PAGE* 15,16
-------------------------------------------------------------
Dasauri Amsard yafito amotarsa domin duba motar su fayal.
Yna zuwa yaga Amnah sai kuka take tana salati.
Dasauri yataimaka mata suka fito da fayal . Sannan yakaita motarsa domin daman shi ba abin da yasami motar tasa sai dai kansa dake zubar da jini.
Tuki yake Amman duk hankalinsa baya jikinsa gabadaya ya rikice kawai tuk'i yake.
Da isarsu asibiti akazo domin awa fayal taimakon gaggawa .
Sannan shima Amsard yaje aka me treatment din kansa.
Ita kuwa Amnah ba abinda yasameta dan haka ta kira momy awaya domin sanar da ita halinda ake ciki.
Aikuwa da fadarta momy tace"gatanan zuwa ".
Bajimawa sai ga momy ta iso adaidai wannan lokacin kuwa fayal ta farfado.
Momy tashiga dakin tasamu fayal da Amnah tace"wai ya akayi haka neh?.
Amnah tabude baki zatayi magana fayal tamata alama datayi shiru. Aiko Amnah tayi tsit domin tasan halin fayaL.
Fayal tace"uhymm momy wata motace abayan mu tana gudu nikuma kinsan ban iya gudu ba shine fa kawai mukaci karo".
Momy tace"hmm toh shikenan dai Allah yakyauta abinma yazo da dan sauki".
Amnah tace"Ameeen".
Fayal kuwa tayi dogon numfashi domin ta tsira da kyar dan tasan in momy tasan gaskiya bazataji da dadi ba.
Doctor yazo yaduba su sannan yace" ga takardar sallamarsu nan angama komai".
Momy tace"toh ai ban biya ba ".
Doctor yace"ai wanda yakahosu ne yabiya".
Momy tace"owk ko zan iya ganinsa?.
Doctor yace"a'a ai ankirasa wai yana sauri shiyasa ma bai tsaya muku sallama ba".
Momy tace"owk to mungode Allah yabiya".
Suka kare dacewa"Ameeen".
momy ko dady bata kira ba suka tattara suka nufa gida domin fayal ta dan warware.
Shiko Amsard yana tafiya ashe managen sa na chan malesia ne yakirasa domin wani aiki na gaggawa wanda dole sai da shi abin zai tafi dai'dai.
Su fayal na tafiya Amota Amman kwatakwata hankalinta baya jikinta gaba daya tunanin irin wulakacin da zatawa Amsard take.
Batama jimamin jikinta sai wani jarabar datake tarawa.
Ita aganinta ma wato ya rainasu ne da har zai biya musu kudin asibiti.
Watomah yadaukesu matsiyatane ko?.
Hmmm duk dai wannan maganar datake ta zuciya ce dan haka babu me bata Amsa.
Amsard sauri sauri yake yakira usman yace masa"su hadu a airport domin ko katsina bazai koma ba malesia kawai zai huce" .
Shiyasa yace"yazo yakarba motar .
Aiko nanda nan sai ga usman yazo.
Usman yace"kaiiii Amman gaskiya banji dadin abunnnan ba nida naketa shirin kallon dramar miskili da miskila".
Amsard yayi murmushi sannan yace"oh yaro ai kabar dadi tun yau mukafara dramar kuma gashi kayi missinh" .
Usman yace"oh haba dai abokina bani labari mana".
Amsard yaduba agogon hannunnsa sannan yace kaga yanzu jirginmu zai tashi kabari sai munyi waya koma hadu a whatsApp.
Kuma ma ai ba dadewa zanyi ba karka damu kakusa zama drectorn dramar mu".
Usaman yashek'e da dariya hade da cewa"lallai kam toh adawo lafiya actor na actress".
Shima Amsard yayi dariya sannan yace"toh sai na isa kajini ko?.
SUKa gesa tare da yin sallama.
Amsard yahau jirginsu suka tashi. Yayinda shima usman yahau motar domin komawa gida.
SU fayal sun isa gida adai dai lokacin da daddy yadawo .
Fayalce tafara fitowa tare da Amnah data rike mata hannu.
Daddy abin ya razanasa domin bai san meke faruwa ba kuma gashi yaga yarshi ba dai dai ba.
DAddy yace"fayallllllllll kala..... sai da yaja numfashi sannnan yakara cewa"fayal kalau kuwa?