WASA DA SO

PAGE*-27

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

Ya na zuwa ku ya iski gida ya cika tam, dan haka kuwa ba tantama Auren Hameeda za ayi. "Subhannallah."kalmar da ya ke iya furtawa kennan.

Jan kafar sa ya ke da kyar har ya shiga ciki Auntyce ta tawo da sauri tare fadin, "Oyoyo Son Amman gaskiya ka shammace mu fa, da har ina gobe azo adauke ka ka zo ayi biki da kai."

Murmushi kawai Adam ya kewa Auntyn nasa domin maganar ma ya kasa.

Hameeda ce ta fito da murmushin ta tare da fadin, "Yaya messi welcome ai na zata ma bazaka zo ba." a shagwabe ta ke maganar kamar yadda ta saba.

Aunty da ta fahimci d'an na ta cewa akwai matsala ce wa tai, "Son zo mu shiga daga ciki, ke kuma Hameeda ki je ki karbo mana dinkin."

Aunty kawai jan Adam ta ke domin tafiyar ma da kyar ya ke.

bayan sun zauna ne Aunty ta ce, "Son me ke damunka ne?"

Dauriya Adam ya yi tare da fadin, "Bakomai Auntyna kawai dai ba na jin dadin jiki na ne."

Aunty ta tashi tare da fadin, "To jirani ina zuwa."

Alokacin Adam ya ji wani abu ya tarnake masa azuciya "Aunty, Aunty ki tsaya zan mutu."

Ahankali ya ke maganar domin kuwa zuciyon ya fara cinsa.

Da sauri Aunty ta karasa waje ta sanar da su Mama da driver domin aje asibiti.

Kan su karasa asibi Adam ya dai na motsi kwata-kwata.

Aunty ta na kuka tana fadin, "Son kar kamin haka dan Allah kar ka tafi ka barni."

A haka har su ka isa asibitin, likitoci suka taru akan Adam kowa ya na iyaka bakin kokarinsa.

Tun safe har dare yayi ba likitoci Ba Adam.

Sai kusan asuba su ka fito tare da musu albishir cewa an samu damar ceto rayuwar Adam da kyar.

Ba karamin murna dukka family su ka yi ba kasancewa Adam ya na daga daga cikin wanda aka fi ji da shi a family.

Bayan su Dady sun zo sun gansa sun tabbatar da cewa jikin da sauki sannan su ka koma gida akabar Hameeda Akan Aunty zataje tai wanka inta dawo sai Hameeda ta koma.

Hameeda na shiga dakin Adam ya kalleta da murmushi tare da fadin , "Hamee na."

Hameeda ta ce, "Sannu Yaya Messi wai Muhsin na gaishe ka anjima zai zo."

Adam ya riko hannun kanwar ta sa tare da fadin, "Hameeda,yanzu nasan cewa na yi kai na babban illar ta dalilin *Wasa da so* ban san cewa ina mi ki so na Aure ba sai ayanzu,Hameeda dan Allah kar ki gujeni akan ki zan iya rasa rayuwata,Hameeda ina son ki wallahi da gaske na ke ina sonki, sonki ne ya kai ni cikin wannan halin,ki aminta da ni mu rayu dan Allah."

Tunda ya fara maganar nan Hameeda kawai kallon mamaki ta ke masa sai da ta ga yayi shiru ta ce, "A'a A'a Yaya Adam ba na son wannan wasan ka bari karka kara bana so ni Muhsin zan Aure,ka dai na min haka wasan ka ya yi yawa,ka bari dan Allah."karasa maganar tai tana kuka tare da fincike hannun ta, ta fita daga dakin.

Adam kuwa banda hawaye ba abinda ke kwarara a idanunsa azuciyarsa ko sai fadi ya ke, "Ni na cuci kai na daman nasan Hameeda ba za ta taba yarda da ni ba wallahi nayi dana sanin *Wasa da so* sai ayau nasan me nene so."

_Ni xayyeesher na ce ko ya abun zai kasance? ku biyo ni domin ganin Ya zata kaya......._

Urs xayyeesherth

***

🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹 *WASA DA SO* 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍 🌹🎍🌹🎍🌹🎍🌹🎍

_{ Ganganci }_

*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🀝🏻*

_________________________

*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________

*Story And Edited By:*

*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_

*Writing by:*

*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_

*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*

*LOVE MESSAGE*