BABU RUWAN SO

PAGE 4

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------

WACECE FAYAL?

Sannan wanene Amsard???...

Fayal y'ace Wajen Alhaji Mohammed Mai zinare Alhaji Mohammed dan garin jigawa neh sannan shi babban dan kasuwane.Abinda yasa akece Masa mai zinare yana safarar sark'wokin zinare neh daga kasashen waje. Matarsa daya wato hajiya Amina Mata mai kirki da son yan uwanta tare da karramah mutane Yarsu daya aduniya wato Nusaiba Mohammed wacce ake kira da fayal fayal yarinyace kyakkyawa fara tas kamar ataba ta jini yafito kana ganinta kaga jinin fulani domin tana da wadatace ciyar suma Sannan fayal tana da miskilanci wanda baran iya misalta muku ba ga kyaliya da rashin son magana sannan tana da wulakanta duk wani namiji da yanufe ta da kalmar so domin ta tsani wannan kalmar...

Acewarta so wahala ne dan haka batada lokacin yi...

Adalilin hali irin na fayal ne momy tadauko yar kanwarta domin taga sun dan shaku da fayal ita kadai

take sakewa fuska...

Ayanxu fayal Tacika shekarah Ashirin tana universty ajigawa karantar likitar mata take...

Wannan kadan kenan daga tarihin fayal...

WANENE AMSARD?

Amsard d'ane ga Alhaji Abubakar ,,,,,,,Alhaji Abubakar minister ne na mai ..

Suna xaune Agarin katsina..matarsa daya wato Hajiya maryam tana da mutuncinta tare da son mutane kuma yar kasuwace Tana fita kasashen waje domin siyo kaya....

yaran Alhaji Abubakar 3 Amsarda ne dansa nafari......Amsarda ba fari bane sannan kuma ba baki bane shi wankan tarwa ne Amman duk da hakan Baya hana kyahu irin na amsard fitowa asalin sunansa Abdulazeez Abubakar Ana kiransa da Amsard...

Amsard bai cika son magana ba duk da yammata dayawa nacewa suna son sa Amman hakan bayasa sa wulakantasu...

Insuka fada mai sai dai kawai yayi murmushi yace ya gode tahanyar da yake rufe ma yan mata baki kenan duk da sun san hakan zai fada Amman hakan baya hanasu cewa suna sonsa....

shiko yamakansa alkawarin bazai auri wace tace tana son sa ba sai yasamu wadda tamai..... tunda hajiyA maryam ta haifi Amsarda bata kara haihuwa ba har Amsarda yakai shekara 20...

Sun cire rai da tunani samun wasu yaran Amman duk da haka basudai nah Addu,a ba ahaka har Allah yabawa hajiya ciki ta haifi yan biyu mace da namiji sahala da sameer....

Amsarda da iyayensa sunyi mutukar farinciki

Yanxu Amsard yagama karatunsa A Ummaru Musa Yar Adu'a dake katsina sannan yakoma malesia domin masters dinsa....

ayanzu yazama cikakken medical Doctor kuma yana da asibitinsa a malesia inda yake aiki shin acen

Kadan daga cikin tarihin Amsard kenan