PAGE*-28
____________________________________________________________________________
Hameeda na fita kuwa ta ci karo da Aunty, tuni ta goge hawayenta kan ta karasa, Aunty ta ce, "Fatan dai ba jikin Yayan na ki ba nE?"
kawai girgiza ma ta kai Hameeda ta yi alamar Aa, ita ko Aunty ba ta tsaya ba ta amsa ba ta shige ciki.
Ta na shiga ta tarar da Adam ban da hawaye ba abin da kwarara daga idanun sa, da sauri Aunty ta kasara tare da fadin, "Menene kuma son ko dai jikin ne a kira likata."
Rikwo ma ta hannu ya yi tare da fadin, "Aa Aunty ki zauna ba komai."
Aunty ta ce, "Indai zan zauna sai ka min alkawarin za ka fadamin abun da ke damun ka."
kawai zub da kwalla Adam ya cigaba da yi domin kuwa in bai manta ba Aunty ma ta ta ba fada ma sa cewa ya na *wasa da so* da kyar kuwa ta shawo kan sa, sannan ya fada ma ta komai abin da ke faruwa tun ya na makaranta kawo yanzu.
Ba karamin tausayin Adam ya ba wa Auntyn sa ba domin tun tuni ta ke guje ma sa wannan ranar.
A karshe ya kara da cewa , "Aunty Dan Allah kimin Alkawarin cewa wannan maganar ta zama sirri, ni zan iya jure komai indai Hameeda za tai farinciki a gidan Auren ta."
Aunty ta ce, "To kai kuma lafiyar ka fa son, kennan farincikinta ya fi lafiyar ka da farincikin ka."
Murmushi kawai Adam Yayi sannan ya ce, "Bakomai Auntyna ai kanwatace."
Duk da haka dai Aunty ta kasa walwala a asibitin nan sai ya kasance Adam ya zama kaman shi je jinyar ta sai ma ta wasa da dariya ya ke duk dan abun ya bar ran ta,duk da cewa kuwa shi ya san mai ke damunsa azuci.
Daga karshe dai likita ya zo ya Domin sallamar su tare da ba wa Aunty shawara akan cewa, "Duk abin da Adam ya ke so amasa indai ana son rayuwarsa."
To fa anan hankalin Aunty ya kara tashi, Adam kuwa ya nuna ma ta cewa ko ajikinsa, Gashi ba ta da damar fada domin tq dau masa alkawari.
Tunda suka koma gida Hameeda ke gudun Adam , shiyasa da ya fahimci hakan ya ma dai na fitowa kullum ya na daki.
Muhsin kuwa Mubarak ya sanar dashi komai akan yq taimaka ya barwa Adam Hameeda Amma ya yi burus tare da da fadin ai shima son tq ya ke kuma ma yq fi Adam son ta.
Akwana atashi yau saura kwana daya bikin Muhsin da Hameeda.
Sun shirya tsaf domin tafiya kamu.
Urs xayyeesherth
***
πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ ππΉππΉππΉππΉ *WASA DA SO* πΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ πΉππΉππΉππΉπ
_{ Ganganci }_
*TRUE LIFE,LOVE STORY.* _(Labarin Soyayyar Gaske)_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONπ€π»*
_________________________
*We are here to educate,motivate,and entertain our readers.* _________________________
*Story And Edited By:*
*Mubarak A Kamba* _(Ramadan Mubarak)_
*Writing by:*
*Aisha Mohammed Sani* _(Xayyeesherth)_
*Facebook:Aisha Mohammed Sani.*
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*LOVE MESSAGE*