BABU RUWAN SO

PAGE 1

by @xayyeesherthulhumaerath

----------------------------------

Fayal ce xaune akan kujera futo war su kenan daga lectures ita da kawarta Amnah chating take yi ciki 'kware wa Amnah ta kalle ta tace. ‘’ Fayal wai me zakicine mukazo nan nikam kitashi mutafi gida mana.‘’ magana take mata amman kaman ba da ita take ba tawani hada rai tare da bada hankalinta ga waya Da take hannun ta Amnah tasan halin kawarta ta sai tayi shiru bata kara cewa komai ba.

Wani saurayi ne yadau wanka yaci fararen kaya shiba mummana ba kuma bara ace mishi kyakkyawa ba.

Da sallamarsa yataho garesu. Amnah ce tace. ‘’ walaikumussalam.‘’ kujera ya samu ya zauna Alokacinneh Amnah ta tashi tabar gurin domin tasan halin kawarta da disga mutaneh bataso ta tsaya agabanta ta hulakanta wannan mutumin ba.

Saurayi yace. ‘’ To nidai sunana auwal Ana kiranah da Arfan kuma ni dan garin katsina ne babana ne sarkin katsina nine d'ansa nafari.‘’Duk maganar nan dayake bata dago ta kallesa ba balle tasan waye.

Yacigaba da cewa. ‘’Dan Allah ko dan iya sanin sunanki.‘’Bata dai kulasha ba sannan shikuma be gaji ba yace. ‘’ sonki nake da aure so na gaskiya.‘’ 'Dauko eye pices dinta yi tasa akunneh Sannan ta tashi tabar gurin wanda har ta tashi ko kallon inda Auwal yake batayi ba.

Tabar shi zauneh awajen abun da tayi masa ya matukar basha mamaki irin hali da miskilanci na yarnan Ko kalloma be shita tayi mishi ba da tunani iri iri yatashi yabar wajen motarsa ya je ya hau ya bar gun aguje.

Fayal tana tashi tanufi inda sukayi paking din motarsu domin tasa Amnah na ciki Tana zuwa ta hau Amnah da fad'a tace. ‘’ amman dai kinsa bana son irin wannan abunko kawai kinbarni dawani kato yazo yanatamin zuba kamar parrot? Amnah tace. ‘’Nasan hula 'kantashi zakiyi shiyasa na bar gun, har yanzu kin ki chanjaa halinki,wallayi Fayal ina kujemiki ranar da zaki fara son wanda bai ma da lokacin ki, ki tuna fa kamar yadda kikema wasu haka za,a miki,Fayal tace. ‘’ Ke dalla cen meye ma wai so hmm wallahi ni banga wani abu asoyayya ba inbanda bata lokaci dan haka ni dakika gannin nan ban da lokacin da har zan tsaya batawa akan wani banxa .‘’

Amnah takara ka da baki tace. ‘’ A bi dai ahankali domin wataran ke zaki zubda hawaye kamar yadda wasu suka zubar akanki.‘’

Fayal tace. ‘’ hmm suma wallahi suna daurawa kansu wahala ne bani na nace suxo susoni ba ai ko? Dan haka kowa yayi takansa banzaYe wahallalu dasu,Nikam mikwomin key mutafi dan wallahi har kinsa nagaji domin nayi magana dayawa yau.‘’

*zamu gani shin tusa zata hura huta kuwa wane rayuwa fayal zata tsinci kanta*