BABU RUWAN SO

PAGE 5

by @xayyeesherthulhumaerath

-----------------------------

CIGABAN LABARIN

Abangaren Fayal tunda ta kwanta bata farka ba sai dataji ana kiran sallah magriba.

Tana tashi tanufi toilet ta dauro alwala sannan tayi sallah.

hakama su momy sun riga da sun idar da sallar su.

Har sunfara shirya abinci akan daning table.

Suna cikin shiryawa sai ga fayal ta fito tana yatsina fuska. daman wannan d'abi'ar tace.

Momy da Amnah suna ganin fayal suka fara mata murmushi.

Tare da fadin."fayal din momy kin tashi ne?.

Alokacin fayal tadan k'akulo murmushin dole tace." good evening mom and amnah?.

Su momy sukayi murnushi tareda fadin." evening fayal.

Alokacin dady yayi sallama.

Su momy suka Amsa.

Fayal tayi gudu taje gun dadynta. Tareda fadin."welcome dady.

Dady yace."how are u daughter?.

Fayal."am normal dady

Dady yace."dax gud

Sannan momy."tace to ai sai kuxo muci abinci ko?

Dady yayi murmushi tareda fadin."oya daughter tashi muje.

da isar su daning Amnah tafara geshe da dady.

Ya amsa mata cikin sakin fuska.

momy tayi serving din su sukaci abinci cikin farinciki da annashuwa.

fayal Ce tafara tashi tareda fadin."gudnight momy daddy amnah.

Momy tace."haba dai wai harkin k'woshi?.

Kafin fayal taba momy amsa har daddy yafara magana.

"haba daughter wai ke har yanzu bazaki fara cin abinci yadda kowa yake ci bane?.

Fayal ta yatsine fuska sannan tace."uhumm momy dadu fa naci.

Nikam byeeee tanufi dakinsu.

Bayan tafiyar fayal daki. Dady yace."Ni Wallahi har yanzu narasa gane irin hali na fayal.

Momy tace."hmmm Sai dai kawai mucigaba da tayata da Addu'a domin abinnan nata bana wasa bane.

dady yace."to dai Allah yakyauta.

Alokacin Amnah tabudi baki tace Ameeeen ni wallahi ma dady abin da yafi bani tsoro shine yadda take wulakanta maza.

INajiye mata kar taje ta wulakanta wanda batasan zuciyarsa ba.

Kokuma wataranah takamu da son wani wanda bazaiso ta ba.

dawannan hirar suka kammala cin abinci.

SAnnan Amnah tamusu sallama kowa yatafi daki.

WASHE GARI

Bayan su Fayal sunyi sallah Asuba basukoma barci bA.

Suka shiga kichin domin daura breakfast tunda yau da safe suke da lectures. Shiyasa koma barcinma basu koma ba

*********

Abangaran Amsard mah yagama Shirinsa domin yau yanaso yaje ziyarah jigawa wajen abokinsa dake karantarwa acen universtyn.

Kamar karfe 7 Amsarda yafito yana fitowa yatarar da su hajiya da Alhaji na break fast sukuma su sahala da sameer har driver yatafi kai su skul.

Alhaji yace."oh Amsard yaushe agari?

Amsard yasosa k'yaya tare da fadin"ina kwana Alhaji?

Ina kwama hajiya?

duka suka Amsa cikin sakin fuska.

Sannan hajiya tace." ai tun jiya yadawo da rana. kai kuma bakanan shiyasa nabari inma suprise .

Alhaji yayi murmushi tare da fadin aiko kin kyauta dole inmiki kyauta ganin my son.

Sunfara cin abinci kenan. Amsard yace."Alhaji jigawa fa zan tafi ana nemana a universtyn da usman abokina yake koyarwa.

Hajiya taci"oh kai kam dai baka gajiya kuma baka zama waje daya.

Alhaji yace gashima ko yar hira bamuyi ba.

Sai alokacin Amsard yayi murmushi tare da fadin."ai inaga bazan kai kwana 3 bama zan dawo indai nagamah.

Bayan sungama yin breakfast yamusu sallama suka mai addu'a.

yadau hanyar jigawa.

******* su fayal sun shirya da huri domin suna tunanin yau sunada practical shiyasa suketa sauri.

Da fitowarsu Amnah tace nikam fayal bani keyn motar nan dan nasan inna biye miki sai kibatamana lokaci.

Fayal ta mika mata key din batere da tayi magana ba domin ita kanta Saury take taga sun isa skul din.