PAGE* 29,30
-----------------------------------------------------------------------
Bayan shigar fayal gidane . Su khaleel kuma suka tafi.
****WASHE GARI*******
Amsard yakammala shirinsa tsaf domin tahowa nigeria.
Yagama komai sannan ya yatafi domin hawa jirgin safe.
yazuwa kuwa ba ajima ba suka kammala kome jirginsu yatashi.
Wata yar budurwace ta nufo inda Amsard yake .
Tana isa tace masa"excuse sir".
Tukun Amsard yadago yakalleta .
Tace"can i sit pls". Cike da shagwaba take maganar.
Shikuwa yarasama me zaice mata kawai sai ya girgiza kai. Alamun eh .
Aiko tana ganin haka tayi saurin zama kusa dashi.
sai magana take me da turanci Amman yaki kullata .
Domin shi Amsard yatsani macen data fiye iyayi.
Baima san tanayi ba duba jaridar hannunsa yake.
Gashi kana ganinta kasan jinin hausawace amman tazo taname wani yare.
Sunfi minti goma ahaka sai daga karshe taga dai ba sarki sai Allah tukun tace"haba oga magana fa nake tun tuni kaki kulani".
Akara na biyu kenan daya dago tukun yace"au daman kin iya hausa neh? AI nazata daga turanci sai turanci".
Budurwar nan tayi murnushi tukun tace"Ai kaine nake tunanin bakajin hausa shiyasa nama turanci".
Amsard yace"owk".
Budurwar nan takara dacewa"sunana zubaidat Amman anakirana da zuby Sannan kuma ni yar asalin jigawace Amman ina karatu A malesia".
Amsard yace"owk barkanki dai".
Zuby takara dacewa"inbazaka damuba inaso nazama sistern ka".
Amsard yamata shiru.
takara dacewa"pls kuma me sunanaka?
Amsard yace"sunana Amsard kuma ni dan garin katsinane nima karatune yakaini malesia sannan nafara aiki".
Zuby gaba daya tabawa Amsard hankalinta sai dataga yatsaya da magana tukun .
Tace"wooow Amman gaskiya sunanka yamin dadi kamar yadda kake da kyau hakama sunanka yake.
Toh pls kayarda nazama sister ka mana".
Amsard"yace owk".
Zuby takuma cewa"toh kadan bani numberka mana dan Allah".
Amsard yace"owk sannan yafadamata ta rubuta sai da takirasa taga yashiga tukun ta katse . Sannann tace"toh kayi save mana".
Amsard baice mata komae ba yayi saving tukun yacigaba da karanta jaridarshi.
Zuby ta lurah dacewa Amsard bai son magana sose shiyasa tun tana jan sa da hira har tayi shiru tabarshi.
Ahaka har suka iso nigeria zuby ta tsaya tukun tame sallama tare da yafadamata a inda yasauka zatazo domin tasamesa.
Amsard yamata kwatance makarantar su fayal tace "aiko gobe zatazo insha Allah".
Aha sukayi sallama kowa yayi hanyarsa.
Abangaren su fayal kuwa yau ana hutu tunda sukayi sallahr asuba ita da Amnah suka koma barci sai wajen 12.30 suka tashi.
Suna tashi kuwa sukayi wanka tare da sallar azahar tukun suka fito geshe da momy.
Amnah ce tafara fita . Tana fita tahango momy naduba takardu ahannnunta.
Amnah tageshe da momy .
MOMy ta amsa cikin sakin fuska .
Sannan fayal tafito ta geda momy.
Momy ta Amsa.
Sannan momy tace"toh tunda sai ynzu Allah yayi kuka tashi ai sai ku daura girki".
FAYal ta hada rai kaman zatayi kuka.
Amnah tace"uhymm momy yunwa fa nakeji nidai".
Momy tace"aiko zakuyi bayani tunda bani nace kuta barci ba".
Fayal tace"uhumm momy".
MOMy tace"toh kudan ban tausayi dai ga abinci ku cen kuje kuci".
FAyal tayi murmushi tare da fadin"owk momy".
AMnah ma tawashe baki tare da tashi domin zuwa cin abincin.
FAYal ma tabi bayanta.
SUNa zuwa kuwa sukaga AShe dambu momy tamusu. DAman tasan Amnah dason dambu shiyasa take yawanyi.
AIkuwa AMnah tana gani tace"woooow sannan tajuya gun momy da gudu turungumeta tare da fadin "nagode momy nah".
Momy tayi murmushi tukun tace"u ar wlcm my daughter".
SAnnan AMNah takoma sukafara cin dambu sai washe baki take tana ta surutu itakuwa fayal sai yatsina fuskar nan take tana ci kaman dolE.
DUK DAtanaso amman bata nunawa.
Itakuwa Amnah sai zakan abinta take.