WASA DA SO

PAGE*-26

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

A kwana a tashi har lokacin jarabar Hameeds yayi Adam kuma zai koma makaranta.

Ranar da zai koma ranar Su ka fara zana jarabawar su.

Tunda Adam ya koma skul ba su kara waye da Hameeda ba kasancewar exams ya sha ma ta gaba, kuma Dady ya karbi wayar ta ma.

Adam da Nusaiba sun fara soyayya Amman zan iya cewa ba kamar yadda masoya su ke ba domin kuwa shi gudun ta ya ke duk da cewa yadage akan sai ya koyawa zuciyarsa son ta na dole amman hakan ya gagara.

Malamin su kuwa kullum acikin jan sa ya ke ajiki domin komai ya faru sai Adam ya sanar ma sa.

_________________________

sai da su Hameeda su ka kammala jarabawar su sannan su ka fara waya da Adam suna dan gaisawa amman ba kamar yadda su ka saba ba.

Muhsin kuwa yadawo daga neman kudi kuma ya samu ba laifi domin kuwa aiki ya yi tukuru domin ya ga ya mallaki abar kaunar sa.

Yau kwanan sa uku da dawo ya zo falo domin magana da iyayen sa.

"Abba nadawo nace ko za akarama iyayen Hameeda magana tun da dai yanzu ta gama makaranta."

Abba bai ce komai ba har sai da Mama ta kara da ce wa, "Haba Alhaji ba ki mai yaron nan ya ke cewa va ne."

Murmushi Abba ya yi tare da fadin, "Ko kun man ta da maganar da nai a bayane?, ni bazan hanasa auren Hameeda ba amman na cire hannuna dashi kuma bazan fasa ma sa fatan alkairi tare da sa albarka ba.

Tun da Abba yagama jawabin sa ya tashi tare fadin, "To ni dai natafi office sai nadawo.'

Muhsin Da Mama su ka ce , "Adawo Lafiya."

Ya amsa da, "Ameen." sannan ya fita.

Mama ce ta juyo ga Muhsin ta ce, "To dai ka ji amman a ganina hakan ba matsala ba ne kaje ka sammi Alhaji Ahmad."

*Babban Aminin Abban muhsin kennan*

Muhsin ya ce, "Ai kuwa Mama shikennan, nasan ina zuwa gun Baba Alhaji magana ta kare."

Muhsin ya fita cikin farinciki domin yasan cewa kaman ya Auri Hameeda ne da yardar Allah.

Aikuwa ya na zuwa yasanar da shi bai bata lokaci ba ya nufi gidansu Hameeda.

Bayan ya je sunyi magana sosai sannan Dadyn Hameeda ya nuna ma sa ce wa ba komai tare da sa ranar Aure nan da wata daya .

Tunda Muhsin ya ji wannan lamari farinciki ya kasa gushewa azuciyarsa,Hameeda ko ita ji tai kamar kullum abun bai dameta ba ko ajikin ta.

Ta fannin gidaje biyun nan kowanne kawai shirye-shiryen biki ake.

Adam ko ya na makaranta bai ma san me ke faruwa ba,Amman wani lokacin ya kan tsinci kan sa cikin damuwa,duk da cewa sun gama makaranta saura kwanaki kadan su dawo gida amman ji ya ke kaman shekaru zai kara, kawai damuwar sa bai wuce ace ya dawo gida ba.

****************************

A kwana atashi yau Adam ya kammala makaranta zai dawo gida kamar yadda saura kwana bakwai bikin Hameeda ka na ganinta kasan cewa ta tana da damuwa domin ku duk ta rame ta yi baki.

Adam ya ki fadawa kowa zai dawo wai shi adole surprise zai mu su mussaman ma Hameeda.

Gidan su Hameeda yafara zuwa a ka ce ma sa ai suna family HOuse gaba daya harda su Momynsa Domin za ai bikin Hameeda.

Abin ya matukar bawa Adam mamaki duk da cewa yasan maganar Muhsin da Hameeda.

Ba inda ya nufa sai Family house din su banda bugu ba abinda zuciyarsa ke ma sa.

Urs xayyeesherth

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOVE MESSAGE*

❀❀❀ when you love someone is not special but when you are loved by every one is the most special thing in life.