PAGE* 43
----------------------------------------------------------------------- Amsard yAce"daman so nake nafada miki gobe Dan zo jigawane",
Fayal taji wani farinciki ya maimaye zuciyarta hakan yasa takasa hakuri sai da tace "Amman dai zakazo gidanmu ko".
Amsard yace"hAba dai ninasa Nazo banga kanwata ba".
Fayal tace"yauwa yayana har naji dadi wallahi ai nazata ko gidanmu bazaka leko bane".
A haka su fayal sukasha hirarsu har tayauma tafi ta kullum sukansu mamakin hakan suke.
Suna gama wayar nan amsard yakasa barci sai tunanin karyar da yama fayal yake yanzu fa yazama dole yaje jigawa gobe.
Daga karshe ya yanke shawarar zaije goben *INSHA ALLAH* Kafin yakwanta sai da yakira usman yasanar masa yadda suka kaya da fayal .
Usman yaji dadin jin hakan Dan haka shima yakara masa gwarin gwiwa akan yazo kawai.
Abangaren fayal ma takasa barci sai murna take da tunanin wani irin tarba zatawa amsard.
A haka har barci yakwasheta.
*washe gari*
Amsard yana tashi da asuba bayan yayi sallah yayi wanka tukun yaje yasanarwa momy akan yau zaije jigawa.
Momy tamasa addu"a sannan sukayi sallama yakira alhajima yasanar masa domin alhaji baya gari.
Misalin karfe 8 daidai Amsard yadau hanya.
Abangaren fayal ma kuwa tun da ta tashi da asuba batakoma ba . Tarasa INA zatasa kanta Dan farinciki hakan yasa tayanke hukunci fadawa amnah yau zasuyi bako.
Amnah tayi matukar mamakin jin wannan zanchan abaki fayal hakan yasa tayi saurin sanarwa da momy . Momy mah tayi mamaki matuka Amman farincikinta yafi mamakinta yaw a.
Hakan yasa tasa akiramata fayal domin Susan yadda zasu tarbi bakon nasu dakyau.
Batare da bata lokaciba fayal da amnah suka shiga kichin domin daurawa bako abinci.
Misalin karfe 12 amsard ya isa jigawa yana isa ba Inda ya nufa sai gidansu usman .
Usman da Ameena sunyi matukar farincikin ganin amsard.
Anmasa tarba me kyau Sai dai baici abincin sose ba.
Hakan yasa Ameena race"wato ni baza aci abinci na soseba ko? Sabida ynzu an min kawa toh shikenan Nima sai narama".
Usman da amsard suka shekye da dariya sannan amsard have"da kin ishemu akan anki miki kawa ynzu kuma anmiki Amman kin ishe mutane da surutu".
Usman yace"kwaji dashi dai kanku akeji keda yay an naki.
Ameenah tace" aiko ba aji kanmu ba tunda munkusa samun amaryar".
Amsard dai dariya yake abinsa.
*************************** Tun safe sai yanzu su fayal suka kammala girki. Hakan yasa taje tayi wanka sannan tayi sallah tadauko wata rigarta wadda momy tasiyomata daga dubai pink Colo CE da adon farin bit da ston ajiki sai gyalenta fari shikuma me adon pink ga takalminta fari shima dai adon pink ne ajiki.
Batare da bata lokaciba tasa kayan ta bazan iya misalta muku kyaun datayi ba domin kayan kamar dan ita akayi sa yamata dam ajiki .
Batayi wata kwaliyaba illa hoda da man baki datasa Amman hakan bai hana fito da kyahun data kara ba.
Tadauko turarenta ta fesa sai tashin kamshi take wadda inbawai kasantaba zaka zeta sabuwar amaryace.
Tana zaune Kennan tagama kome amnah tashigo tare da fadin woow my soul kinga Kyan dakikayi kuwa wannan ai sai ki zaburar da bakon.
Fayal dai murmushi take domin ita kanta tasan tayi kyau.
************************* Usman yace"kaga mallam tashi muje muyi sallah sai mu huce gidansu amaryar tamu. Inmuka biye ta amena sai mukai LA"asar anan.".
Ameenah race"aa gwara kutafi nikam nasan kawata NATA zuba I do.
Sai dusu amsard sukayi sallah sannan suka dau hanyar gidansu fayal
Dashike daman jiyan fayal ta turamasa address din.
Batare da bata lokaciba suka isa . Amsard yakira fayal yasanar mata sannan suka Shiga da motar ciki.
Amnah CE tafito domin shiga dasu ciki ananne taga abin mamaki wato amsard.
Haka tadaure tamayar da mamakinta tamusu iso izuwa falo.
Suna Shiga taje takawo musu girkin da akamusu.
Sannan suka gesa takoma ciki.
Usman yace"toh sarauniyar sai taja mana ajine kafin tafito.
Bai rufe bakinsaba sukaji anyi sallamah