PAGE* 13,14
---------------------------------------------------------
Fitowar Fayal kenan daga mota . Tana yatsina fuskar nan kaman yadda tasaba.
Amsard kawai tsayawa yayi domin abin mamakima yabasa"wato ma abin yarinyar nan har yakai haka!. Yake fada azuciyarsa.
ita kuwa batamasan dawani abayanta ba tafiyarta take cikin isa da k'asaita.
Amsard yafito shima sannan yanufa wajen usman.
Dazuwansa bayan sun gesa da usman sai yace"usman wai dama haka yarinyar nan take?. Ita yar wayema wai agarin nan?."
Usman yanunfasa sannan yace"hmm daga maganar nan take nagane wa kake nufi Domin nasan inba fayal ba ba wace zata nemi b'atama rai".
Haka take kuma wallahi karkayi tunanin wai iyayen ta ne suka goyamata baya domin wulakanta mutane.
Aa ba haka suke ba domin su kullum fatan ta gyaru suke domin su kansu basa ganewa halayenta ".
Karkaji mamaki innacemaka bata da samari domin ita aganinta soyayya bakomae bace bace wahala . Batasan cewA *BABU RUWAN SO* ba ita tadaukesa amatsayin shirme".
Amsard ya nunnfasa tare da fadin"hmm A lallai wannan tacika miskila duk miskilancin dasu momy sukecewa inadashi insuka wannan yarinyar sai sun sara mata. Domin komai nata nadaban ne . Amman insha Allah ni nadau Alkawarin sai na chanja mata hali kai dama rayuwarta ta gaba daya".
Usman yayi murmushi sannan yace"anya kuwa abokina baka fada ba?".
Amsard ya sheke da dariya sannan yace "haba kai kam usman me zanyi da ita kawai dai inaso na nuna mata *BABU RUWAN SO* ne. Sabida takiyaye wulakanta masu sonta".
Usman yace"aa fa dai kar azo daga baya akamu kuma".
Amsard yayi murmushi'sannan yace kadai ka tsaya kaga dramar nan . Domin yanzu za,a fara".
usman yace"toh shikenan fatan alkairy nakewa abokina".
Amsard yacewa usman"yagode sannan yakarasa maganar dacewa su tashi su tafi domin fara aikinsu".
ita Kuwa fayal tine taje tasamu waje tazauna sai alokacin Amnah kecewa"fayal kinsan kuwa dazu wannan lecturern abayanmu kuwa kikaki matsa me"?.
Fayal ta dago sannan taja dogon tsaki tare da cewa"ai gwanda haka indai ko shine yanzu yafara ganin abubuwa kala kala sai randa yabar makarantar nan zai rabu da jarabawata".
Amnah batasan sanda ta shek'e da dariya ba sannan tace"lallai ynzu kinaso ki taro wanda yafi karfinki, anya ma kin kallesa Da kyau kuwa?.
Fayal tace"toh uwar kalle kalle ni me zan kalla ajinkisa me yake dashi".
Amnah ta karAshekewa da dariya sannan tace"amman gaskiya zanji dadin wannan dramar taku . Za,asha kallo awanga makaranta.
Fayal tace"kyaji dashi dai nikam wlh duk akan mutumin nan kwanann sai magana nake mtsww".
Ita dai Amnah dariyar ta take domin taga tun ynzu yar uwarta ta tafara magana inaga in aka fara dramar?.
Hmmm kallo nagaba kubiyoni danjin yadda zata kaya.
Amsard ya usman sun shiga domin fara practical.
Shigarsu keda wuya kawai Amsard yaga fayal azaune .
Abin yabasa mamaki azuciyarsa yace"toh yar girman kai yau anzo kenan.
Sunfara practical dinsu cikin nutsuwa ita kanta Fayal sai dataji farinciki tanata tunani ashe fa jiya tayi missing sose,wata zuciyar kuma tace sai me? mtsw".
Suna kammalawa fayalce tafara fita aiko da amsard yaga haka sai yayi sauri yabita.
Tashiga mota tanajiran amnah .
Shiko Amsard yana zuwa yahau motarsa sannan yasha gaban tata.
Fayal tace"owk wato mutumin nan adole shima so yake ya rama abinda name dazu ko? Alallai naga alamon cewa bai san wacece fayal ba, Amman yaro kakusan sanin ni wacece yadda inma kaganni barakaso karasawa inda nke ba balle ka kalleni".
Tana maganar nan Amnah nashiga motar aiko ta figa motar da gudu.
Amsard yana ganin haka shima yafara gudu.
Fayal tayi tayi yadda zatayi ta huce Amsard Amman takasa gashi daman ita ba iya gudu sose tayi amota ba.
Aiko ananne ranta yakara baci batasan sanda ta figi motar da mugun guba.
Aiko karaf sai gashi tayi gware da motar Amsard .
Amnah tun tana magana tana ta"haba fayal kiyi ahankali mana ko kibani nayi driving din.
Duk magiyar nan da Amnah tayiwa fayal Amman bata saurareta ba hasalima batasan me take BA.
Aiko amnah naganin sunyi karo da mota ba abinda take fada sai" innalillahi-wa'inna -illaihir-raji'un".
Ita kuwa fayal ko numfashima batayi bare motsi.
Shiko Amsard yabuga kansa ajikin madubin mota kansa sai zubar jini yake.
Amnah gaba daya tarasa ta yadda zata fara dominga fayal nan kwance ko motsi babu .