jin zafin domin kuwa azuciyata na ji sa, ki yi hakuri ki ya fewa Yayan ki bazan kara ba." yakarasa fadan hakan tare da rikye hannuwan sa biyu

Alokacin Hameeda ta dago tare da durkusa kamar yadda ya yi ta rikwo hannayensa biyu tare da fadin, "Yaya ni ce da laifi wallahi duk laifi na ne, domin kuwa nasan da ban ma haka ba bazaka taba mari na ba, kuma nayi danasanin yi ma rashin kunya, Abun da ban taba ma ba arayuwa, nasan cewa za kai tunanin cewa na girma ne nafara hakan." Ta karasa maganar ta na kuka.

Share ma ta hawaye Adam ya fara yi tare da cewa, "Ki bar kuka Hamee na ni ai nasan ba haka Hamee na ta ke ba, kin yanzu bari akawo ma na ice cream mu sha sai mu tafi gida ko." ya fada yana kallon Auta wada tuni ta wage baki domin an ambaci masoyinta.

Icream Adam ya je yakarbo mu su aiko tuni Hameeda da Auta su ka ware su na sha, Adam ko sai dariya ya ke mu su.

Da ka gansu kasan cewa su na cikin farinciki kaman ba su ne dazu ba.

Harda rige-rigen shanyewa tuni ko Auta ta riga Hameeda, ai ko Auta ta kwace na gun Auntyna ta shanye.

Sannan su ka tashi da nufar hanyar gida.

Urs Xayyeesherth.

***

๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ ๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน *WASA DA SO* ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ๐ŸŒน๐ŸŽ

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOVE MESSAGE*

Once in a white, great love comes to your life. it probably wont last but its good to know that at least once in your life, you had that kind of love