WASA DA SO

PAGE*-29/30

by @xayyeesherthulhumaerath

πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šοΈ____________________________________________________________________________

_SADAUKARWA GAREKU YAYUNA HASSAN ATK$HUSSAINI ATK ALLAH YAKARA RAYUWA MAI ABARKAπŸ™_

*Godiya ta mussaman gareka YAYA Mubarak Allah ya kara basira da daukakaπŸ™ALLAH YA BAKA ABIDILLEπŸ₯°*

*FEjin yau dai ba editing kuyi hkr da typing erorrs*

Fitowar da Adam zai yi domin tafiya ganin Muhsin da Hameeda ne ya rikita ma sa zuciya tuni ya fadi akasa,Hameeda ko na hango hakan tuni ta tawo da gudu tare da zuwa wajen yayan na ta,kan ta karasa har numfashin sa yadauke.

Kuka ta fara tare da kiran su Mama,Momy da Aunty,ai ko tuni aka dau hanyar asibiti.

Su na zuwa aka fara Adam taimakon gaggawa , anyi sa'a wannan karan bai kai na wancen jimawa ba amman wannan din ya fi hatsari domin kuwa ya na dab da rasa rayuwar sa,Hameeda na dakin ta ki fita rikye ta ke da hannun Yayan na ta, ai ko ya na farkawa murmushi ya yi tare da fadin, "Hamee na bakuje gun kamun ba ne, ku ta fi nima zan zo."

Hameeda ta ce, "Aa ai an ma fasa."

Adam zai yi magana kennan sai ga likita ya shigo.

"Barkan ka dai Adam ya karfin jiki?"

Murmushi ya yi tare fadin , "Jiki Alhamdulillah likita."

Likata ya kara da cewa, "Ka na dai daurewa ne kawai, amman dole akwai abun da ka ke so kuma in baka samu yanzu ba ina da tabbacin ka kara faduwa irin ta yau ka yi ta karshe kennan."

Daga idon Hameedan har Adam hawaye ne kawai ke zuba,sai ita tai dauriya tare da fadin, "Ba zai mutu ba insha Allah likita,zai samu abun da ya ke so."

Adam na jin hakan tuni ya tashi daga kan gadon tare da fadin, "Da gaske ki ke Hameeda?.

Daga ma sa kai kawai ta yi tare da rufe fuskarta.

Adam bai san lokacin da ya rungume Hameeda ba tsabar murna.

Likata kuwa fita yayi kawai yana murmushi sannan ya sanar da su Abba da Momy duk abin da ya fahimta ga me da hakan,ba karamin farinciki Aunty tayi ba da jin hakan.

Tuni aka sallami Adam.

Suna komawa ba jimawa Muhsin da kan sa ya zo yana taya Adam Murna tare da fadin ai bakomai daman Allah ya yi Hameeda ba matar ba ce ya dauki hakan amatsayin kaddara kuma ya sanar da iyayensa komai sun fahimta.

Ancigaba da shagalin biki kamar yadda aka fara amman fa Adam baya barin Hameeda ko ina ta yi yana biye da ita duk wanda ya masa magana yakan ce masa, " *Ni fa ku barni nasan illan wasa da so gwanda nai tatttalin abuna, dan da tuni an gama kayar dani*."

Shi dai Adam gani ya ke za akwace ma sa Hameedar sa.

Dariya kawai su ke domin su kan su sun dau babban darasi akan rayuwar Adam Da Hameeda.

An daura Auren Adam da Hameeda, Dady ya ba su wani karamin gidan sa achan su ka tare.

Mubarak kuwa soyayya ta kullu tsakanin sa Da Hameeda suma an fara shirin Auren su.....

Bayan shekara biyu......

Hameeda ce ta fito da wani lukekyn cikin ta haihuwa ko yau ko gobe ta na shagwabe fuska tare da cewa, "Honey ni fa ice cream zan sha."

Adam da ke kallo A TV juyowa ya yi ya na, "Ah Mama Lutiya yau Yan abun sun motsa kennan yau ba ni ba hutu daga wannan sai wancen."

Zama Hameeda tai tare da fara kuka tana, "Ni wallahi in ba zaka siyomin ba sai na baka Babynka daman ni na gaji."

Dariya Adam ya yi, ya tashi ya na, "yoo ni nama isa?, ai tashi muje."

Rikyeta ya yi suka fita tare.

Haka Rayuwa ta cigaba da kasancewa cikin farinciki Da anashuwa tsakanin Adam da Hameeda.

*ALHAMDULILLAH,ALHAMDULILLAH YAU DAI ALLAH YA YI NA KAMMALA WANNAN LITTAFINA MAI SUNA WASA DA SO,ABIN NAYI KUSKURE ACIKI ALLAH KA YAFEMIN,ABIN DA NAI DAIDAI ALLAH YASA YA AMFANAR DA AL UMMA, AMEEN YA ALLLAHπŸ™*

_Nagode sosai masoyana wajen bani hadin kai acikin wannan littafin nawa inan ta fe da sabo amman kan ya zo ga wanda na fara nan ni da kawata eyman maj suna *Yaya Imran* fatan zaku cigaba da bibiya kamar yadda akasa ba_

Duk mai shawara,sharhi,neman karin bayani ta nemeni ta wannan numberπŸ‘‡

***

Urs xayyeesherth