PAGE 3
--------------------------------------
Daga shigar Fayal daki har tanufi toilet ta dauro Alwalah sannan tayi sallah tana idarwa bata nufi ko ina ba sae gado..
Ita kuwa Amnah tana idar da Sallah ta nufi shashin Momy domin taci abinci sannan ta tayata aikin gida.....
Dazuwanta tace."momy ina food dina? Momy da dan murmushinta tace."gashi cen a kichin Amnah tace."ok momy Taje tadauko abincinta ta ci sannan suka shiga kichin ita da momy dan d'aura abincin dare.
Sunayi suna yar firarsu,, Momy tace."Amnah yau kuma fayal tayi wani aikine Askul?. Amnah tace."hmm momy wallahi bawani aiki datayi illa abinda tasaba kuma shine wai nasata tayi magana dayawa....
Momy Tace."hmm to dai Allah ya shiryata domin narasa gane hali irin na fayal nidai da abbanta ba haka muke ba
Amnah tace."Toh Ameeen dai momy ni abinda ma nafi jiye mata tsoro kar daga karshe tafAda tarkon wani..
Da wannan hirar suka kammala girkinsu
*********** wani saurayi na hango zaune afalo yanata murmushi nikai na dana ga irin kyansa sai da nace masha.. Allah hajiya ce tafito tana fadin."a Amsard Yaushe ka iso ko maganah babu? Sannan saurayin nan yad'ago" oh my hajiya yanzu na iso fa ina hutawane kinsan da jirgi yasauka a airport nina driving kai na xuwa gida shiyasa nagaji....
Hajiya tace."owk to welcome my son yanzu tashi kaje kai wanka sai muci abinci ko?
Amsard yace." ok hajiya nah yanaji gidan shiru neh? Inasu salaha da samir
Hajiya tace."suna makaranta
Amsard yace."oh hakane fa namanta ne yana maganar yana tafiya shashinsa.
Dashigar Amsard yashiga toilet yayi wanka sannan yayi sallar la'asar da hike yayi azahar tun amota bayan ya idar da sallar yasaka kananun kayan sa pink din riga tare da farin wandon jeans .....yafeshE jikin sa da turare sannan yanufo shashin hajiya..
Dashigarsa yatarar duk sun dawo daga skul...
Yashiga da "sallamarsa Su sahala suka amsa tareda rungume yayan nasu
Amsard."yace a su sahala an girma anbar fitina kenan Sahala.Tayi murmushi
hajiya tace."to kuxo muci abincin tunda dai duk kun dawo..
Suka nufi daining table tareda fara cin abinci
Sahala sai surutu takewa yayan nata shiko ba mai son magana bane sai dai kawai yamata murmushi
Sahala tace."uhummm hajiya kinga yaya amsard yaki kulani ko?
Hajiya tayi murmushi tace."kema dai kinsan halin yayannan naku shi magana ma wahala take masa keko bakya gajiya da zuba kamar parrot....
Sahala tace."hhhhh lallai matar yaya zatasha wahala dashi wlh tab Nidai bazan yarda da hakan ba...
Shiko Amsarda,,murmushinsa yake tare da cin abinci
Ahaka suka kammala cin abinci kowa yayi dakinsa