PAGE* 17,18
----------------------------------------------------------------------
Daddy yazo yatallafawa fayal domin shiga cikin gida.
Suna shiga ya kwantar da ita akan kujera domin ko bed room basu karasa shiga ba afalo suka tsaya.
Bayan yan wasu daki k'u ne daddy yaja numfashi sannan yacewa momy"wai ya akayi ne? meyafaru?".
Momy itama sai da taja mufashi sannan ta kwashe duk abinda yafaru ta fadawa daddy.
Daddy yadanyi murmushinsu na manya sannan yace"kice ma abin yatsageta kennan kuma gashi ansamu dan albarkan yaro . Domin na tabbatar da wasu ne guduwa zasuyi".
Momy tace"wallah kuwa ninaso ma nagansa domin namasa godiya amman ba dama".
Daddy yace"ai nima inason ganinsa insha Allah duk randa Allah yayi zan gansa sai name halallaci kamar yadda yamin".
Ita dai fayal jinsu take Amman zuciyarta cike take da bak'in ciki .
Ita kuwa Amnah suna zuwa tayi kichin domin daurA musu abinci.
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Amsard ya isa malesia lafiya da isarsa bai nufi ko ina ba sai Amsard special hospital .
Yana isa managen sa yazo yamasa bayanin komai.
Ashe wata yarinya aka kawota sunyi hatsari gaba daya namomin kafarta sun fita sai jijiyoyi kawai ake hangowa.
Sannan kuma yar Nigeria ce ankasa aikin ananne aka turasu malesia.
Batare da bata lokaci ba Amsard yaje yayi wanka sannan yayi sallah yana idarwa yaci abinci sannan yasaka kayan aikinsa.
Sukaje domin farawa yarinyar nan aiki.
Batare da bata lokaci ba yafara aikinsa cikin zafin nama da kwarewa.
Aiko aikin nasu da alamon nasara aciki domin kosu yan malesia sai da suka jinjina masa.
*KATSINA* Gidan su Amsard.
Sahalace tabiyo sameer da gudu tana fadin"uhymmm hajiya momy kice yabani abuna".
Sameer yayi sauri ya dane ajikin hajiya momy yana fadin"uhymm hajiya momy nawane fa ba nata ba ".
Hajiya momy tayi murmushi tare da fadin"kai sameer fa kaine babba kabawa yar kanwarka Aro mana".
Sameer yace"uhumm to gashi kuma in bro Amsard yasiyomin kayan wasa bazan baki ba ".
hajiya momy tace"oh kun tunamin mah bara nakirawosa.
Domin yacemin zai koma malesia Yau.
Momy taceWa sahala tadauko mata wayarta domin ta kira Amsard.
Sahala tadauko sameer yace"ai shi zai kira Amsard tindama bros dinsa ne".
Sameer yakira Amsard har sau ukku bai dauka ba.
SAhala sai dariya take masa.
Momy tace"rabu da ita sameer dina inaga aiki yake kuma ma nasan inyadawo zai kiramu".
Haka dai hjy momy tata fama da rigimarsu sahala.
Har daddy yadawo sannan tasamu sauki suka koma kansa.
๐๐๐๐๐๐ Amnah tagama abinci sannan tayi sallah aka taimakawa fayal ma tayi sannan suka zauna domin cin abincin.
Daddy sai jan fayal yake da magana Amman samm taki .
shiko da hike yasan halinta bai damuba domin yasan koda lafiyarta kalau ba sakewa zatayi ba inaga bata da lafiya.
Dakyar fayal tadan chakali abinci sannan suka tashi sukayi sallah . Kowa yayi bed room dinsa.
๐๐ Abangaren AMsard kuwa sai yanzu yasami kansa . Bayan yayi sallahne yaduba wayarsa yana dubawa yaga missed call din hjy momynsa.
AIKO batare da bata lokaciba yakirata .
Sameer ne yafara dauka suka gesa sannan yabawa sahala suka gesa. BAyan su gama masa shirmensa ne suka bawa momy wayar .
DASuka gesa hjy momy tace"dazu kar dai har kunfara aikine?".
Amsard yafadawa hjy momy duk abinda yasami yarinyar nan
Hajiya momy ta matukar tausayawa yarinyar nan.
SUKayi sallama sannan kowa ya kwanta.