BABU RUWAN SO

PAGE* 35

by @xayyeesherthulhumaerath

----------------------------------------------------------------

Fayal bata daga sabuwar number awayarta wani lokacinma ko tasan number ba dauka take ba bare wadda batasani ba.

Awannan lokaci kawai sai ta tsinci kanta dason daga wannan number.

Dan haka ta amsa tare da sa wayar akunnenta. Tayi shiru .

Abangaren amsard ma shirun yayi domin ya tsinci kansa asabon yanayin da bai taba shiga ba.

Dan haka dukansu sukayi shiru nadan mintuna .

Sai chan Amsard yayi jarumta yace"Assalamu alaiki".

Fayal sai da taji wanni iri ajikinta na sabon yanayi . Itama dakyar tayi dagiya sannan tace"wa"alaika salam".

Alokacin Amsard yaji yasamu kwarin gwiwa dan haka yakara da cewa"Yakike? ya gida? ya aiki?.

Fayal batasan sanda dariya ta subuce mata ba tsabar tambayoyin da taji ya jero mata.

Aiko Amsard yanajin haka shima yafara tayata dariya.

Sai da tasha dariya iya shanta sannan tace"yooo irin wadannan tambayoyin har ina?.

Amsard yace"har zuciyAr fayal manah".

Sai da faya taji wani zir azuciyarta sannan tayi karfin halin cewa"toh duk dai lafiya".

Amsard yace"ai haka akeso . Yau kunyi lectures ko?.

Fayal tace"eh wallahi gashi duk mungaji ".

Amsard yace"hmm to Allah yahuta gajiya".

Fayal tace"Ameeeeen".

Sai kuma duka sukayi shiru kowa yakasa maganah.

Sai chan amsard yKuma cewa" to sai anjima malama fayal".

Alokacin fayal taji duk walwalarta ta dauke domin bata gaji da jin muryArsa ba.

Dan haka tace,,,,,,,,,,,,,,,,,,