BABU RUWAN SO

PAGE 9,10

by @xayyeesherthulhumaerath

--------------------------------

Amsard yaciga ba dayiwa student bayani.

Amman acikin zuciyarsa tunanin fayal yake.

Oh afili kuma yace"oh wai nikam ma ina ruwana da ita.

Miye damuwata ai ita tawa kanta.

Mtws.

Usman yace"yadai amsard naji kaman kana magana.

Amsard da baima san maganar zuci ta fito fili ba.

Yayi murmushi sannan yace" aa no bakomai.

Ahaka sukagama practical dinnan Amman Amsard yarasa me yasa yake tunanin fayal.

Duk yadda yaso yabari amman yakasa.

Awata zuciyar kuwa cewa yake inaga dai tausayinta nake.

Yanata sake sake azuciya.

su amnah sun fito kenan ta hango motarsu.

Dan haka ta nufa wajen domin ita atunaninta driver ne yazo daukanta.

Tana zuwa taga abin mamaki abin da bata zato.

Fayal ce zaune tazuba uban tagumi tana kuka.

Arikice Amnah tashiga tare da fadin"yaya dai fayal lafiyan ki kuwa kike kuka haka?.

Fayal takasa magana saima wani kukan dayagara tawowa.

Bashiri amnah tafara driving .

Gudu take akan titi domin jikin fayal yadau d'umin zazzabi tafara.

Fayal rawar sanyi take matuka.

Domin yau tayi kukan da bata tabayi ba tunda tazo duniya .

Niko nace wace take ganin magana aikin wahala ne inaga kuka? Hmm.

Da isarsu gida Amnah tashiga domin sanar da momy.

Momy tafito arikice domin shiga da fayal cikin gida.

Ita kuma Amnah takira family doctorn su domin yazo yaduba jikin fayal.

Kafin likita yazo har momy tafara d'uma ma fayal jiki da ruwan zafi.

Har zazzabin yafara sauka.

Sai ga doctor Abdulrahman ya iso.

Isowarsa keda wuya yashiga dubata . Sannan yasa abata koda tea ne tasha yamata allurar barci.

yana mata kuwa tasamu yin barci. Bayan doctor yatafi ne momy tafara"Tambayar Amnah wai meyafaru ne?

Batare da bata lokaci ba Amnah tama momy bayanin yadda komai yakasance.

Momy taji dadin abin nan ba duk da tasan laifin yartace Amman bataji dadin hakan da amsard yamata ba.

Allah sarki uwa da y'a kenan.

Momy tace"hmm to dai Allah yashiryamin ke fayal bansan ya zanyi dake ba sai dai mucigaba da addu'a .

Amnah tace"Ameen momy.

bara nayi sallah sai indaura mana abinci.

Momy tace"ok nima bara nayi sai mushiga kicin din tare.

Suka tashi domin sallah bayan sun idar suka nufa kichin domin daura abinci.

Fayal barci take Amman ganin abin da yafaru take acikin idonta.

Afirgice tafarka tare da fadin"wai ni yau wani zai wulakanta!!!!!

Wallahi wallahi sai sai na rama abin da yamin.

Yanzu zan fara asalin wulakanci tunda da ance INayi nikumA banga hakaN ba.

DAn hakA yanzu da afara.

Hmmm niko nace kome da afara? Sai kubiyo ni Aysherth(preety xayeesherth) Domin sannan me za afara cewAr fayal.

Bayan su momy sun kammala girkinne suka fito .

Fitowarsu keda wuya sukaga fayal zaune afalo.

Da alamu dai tunani take.

ko tunin me take? ohoo dai.

Amnah ce tafara magana"fayal kin tashine? Ya jikin?

Sannan momy tace" sannu fayal.Ya jikin dai?.

duk maganar nan bata dago ba sai daga baya ta yatsina fuska tare da fadin dasauki.

Tun daga nan bata kara cewa komai ba.

Suko su momy da hike sunsan haka halin fayal yake sai abin bai damesu ba.

sabida hakan yabi musu jiki.

Tafiya sukayi suka fara jera abinci adainin.

Bayan su kammala ne sukace da fayal tazo taci abinci.

taje tazauna Amman tunani take. Har yanzu abin yaki bace mata a ido .

Niko nace ai ke kikajawa kanki.

anzuba mata abinci amman takasaci.

Momy ta lura da hakan Amman tashareta. SAi Amnah ce ta ka da baki tace."fayal bazaki ci abincin bane?

FAyal"ta yatsine fuska. Sannan tace na k'woshine fah.

Sai alokacin momy ta bude baki tace"wallahi indai yau bakici abincinan ba sai dadynku yaji abinda kika aikata askul .

Kinsan dai inasane dakomai ko?

Fayal ta girgiza kai tare da fadin "aa danci.

Ahaka faya ta chacchakula abincinan tabari wai adole taci.

Domin ita dama asalinta cin abinci wahala yake mata.

Suna gama ci FAyal taje tayi sallar la'asar sannan takoma gado. **** Abangaran amsard kuwa sun koma gidan usman dake jigawa .

SUNa isa yatarar da matar usman phertymerh sai fara"ah take.

Dasauri tazo ta karba jakar mijinta tanamai sunnu da zuwa.

Amsard kuwa murmushi yake.Domin usman da pherty na birgeshi.

Pherty tace"ah kacemin yau munada babban bakwo agidannan .

Amsard yace"oh sai yanzu kikaganni ? Bayan kingama karban mijinki?

Pherty tayi murmushi sannan tace"hmm ai kasan halin naku ne sai ahankali inmuka sake sai amana kari.

Amsard da usman suka sheke da dariya .

sannan Amsard yace"ashe dai anajin tsoronmu.

pherty tace"ai dole munma wallahi harda gudU.

Shidai usman ba abinda yake musu banda dariya.

Pherty tace"gwandama ogana fa ashe tunda kai har yanzu ko budurwar ma babu.

Antsaya anamin bakin cikin samun kawa.