PAGE 2
-------------------------
Fayal driving take kaman kaman bazatayi ba. amnah tace. "Haba fayal bakiga lokaci yanata kure manah bane? Haba Dan Allah kiyi sauri mana kinsan halin mumy fa Duk maganar nan da Amnah take Fayar ko sauraranta batayi ba. Amnah batagaji ba takara ka da baki tace. "magana fa nake miki inkuma baraki iya yin sauri bane ki tsaya ni nasauka na hau adedeta kawae. Sannan Fayal tace. "oh kekam baki da hakuri kinsan dae banason yawan magana ko? hmm Kayi hakuri dai ai munkusan isa ko.?
Duk irin miskilanci da kyaliya irinta Fayal tana ragawa Amnah domin ita kadai ce tasan halinta kuma ta karance ta
Amnah tace."shikenan amman wlh kome mah mumy tace ke ce da laifi ba ni ba.
Ahaka su fayal da Amnah sukA isa gida batare da k'ara yima wani maganah ba.
Da isarsu mai gadi yaxo yabude musu get sannan fayal tayi paking. suka shiga cikin gida da sallamar su
Momyce zaune tana kallon Tv.
Tace. "wa,alaikumul salam.
Fayal dakinta tanufa batare da ta tsaya sun gaisa da mumy ba. Ita kuwa Amnah taje tageshe da mumy kafin ta nufi d'akinsu.
Mumy tasan halin yarta ta shiyasa ko damuwa batayi ba da tun tana damuwa yanxu kuwa abin yaza me mata jiki sai dai kullum tana taya yartata da addu,a